Sinasir na daya daga cikin abincin hausa wanda yake da matukar dadi da kuma sauki wurin hadawa. Anan uwar gida zakisan abubuwan da kike bukata da kuma yadda ake hadawa.
Abubuwan da uwar gida zata bukata sun hada da:
- Shinkafar Tuwa.
- Yeast (Yis).
- Baking powder.
- Sugar (Sikari).
Yadda Ake Sinasir Din Shinkafa
- Za’a jika shinkafar tuwu a wanke ta tas, a markada.
- Idan an markada, sai a zuba yis kadan da bakar hoda a kai shi rana ya tashi.
- A dora kaskon suyar sunasir a wuta, idan ya yi zafi sai ana shafa mai kadan a kaskon ana diban kullin a na zubawa kamar wainar fulawa, ana rufewa har sai ya yi.
Dazarar ya soyu zakiji yayi kamshi sosai yana tashi sosai ki bude a fara shan shagali.