Health Care

Maganin Sanyin Kashi Na Galgajiya

Maganin Sanyin Kashi

Sanyin Kashi

Sanyin Kashi ciwone da kan damu mutane musamman ma tsofaffi ko da yake yaranma sunayi. Mutun Zaiji gabobin jikinshi duk suna ciwo kamar wanda ya shekara yana noma. Amma sanyin kashi yana da magani wanda in sha allah idan akayi ana samun sauki da izinin ubangiji.

Maganin Sanyin Kashi

Wannan fa’ida ce game da ciwon sanyin kashi ko ciwon gabobin jiki. A samu man Habbatussauda mai kyau kamar kamfanin Hemani ko Al’habshi ko Al mu’ujiza sai a samu Albasa a yayyanka ta kanana sai a soya ta da man Habbatussauda har sai Albasar tayi kone sai a sauke. Idan ya huce a zuba a mazubi a rika shafawa a duk inda yake ciwo ko rikewa.

Leave a Comment