Girke Girke

Yadda Ake Samosa Cikin Sauki Domin Mai Gida

Yadda Ake Samosa Cikin Sauki

Abubuwan Da Ake Bugata

  • 3 Cup Flour
  • 1/4 tsp Salt
  • 1 cup Water
  • 1/2 cup Corn flour

Yadda Ake Samosa Cikin Sauki

  • Da farko dai zaki zuba duk kayan hadin ki a kwano daya sai ki kwaba kamar soft dough zaki yi shi sai ki murza idan yayi dan ruwa sai kina kara fulawa kina kara murzawa har sai yayi soft fulawar ta bi jikin dough din.
  • Zaki murza ki gasa shi kamar yadda zaku gani,dama yadda ake nadin za,a nuna miki.
  • Bayan ki gasa shi yayi fadi kamar arebian bread sai ki ninka shi gida biyu yadda zaki gani ki yanka shi.
  • Sai ki kara lankwasa shi gida biyu king a ya zama gida hudu ke na.
  • Sanna sai ki sami fulawar ki kamar cokali uku ki kwaba ta ruwa ruwa yadda zaki na like bakin samosar ki.
  • Sai ki yi nadin kamar bututu(funnel)ki zuba kayan ciki (fillings).
  • Sai ki lankwashe bakin yadda naman ba zai fito ba ki goga ruwan fulawar a bakin karshe ki lankwashe shi.
  • Shike nan kin gama nadin samosar ki sai suya.

Yadda Ake Sinasir

Leave a Comment