Yadda Ake Gyaran Fata da Aloe Vera
Mata da dama na sha’awar ganin fatarsu ta yi sumul babu ƙuraje ko kaɗan. Wannan ganyen yana ɗauke ne da sinadarai da dama waɗanda sukan iya dada tsawon gashin mace, sanya fuska sheƙi, gyaran jiki da dai sauransu. Saboda haka ne a yau na kawo muku hanyoyin da za’a bi domin amfani da ganyen wajen gyaran fata da kuma gashin kai. Inaso masu karatu su gane cewa a duk rubutun da nake yi, idan na lissafo ababen hadin kwalliya, guda ɗaya daga ciki nake so a rika amfani dashi. Domin yawan sanya wa fuska ababe da dama na haifar da fesowar ƙuraje.
Amfanin Aloe Vera A Jiki
- Koɗewar fuska: yawan aiki ko shiga rana na sanya fuska ta yi baƙi ko kuma launinta ya zama biyu. A sami ganyen ‘aloe bera’ sannan a matse ruwan sai a matsa ruwan lemun tsami sannan a kwaba a rika shafawa a fuska domin gyaran irin wannan fatar.
- Yanƙwashewar fata: wannan ganye na rage shekaru daga fuskar mutum. A matso ruwan sa sannan a haɗa da ruwar ‘rose’ sai a rika shafawa a fuska a bari na tsawon minti goma zuwa goma sha biyar kafin a wanke a kullum.
- Domin fuska mai yawan gumi/maiko: a sami ganyen sai a dan kankare bayansa sannan a ɗora a tukunya da ruwa har sai ya yi laushi sannan a sauke a zuba zuma bayan ya huce sannan a shafa a fuska na tsawon minti 20 a kullum kafin a shiga wanka.
- Domin gautsin fata: a markaɗa dabino da gurji sannan a matsa ruwan ganyen ‘aloe vera’ da ruwan lemun tsami sannan a shafa a fuska da jiki na tsawon minti talatin kafin a wanke.
- Gyaran gashi: a matse ruwan ‘aloe bera’ sannan a haɗa da man zaitun a kwaɓa su kwaɓu sosai sannan a riƙa shafawa a fatar kai da kuma saman gashin a duk lokacin da aka yi niyyar wanke gashin kai kafin a wanke . Yin hakan na sanya baƙin gashi da kuma daɗa wa gashin tsawo da ƙarfi.