Assalamu Alaikum yan uwa na barkan mu da warhaka ina fatan muna cikin koshin lafiya. A yau zamuyi bayani ne game da maganin ulcer Sahihi amma zamu fara da wasu daga ciki alamomin ta kafin fadar maganin ta.
Alamomin Ulcer
- Ciwon baya
- Ciwon kirji
- Zafin ciki
- Gudawa mai dauke da majina
- Yawan magwas.
Yadda Ake Gane Ciwon Ulcer
- Shi ciwon bayan ulcer yana tashi ne da zarar ka fara jin yunwa,amma daka ci abinci sai kaji bayanan.
- Haka shima ciwon kirjin shi kuma aksari sai kaci abu mai yaji ko mai tsami.
- Ciwon cikin ulcer ko ciwon bayan baya tashi sai kusan cikin dare ko da sassafe.
Maganin Ulcer Sahihi
- Garun Habbatussauda chokali 10
- Garin Tafarnuwa chokali 7
- Garin ganyen bado chokali 3
- Zuma liter 1 da rabi.
Da farko zaa hade garin dukkan su waje guda sai a kawo zumar gaba daya a zuba a cikin ruba sai a juye garin gaba daya a ciki asa hannu ko chokali a cakuda sasai.
Zaa rika shan chokali 1 da safe kafin aci komai da awa 1, chokali 1 da dare kafin a kwanta.
Za ai ta yin haka har sai an samu waraka,ko kuma ayi na tsawon sati 2 ko wata 1 gwargwadon dadewar da kayi da ita.
Amfanin Man Kadanya A Jikin Dan Adam