Health Care

Amfanin Man Kadanya Ga Jikin Dan Adam

Amfanin Man Kadanya

Amfanin Man Kadanya

Magungunan Da Man Kadanya Keyi

Amfanin Man kadanya na da matukar yawa a fata domin yana dauke da sinadarai da dama har da sinadarin vitamin A da E. Wannan man na magance kurajen fuska da gautsin fata da kodewar fuska da kuma kyasbi. Amfani da man kadanya na sanya sulbin fata. Ga kadan daga cikin amfanin man kadanya.

  • Hadin magance kyasbi: A samu man sandal da man ‘labender’ a zuba a cikin man kadanya sannan a kwaba sosai sannan a samu murta a zuba hadin. A mayar da wannan man ya zama tamkar man shafawa a kullum. A yi amfani da shi na tsawon watanni shida za a ga canji.
  • Gautsin fata: A samu man kwakwa da man zaitun da kuma man ‘almond’ sannan sai a zuba a murta a zuba man kadanyan a ciki sannan sai a kwaba da cokali ya kwabu sosai sannan sai a rika shafawa a jiki. A mayar da man, man shafawa bayan an yi wanka.
  • Domin magance bushewar labba: A samu zuma da man zaitun sannan sai a zuba a kan man kadanya a kwaba sosai. Sannan a sa a wuri mai sanyi . Sai a rika shafawa a labban baki a kullum za a samu sauki.
  • Domin magance kurajen aski ga maza: A samu man ‘rosemary’ da man kwakwa sannan a zuba a kan man kadanya a kwaba. A rika shafawa a kulum bayan an aske gemu. Yana warkar da kurajen da ke fesowa a gemu bayan an yi aski.
  • Makero: A samu man kadanya a hada shi da man zaitun sannan a rika shafawa a inda makeron yake a kullum domin samun biyan bukata.
  • Kitso: Kitso da man kadanya na magance fatar kai daga makero sannan yana sanya gashi laushi da tsayi da kuma sulbi.
  • Sulbin fata: Yawaita shafa man kadanya a jiki bayan an yi wanka na sanya sulbin fata sannan yana hana fesowar wadansu cuttukan fata.

Yadda Ake Yin Yam Ball

Leave a Comment