Girke Girke

Yadda Ake Dafa Kuskus Da Ruwan Kwakwa

Yadda Ake Dafa Kuskus Da Ruwan Kwakwa

Yadda Ake Dafa Kuskus Da Ruwan Kwakwa

Abubuwan Da Ake Bukata

 • Kuskus
 • Cabbage
 • Carrot
 • Oil
 • Peas
 • Green Beans
 • Seasoning
 • Coconut
 • Liver
 • Spices
 • Egg

Zaki qanqare bayan kwakwar ki saiki gurxa ki kuma blending nata saiki tace ruwan ki aje a gefe.

Sai ki kawo vegetables dinki ki yanka saiki fidda na salat ki aje agefe Wanda kuma zaki sanya acikin dahuwar cous cous din shima ki ajeshi daban.

Sai ki dauko hamtar ki ki wanke ta sai ki tafasa ta ki sanya maggie da spices sai ki yanka ta qanana ki daura tukunya akan wuta ki sanya mai ki sa albasa da sauran vegetables din da kika yanka da green beans da seasoning da spices duk ki sanya ki motsasu har sai sunyi taushi amma kadan.

Sai ki zuba cous cous dinki kiyita motsawa har sai ya soyu amma kada ki barshi ya soye sosae sai ki sa ruwan kwakwa wanda already kin daura shi a wuta ya tafasa sai ki zuba acikin cous cous din amma kada ki sanya yadda zaiyi yawa sabodd cous cous baya son ruwa da yawa domin kada ya ca6e.

Sai ki rufe tukunyar ki kuma rage wutar har sai ruwan kwakwar ya tsane saiki sauke.

Agefe guda kuma kin riga kin hada salat dinki kin kuma yanka qwai bayan kin tafasa shi saiki hada cous cous din ki ayita shagali.

Yadda Ake Wainar Shinkafa Cikin Sauki

Leave a Comment