Yadda Ake Banana Cake
Banana cake, cake ne mai sauki wajen hadawa ga kuma dadin ci domin indai an maida kai wajen yadda za’a hada to nikam a wajena harma yafi normal cake dadin ci da kamshi.
Abubuwan da uwar gida zata bukata sun hada da:
- Banana (Ayaba) 2 ko 3.
- Egg (Kwai) 1.
- Milk (Madara) 150ml.
- Suger 80g.
- Oil (Mai) 60ml.
- Salt (Gishiri).
- Vanilla.
- Baking Powder.
- Flour (Fulawa) 150g.
Yanda Ake Banana Cake
Da farko zaki samu banana dinki masu kyau, bamasu laushi ba saiki bare bawonta saiki yayyanka ta kanana kanana amma ba sosai ba.
Saiki kawo kasko kamar na suyan kwai, saiki barbada suger a ciki saiki kawo wannan Ayaba (Banana) saiki shiryata a akan suger dinan da kikasa a cikin kaskon.
Yadda Ake Hada Dambun Shinkafa
Bayan kin gama wancen matakin saiki samu dan kwananki mai kyau saiki kawo kwanki (egg) kamar daya saiki fasa a ciki sai ki kawo gishiri kadan ki zuba ki dauki Vanilla dinki ki zuba saiki samu Suger ki zuba.
Sai ki juya su sosai, saiki kawo madara dinki ki zuba a ciki sai ki kawo mai dinki shima ki zuba sai ki juyasu sosai su juyu da wannan ruwan kwan naki saiki kuma kawo Fulawa dinki ki zuba a ciki kici gaba da juyawa sai kuma Baking Powder naki shima ki zuba, zakiyi ta juyawa har saikin tabbatar ya juyu sosai wannan fulawar taki bata duddunkule ba.
Bayan kin gama juyawa ya juyu saiki kawo wancen kasko naki da kika shirya ayabarki (Banana) saiki zuba kayan hadinki a kan ayabarki dake cikin kaskonki ki tabbatar ko ina yaji wannan kayan hadin.
Bayan kin zuba saiki dora akan wuta kamar yadda zaki soya kwai amma shi zaki dan rufe saman kidan bashi mintuna saiki bude ki juya bayansa shima yadan samu mintuna amma karyakai mintunan farko, da zarar ya soyu zakiga yayi ja kamar yadda zaki gani a hoton dake kasa.
Masha Allah Bannan Cake yayi sai ci kawai.