Yadda Ake Yam Balls
Abubuwan Da Ake Bukata
- Doya
- Kwai
- Attarugu Da Albasa
- Spices and Seasoning
- Mai
Zaki fere doyarki sannan sae ki wanketa sosai kisamata kishiri ki dora akan tukunya kibarta ta dahu.
Kafin ta dahu sae ki markada attaruhunki da albasa sae ki duba doyarki inta dahu sae ki sauke ki taceta.
Sannan ki daba Gwanki iya wadda kike needing sae ki bareshi ki ajiye aside.
Zaki dauko abun goga kubewa na roba karkisa na karfe saeki goga doyarki bayan Kin gama saeki xubawa wannan gogaggiyar doyar taki kayan miyar da kika markada kisa seasoning da spices harda curry if you need.
After that sae ki fasa danyen kwae acikin inda yawa doyar saeki fasa biyu in kadance ki fasa daya. bayan nan sai ki dauko wannan dafaffan kwanki ki dinga cura doyan a jikin kwan yaxamana na zagaye kwan. Sai ki ajiyeshi a gefe a haka zakiyi har ki gama.
Bayan kin gama saeki dora manki a wutah yayi xafi sae ki fasa kwanki kidinga tsoma yam balls din a ruwan kwan sae ki sa a mae in yayi brown sae ki juya dayan side din shima.