Yadda Ake Gyaran Gashi
Akwai hanyoyi da dama wadanda mata za su bi domin samar da gashin kai mai tsawo. Yadda ake gyaran gashi abu ne mai sauki. Mata da dama na son ganin kansu da gashi mai tsayi kamar na Indiya. Gashi na daya daga cikin ababen da ke dada wa mace kyau, don haka ya kamata mata ku kula da gashinmu sosai.
Wannan hadin da zan rubuto muku na dada wa gashi maiko, wato yana hana gashi karyewa da sanya shi tsayi da laushi. Ina so a san cewa wannan hadin a kan yi shi ne kamar sau biyu a wata. Idan mutum ya kasance mai yin wani hadi ne daban wanda ba wannan ba, bai kamata ba a rika hada wannan salon gyaran gashi da wani daban in ba haka ba, sai aga kwalliya bata biya kudin sabulu ba.
Yadda Ake Gyaran Kaushin Kafa Lokacin Sanyi
Abubuwan da za a bukata:
- Man Amla.
- Zuma.
- Ruwan dumi.
Yadda Ake Hadawa
A zuba cokalin amla biyu a roba. Sannan sai a zuba rabin cokalin zuma a cikin amla din. A sanya cokalin ruwan dumi kamar 2 zuwa 3. A juya hadin har sai sun cakudu da juna. A taje gashi kamin a shafa wannan hadin a fatar kai. A jira na tsawon mintuna 30. A wanke kai da man wanke gashi (shampoo).
Gyaran Gashi Da Gwaba
A maimakon badda makudan kudade wajen sayen mayukan kara gashi da hana zubewar shi, za’a iya amfani da ganyen gwava wanda bincike ya nuna cewa ya fi karfi da inganci akan yawancin kayan gyaran gashin da ake sayarwa na kamfani. Ganyen gwava na dauke da sinadaran da ke kara yawan gashi, ya tsaida zubar shi, ya kuma kara mashi lafiya da sheki.
Za’a dafa ganyen gwava kamar cikin hannu ko damka daya a cikin lita daya na ruwa, sai a barshi ya tafasa na tsahon minti 20, sannan sai a sauke a barshi ya huce. Idan ya huce za’a matse ganyen a tace ruwan. Wannan ruwa shi za’a mursuka cikin gashin tun daga kasa.Ko dai a mursuka ruwan bayan an wanke gashi a barshi na tsahon awanni sannan a wanke, ko kuma a mursuka shi da daddare, a rufe da hular leda a kwana da shi.
Yadda Ake Wanke Hakora Suyi Fari
Idan aka ci gaba da amfani da Ganyen gwava, za’a ga banbanci. Gashi zai kara laushi, ya karfafa, sannan ya daina zuba, al’amarin da zai sa shi ya kara tsaho cikin dan kankanin lokaci.
Gyaran Gashi Da Man Kwa-Kwa
Man kwa-kwa na sanya gashi laushi da tsayi da kuma santsi. Yana da kyau a rika shafa man a fatar gashin kai a duk lokacin da za ayi kitso ko kuma a rika gauraya shi a cikin man kitso.
Gyaran Gashi Da Man Zaitun
Wannan man na da mahimmanci sosai a jiki baki daya. Sannan kuma yana sanya gashi santsi da baki. Yana kuma magance hurhurar gashi da kuma sanya gashi tsayi da baki da sheki da kuma kyau.