Hausa Novels

Download Amratu Hausa Novel Complete

Amratu Hausa Novel Complete

File Name: Amratu Hausa Novel
File Part: Complete
File Type: Text File
File Format: .txt
File Language: Hausa Language
Written By: Khadija Muhammad
Uploaded By: Hausa Drama (https://arewangle.com.ng)
Da gudu ta shigo tafada kan mami dake zaune wash mum nagaji wallahi tai dariya kin gaji kuma kike san karya ni ko haba mami sai kace wata mai kibar axo agani Aliyu dake gefe yana cin abinci ya wurga mata harara kaga ni kadaina hararar mun diya wallahi mum kina shagwaba yarinyar nan da yawa ace yarinya tana SS3 bata dena hawa cinya ba tunda dai ba cinyarka ta hauba ai saika xuba ido. Ke jeki ki daukon abincina kai yaya kai yaya ta fada tana xunbura baki aikifa nake ke nikike fadawa kina wani abu yakai hannu xai maketa tai saurin direwa daga kujerar mami dake shigowa tace kul karka sake ka daketa ta koma bayan mami tanai masa gwalo yakara kuluwa amman mami anman mai inajinku ace ka bi ka gallabi yarinya bakaga rubutu take ba baka ganin salame baka sata kenan mami ni ban isa in aiki kanwata ba kenan oho duk yadda kadauka. Kanwis mai ake dafa mana ne nafaji kanshi ko ina mutumin naka ne ah kice yau da gara yafada yana dariya maxa gama kixo kiga abinda na kawo miki tai dariya that’s my yaya sulaiman shima yandariya😀yace that’s my little sister shiyasa nake sonki suna shirmensu mummy ta shugo tare da murmushi matsalata daku akwae hankali Suhailat ta turo baki”haba mamy wlh ke kk ja Yaya Aliyu yake mana son ransa” Mummy ta”bige bakin ja’i’ra ba yayanki bane Amra ta fita kitchen a guje tana dariya. Amra ta wayi garin ranar litini da xaxxabi sbd haka bataje makaranta ba tana qudundune a blanket,mamy ta shugo dakin tare da fadin Babyn mamy ya naji shuru baki fito parlour ba har munyi breakfast, kuma nagani baki da niyyar xuwa skul ta yamutsa fuska wallahi mami bana jin dadi ne subhanallahi ta fadi gami da saurin kai hannunta goshin ta yadda taji jikin rau daxafi yasa ta mike maxa wannan ciwon bana gida bane maxa mike Ali yakaiki asibiti ta xaro ido gami da mikewa nawarke umma kinwarke kamar ya bansanfa shiririta kintaba ganin inda mutun yaxauna da cuta tafice bari naje kar shima ya fita inda abinda Amra ta tsana bai wuce wata wurda ta hadata da yaya Ali ba dan bata debewa ta dadi. Mami kinsanfa sauri nake kayi hakuri gadanga yanxu xata fito yakara duban agogonsa gami da xura hannu cikin aljihu ya ciro yan dubu dubu guda shida kibata kawai tahau taxi na makara ce maka akai bani da kudin bata ko kuwa motar hayace bansan ta hau inkuma ban isa insa kabane saika fada bahaka ne mami to maine yarinyarce yar rainin hankali kaga inbaxaka kaitaba ka iya tafiya yi hakuri ya fada atakaice gami da komawa mazauninsa mami ta mike tai sama inda dakin yar lelenta yake. Haba Amra ashe ko tashi bakiyiba Alifa yanacan ke yake jira kinsan halinsa nifa mami nace miki na warke kinci gidanku nace maxa mike ta mike alangabe mami ta ruko hannunta sukayo waje kallo daya yai mata ya dauke kansa ganin yadda take wani shagwaggwabewa kamar wata jaririya yabashi haushi jiyake kamar yaje ya maketa ganin yadda mami duk tabi ta daga hankalinta. Suna fitowa farfajiyar gidan ya galla mata harara dallah malama inxaki nutsu kinutsu bansan iskanci sanin yanxu ba mami ko dady masu tare mata yasa ta nutsu kai bakace Amra din da daxu tafiyama sai ana riketa tana wash wash da tafiya dakyar bace. Haba yar gidan dady kidaure kisha maganin ta turo baki ni wallahi shiyasa banasan akaini asibiti yaya Habule dake gefe yace haba kanwis sha xan sai miki wannan abun naki wayon ta fada mami tace daurewa xakiyi ai daman shi magani badan dadi ake shansa ba kinga kar dadinki yadawo yaga kinrame baxaiji dadi ba sulaiman yashigo rike da waya ya mika mata ungo ta kara akunne hello dady ta fada cikin miryar shagwaba haba baby Amra yanxu yayanki yake fadan baki da lafiya ance allura kinki ga maganinma kinki sha indai kina so mushirya to kisha kinji ko ta hannun daman to dadi phone din yaushe xaka siyon kisha maganin indawo sai asiya to dady karka ji komi xan sha promise promise dad love u dad love u dear ta mikawa sulaiman wayar gami da watsa kwayoyin abaki ya Abdul ya mika mata ruwa a glass cup ta kurbi kadan gami da ya mitsa fuska gabaki daya suka saka tafi kaga yar gidan dadinta da maminta sauran nadare Ali da tun daxu ke xaune kujerar gefensu yanajin abinda suke baice tatafus ba inbanda wayarsa da yaketa dannawa mintina zuwa mintina yakan sakin murmushi alamar hirar tasu da kaltum tanai masa dadi sai yanxu yamike dalla malamai kun cikani da tafin banxa ai dakun kyaleta karta sha waxai ji badadi in cutar ta keantar dashi suna basu ce dashi uffannba ya gama banbaminsa ya bar fallon suka bishi da kallo kaji dashi inji sulaiman ashe mutin bai da aiki sai abota da fada Abdul yace ai matar yaya Ali ta banu da fada waya fadama ai iribsu rakumi da akalane suka saka dariya gaki daya mami tace maxa ku mike lokacin sallah yayi sukai waje yayin da Amra tai bayi…. Amra kinko yi sallah eh mami to maxa tashi ki karya time din shan maganinki ya kusa wayyo mami yanxufa sassafene wane safe gomafa ta wuce ni wallahi baccin nan be isheno ba kaji ja’irar yarinya yanxu da lpyr ki kalau aida kina sch ta ruko hannunta maxa ni fito kinga ansamu zazzabin ya tafi inkika ki shan maganin zai iya dawowa. Dasauri ta mike zonan inazaki kuma baki gama cin a bincinba mami zuwa xan inkara tunawa yaya sulaiman sakona tai dariya se akace miki zama zai yaita jira harsaikin tashi ko to tun daxu ya fice oh my God na kwafsa kinga ba surutu zaki tsaya munba abinci zaki zauna kici ke nake jira zan shiga ciki. Zaune take tana kallo taji ancillo mata leda adan tsorace ta dako yaya sulaiman tagani yana dariya matsora ciya kawai ta daka tsalle shiyasa nakesanka yaya baka mantuwa yai dariya ina zan mance da sakon yar kanwata ta bude kai amnan yaya nagode Allah ya saka saunawa zance ki dena godemun innai miki abu kai anman wannan yafi ma wanda nace maka kyau ta mike da gudu tai dakin mami tana kwala mata kira ke lpy kike kirana haka saikin kashen dodon kunne kingani yaya sulaiman ne ya kawon takarba tana dariya kai anman yayanki ya birgeki mami ki tayani godiya. Kefa yar gata ce wallahi ji nake dama nice ke ko Allah maminki da dadinki nasanki yayyanki nasanki kowa ya kwaso alkairinsa naki ne tasa dariya Bilkisu ta kalleta kinsan Allah yayyanki ba birgeni musanman babban wanku yaya Ali ta turo baki tabdi mugun zakice ke nifa dabadan mami da dady ba ai kullun sai ya bugeni hakan ma sunai masa fada ya aka kaya aikedince wani xubin kinfiye abin haushi wallahi koni shagwabarki wataran sai a slow maryam tace kinji mu da bilki mutum bazai shana ba fada mata dai sis shiyasa nake sanki da yawa. Kinsan mai ni wata alfarma zakimun ki taimaka ki danmun hanya yaya Ali yasoni hhhhh waima rufan asuri kar budurwarsa tajini yanada budurwa tanaso na wallahi nifa harba k’agu yai aure yabar mana gida ma huta ace dad yace anan zai zauna tab ai wallahi saina saka yace yabar gidan kinsan mgn ta yakeji shiyasa yaya Alin kekishi dani. Mami wai yaushe dady zai dawo kya tambayeni keda kika san komi nasa kullun saiya cemun sai nanda sati ni haushina ma karmuyi candy bai gida haba aikema kinsan yanasane da ranar zai zo kodan gujema mitarki mami kema mai mita kike cemun tahawota da wasa nake yar gidan mami. Ke ungo sauran kiyi ta cikata da shirmen banxa kinji ko ta karba tabar gun dan sanin halinsa tana shiga daki tace aunty mukli yaushe xakixo daga can barin tace Amran mami kenan aina kusa zuwa na har abada anman kullum sai mami tace bakixo kin gaidata ba shikenan zanyi tunani shikenan ni zanxo intaho dake hooo amra sarkin rigima nidai zanzo to yaushe aisaidai ki ganni kawai to shikenan sunfi awa suna hira sannan sukai sallama ahankula take tafiya dan karta ganta harta shiga dakin ta aje masa wayar tana fitowa ta tsaya ta ajiyar zuciya alamar tasha saiji tai yace sai yanxu kika gama wayar tai saurin jiyowa tana rawar murya u a daman daman daman me kingama karar mun da kudi ce miki akai hako kudin nake yi hakuri yaya inbanyi mai kikeso nayi sai afkin kiyi barna ki bada hakuri bace mun dagani ni sunsun tabar gun hartakai kofa yace tsaya nashiga uku kije kitchen nakawo kifi mimun romonsa sauran kuma kisa asabe tayimun to yaya ta fice da sauri. Ita tai komai na girkinki inka dauke dakan sakwara da asabe tayi hadadden farfesu tai masa da yaji kayan yaji sai lemon citta kasantuwar tasan yanasansa dining takai masa sannan tai dakinsa yaya angama ya fito falon dakin rike da waya ina yake yana dining haka nace miki acan zanci ayi hakuri tace gami da ficewa tana fitowa ta hango yaya sulaiman yana kokarin zubawa da gudu tai gun ta rike masa hannu rufan asiri na yaya Ali ne yasa dariya kincika tsoron yayan nan kaidai barshi danyafa dady da mami basa ban shine yaketa sani wahala ina mamin ta tafi gidan umma Balara haba koda naji nidai yanxu raina ya biya wallahi aikodai saidai kaje kasameshi yasanma wa rufan asiri tasa dariya ashe dik kanwar ja ce akwai a kitchen kaje ka xube au baxaki zubonba ni wallahi na gaji da yawa to kawo na tayaki kaimasa ya daukar mata saida sukaxo bakin kofa ya mika mata nagode tace tashiga sallama akasan makoshi ya amsa ta ajiye gashi yaya baice komaiba ta mike me kike nufi ni xanma xuba wayyo ta fada me kika ce bakomai tai saurin fade ta mika masa gashi ajiye nan ta ajiye tadan zauna adan kaikaice ya kalleta lafiya daman ko kana buk’atar wani abu no zaki iya tafiya Nagode dasauri tabar dakin karya tuna da wani abu Sannu sis gaskiya na tausaya miki kaidai bari ni ba’abin inkai kararsa ba su kara tafiya ya hadan da duka ni wallahi dama kai mami ta fara haifa dana caba seka dunga zanenshi kodai cikin zamu koma ne tafara haifonin ta turo baki kajika yaya ana magana kana sako wasa yasa dariya. Wallahi mami nai missing dinki yaushema na fitan balle kice kefa kike ta cewa intafi karnai dare Ali yashigo ah dole kice kinyi missing dina dodon naki yana gida kenan tai saurin tashi zaune daga kan cinyar mami ganin yadda Alin ke zabga mata harara kai narasa wane irin mutun ne baka da aiki sai harara barshi mami idon ya fado ai ke nikike fadawa haka sa’anki ne ni yi hakuri tace ta faki idon mami ta mai gwalo mami kina ganinta ko me kuma nagani sarkin mita Allah mami yarinyar nan ta raina ni saita dinga mun abinda taga dama innai mgn ace na fiye fada aikaidinne komai fada me yasa sulaiman bai cewa ta raina shi tun ana tsoronka har sai an dena ya kada kai kawai ya bar gun. Tsaki yaja ni wallahi na gaji da jiran yarinyar nan kullum saita makarar dani banda abin Ali kwanan nan zata gama makarantar nan se ka dena kaita ina komai sulaiman ke mata kai makarantar ma kana mita ina yanxu waec suke ace saida aski yaxo gaban goshi zaka kosa kadaure ka karasa ladanka anman mami kina sane da bata makara a islamiyya bata makara dayake sulaiman ke kaita hakuri zakai da’ace zaka daure ka dena wannan fadan zakaga kun shirya tana makarane dan batasan kake kaita kinji ko mami kemafa dakanki kin fada baso na take ba rai dariya hoo Aliyu kaima kasan tana karama kai tafi so halinka ne bata so tana fitowa tace mami sena dawo to yar maminta Allah ya bada sa’a tace amin suka wuce. Wai dagaske kike yayanki yanada budurwa bilki kenan inma baki yadda ba to wallahi kixo jibi nakesan zuwa gaida ta semuje bilki tace Allah sarki ni nafa tausayama kaina nikam nai miki murna da bake wannan dan xafin zai aurava ni murnata ma ya barmana gida uhum bazaki gane bane Kawai anman dai zanje dan ganin wace me sa’arce. A gidansu muklisa budurwar Ali an karbi Amra da kawarta hannu bibiyu da yake ba bakuwa bace tsaraba kuwa da zasu tawo ba’a magana ke nifa inbanda so sone Allah banga me ya Ali zaida wannan ba Amra ta hade rai banfa san cin fuska kema kinsan ta ko’ina aunty mukli tayi ga mutunci sankowa kin wanda ya rasa kedai kice kina kishi kawai haba yarinya kema kinsan na wuce kishi da wannan ohoo dai kyaji dashi. Kinsan me mami sai kin fada aini shagali goma da ashirin gana bikin yaya gana candy ahlallai kice tarihi zaki kafa tai dariya ai wani abun sai ranar Allah dai yasa zamu gani amin Amratuna kaji mami bashi ne dan fariba ko kunya bakiji ba ungo nan ta watsa mata dakuwa yarinya sai zakulo zance tasa dariya aina girma candy zanyi ah lallai kin girma ni kike fadawa haka ko tai sama tana dariya. Motar sa data hango yasa ta cewa na shi na salim dake gefe yai saurin kallon gefe mts yasaki karamin tsaki yasan yanxu wannan yayan nata zai katse musu jin dadi yadda ya hade rai yakara bata tsoro sannu da zuwa yaya yawwa ya fada me kike anan gurin ba komi ta fada to maza wuce gida tai ciki da sauri tana kuka kai kuma saunawa zan ce maka karna kara ganinka anan ba yanxu xanu aurar da ita ba to yaya ya fada yai gun motarsa. Towo yar gidan mami keda wa mami ba yaya bane muna hira da salim yazo ya koroni shima ya koreshi to yo hakuri zaizo yasame ni. Yashigo yana huci mami sannu da gida bata amsa va tace Aliyu wai yaushe kakeson indena maka magana kan Amra takurar dakake mata tai yawa karka manta fa banazatai candy karka kara korar mata samari to mami zan kiyaye yai ciki yana huci gami da hararar amrar Dad nai missing dinka da yawa yai dariya ai nima nayi missing diyar tawa dad kasan ka dawo adedai ko eh mn gobe be final pape dinmu ai nasani ban mance shiyasa nadawo yau ayi komai a idona har suka isa gida suna hira me dadi dan ita da mami kawai suka samu damar taroshi. Agurin yaye su Amra tana daya daga cikin dalibai da suka sami kyautuk tuka na mai kokari tsafta da girmama malamai aikuwa dady da mami sai murna suke diyarsa ta zamo abar alfahari hotuna haka akai tayi kyautuktuka kam tasamesu daga gurin dangi da yayyenta suma kansu murna suke danma anbar nata taron sai ta hada da bikin yayanta anman hakan besa yan uwa sun zozzoba. Yau za’a kai kayan lefen Ali kana ganinsa kaga ango yadda yaketa washe baki sai tsokanarsa ake kai banda abinka kafin azo daurin aure har kafara shinning irin na angwaye dayake bai cika magana sai dai kawai murmushin sati hudu akasa bikin dan haka kowanne bangare wato amarya d ango shiri kawai suke . Yadda Amra ke zagewa kai kace itace amaryar komai ta bukata bata ake gyaran jiki takanas taje tai kyau sosai da biyu take wannan murnar bikin babban yaya sannan bikin su na farko gashi zai bar musu gida acewarta shanawa kuma ao ba kama hannun yaro. Biki kam ya gabato dan yau ake Diner kaf kawayenta Amra ta gayyacesu dan itama yau take party dinta na candy biki ne irin na kasaita bikin girma da girma kudi kam an kashesu. Yau take asabar yaushe ranar daurin aure Amra nacan na kwasar baccinta dan tace ita sai sha daya zata shirya ango yai kyau sosai yaci babbar riga milk komai milk kwarjininsa ya kara fitowa sosai . Waliyin amarya yace eh kunji yadda akace waliyyin ango yace to gaskiya saidai ku tsaya ayi magana da ango abinda yace to to aishike nan bari akirashi awaya ga mamakin Ali wayar uncle dinsa ce ke kiransa aransa yace towo lpy asaninsa uncle yana gun daurin aure kaji waliyyan matarka sunce zaka bar yarsu zuwa Malaysia dan karo karatu shiyasa nace abari kar adaura inji ta bakinka Ali yace ina ni bamu taba batun dasuba kenan baka amin ce ba eh kawu nima dai hk nagani ti kunji yace be amince ba to falillahi hamdan sai afasa aure afasa kuma eh to kutsaya in tuntubi iyayan yaro ko zasi saka ya yadda nan ya fito yasamu baban Alin ya fada masa shi kuna yace bari suyi shawara fa matarsa ya fita daga baya ya shigo yake cemasa afasa daurawa da mukli anman aure babi fashi. Abinda kunnuwansa suka jiyo masa yasa ya kara matsawa kusa bai yadda da abinda yaji ba kai Abdul wai me marokannan ke cewa cewa suke Alhamdulillahi an daura auren *Amratu* da angonta *Aliyu* What dagaske kunnena dedai yajiyo nima dai jinake shirme suke muje mu jiyo suka kutsa cikin jama’a duk inda sikai maroka na biye dasu kaga ango gun amratu bai san sa’adda ya doka musu tsawa pls ku kyaleni haka kun isheni iyye yai cikin masallaci yana hango kawunsa yai gunsa kawu wai da wa aka dauran aure ya washe baki da Amratu mana what waje yai Abdul yabi bayansa yasamu waje ya rafka tagumi Abdul yace abinnan fa da daure kai ina wa ya taba auren kanwa inaji dai ba amra kanwarka suke nufiba shi gabaki daya baijin me yake cewa ba abinda yake tunawa sai Alhamdulillahi an daura auren Amra da ……. Alhamdulillah an daura auran Amra da Aliyu kalman da yake ta maimaitawa knan tabbas in abun da yaji gsky ne xaifi jin dadin inama ace mafarki yake Muhammad ne ya dafa shi haba Aliyu mene haka karka sa sauran jama’a su zaci wani abun yadago idonsa wanda yakada yai jawur pls muhd kafadan gaskiya bacci nake ko idona biyu kaga dan Allah ka tashi mu shiga jama’a yaufa ranar farin ciki ce agunka haba muhd taya zaka kira wannan ranar ta farinciki eh kai agunka ranar bakin ciki ce anman kowa yana kallon ta amatsayin ranarka ta farinciki be a man pls kadaure haka yai tabashi baki har yadan saki ransa suka shiga jama’a yake kawai yake dan shi kadai yasan abinda yakeji aransa. Amra na kwance kamar kamar a mafarki taji wayanta na ringing xumbur ta tashi baccin me dadi da takeyi daddyne ya kirata yace ynxun nan yake son ganinta a falonsa saida gabanta ya bada dam a xuciyarta tana fadi meya faru Daddy kson ganina ynxun gashi ana biki ta bawa kanta amsa bb komai may be yanason ya sata abune tunda mummy mutane sunyi mata yawa da haka ta fito falon tunda tafito mutane ke rangada buda amarya ansha kamshi bata kawo komai aranta ba dan tunda aka fara bikin ma wasu kafi amarya suke kiranta tai bangaren dady. Shi kadai ta tarar adakin kamar yadda ta zata ta russuna ta gaidashi ya amsa cikin sakin fuska badai sai yanxu autan tawa ta tashi ba tai dariya ai nai sallah ok daman magana nakesan muyu ta fahinta to dady ta samu guri ta zauna. Amrah ya fada yanayin yadda ya anbaci sunan da iya saninta bai taba kiranta da shi ba yasa tai saurin dagowa na’am dady ni waye agurinki tace baba na ne ya kada kai yawwa daman alfarma na kiraki kimun tai saurin dagowa haba dady kadena cewa alfarma ka wuce ta aguna yafi kace umarni ashirye nake nabi duk abinda kace yai dan guntun murmushi irin nasu na manya kinsan yau ake daura auren yayanki ko ta daga kai yace yawwa adazu agun daurin auren andan samu matsala iyayen yarinyar sun bada sharadi mu kuma muka ga da cutarwa to hakan yasanya aka fasa auran tai saurin dagowa yace eh an fasa auren da muklisan hakan yasa muka yanke shawarar daura auranku keda Alin zunbur ta mike dady dan Allah karkace ba mafarki nakebe kafin yace wani abu tayi kasa yaraf inda yai dedai da shigowar mami batasan sa’adda ta watsar da ture dinba tai kanta tana jijjigata cikin kuka. *Tuna Baya* Alhaji muktar shine asalin sunan dady wanda yake haifaffen garin kano unguwar galadanci shine dana uku agidansu mahaifinsa wanda yake malamine ajami’ar bayero yayin da mahaifiyarsa take ma’aikaciyar jinya su su shida iyayaensu suka haifa yanayin yadda iyayensu suka tsara musu rayuwa yanayine mai ban sha’awa da birgewa ga kowa. Lokacin da muktar ya kammala secondry dinsa ne ya wuce ABU dake zariya danyin degree dinsa alokacin da ya kammalane aka turashi bautar kasa makarantar yan mata ta kwana dake garko anan Allah ya hada jininsa da wata yarinya me suna Aisha yanayinta na birgeshi yanayin kamalarta nutsuwarta da komarinta saidai yakada fada mata santa yake. Bai kuma yadda san yarinyar yakeba sai bayan sunyi candy dan sune shekarar karshe alokacin da ya dena ganinta ya fiskanci lallai ba karamar kwarar kansa yaiba abokinsa ne yabashi shawarar kafin ya gama service dinsa ya bincika ko zai samu address dinta yai sa’a ya samu batare da wani shan wahala ba yasamu soyayyarta yana kammala service dinsa sukai aure. Rayuwarsu rayuwa ce me dadi rayuwa irin ta yan boko masu illimin addini suna da shekara biyi da aure lokacin Aisha na level 200 ta haifi danta namiji me kama da babansa wanda yaci sunansa *Aliyu* murna gun muktar ba’a magana dan shima yazama baba. Aliyu nada shekara hudu ta kuma haihuwar danta namiji wanda yaci sunansa sulaiman tun daga nan haihuwa ta bude ta kuma hauhuwar Abdullahi bai shekara daya ba tai masa kani Ibrahim shima ta haifo masa kani umar sai yan autanta yan biyu usman da Bilal. Kasan tuwar Aisha bata da diya mace yasanya takesan ya mace kazalika yayanta da mai gidanta. Amra yarinya ce yar kimanin wata takwas tun haihuwarta Aliyu ke kula da ita diya ce ga makotansu in yadawo daga makaranta kan yaje gida ya shiga gidansu amra ya sabota akafada in ba makaranta ba ba abinda ke rabashi da ita sun shaku sosai yarinyar nasansa tun batai wayon cin abinci ba da yasamo kudinsa ai amra zai saima madara. Zaman Amra agidansu Aliyu yafi zamanta agidansu hakan yasanya tafi sabawa da yan gidansu Aliyun fiye da yan gidansu tasaba da dadynsu Aliyu balle kuma maminsu ko unguwa zasu tafi da ita suke tafiya dan yaye ma anan aka yayeta hakan yasanya wasu da dama basusan ba yar gidansu Aliyun bace sai na kusa kusa. Lokacin da zasu tashi daga unguwarne akasha rikici dan amra kuka Aliyu kuka kannensa kuka kai saida takai Amra da cuta iyayenta ganin zasu rasa diyarsu yasanya mahaifinta ranar wata juma’a yasa mamanta ta hada kaf kayanta yadauketa ita da maman nata sai kwanar ganduje nan gidansu Aliyun. Sun gaisa cikin mutunci Amra nata murna taxo gida dayake Ali bayyanan sulaiman ya shigar da ita ciki mami da day da iyayenta suka zauna afalon saka makon ganin shakuwar yarinyar nan daku yasanya naga dacewar in kawo muku ita bawai matsayin yar rikoba na baku ita ne duniya da lahira kuna da damar yin komi da ita tazama yarku mami kam harda kuka dan murna dan tanasan yarinyar da yawa dan ba yadda zatai ne yasanya ta tawo ta barta ko lokacin da suka zonan unguwar kullun da ita take kwana aranta. Sanadiyyar dawowar Amra gidan. Koda Ali ya dawo yai murna sosai koda amra ta isa shiga makaranta Aliyune ya kaita kudi kawai dady ya bashi saida sukai fada da sulaiman dan cewa yai shi zai dinga kaita Aliyu yace be yadda shine hakan yasanya aka raba shi zai dinga kaita boko sulaiman kuma islamiyya tun yana daukanta a hannu hartakai yana dauketa abakin mamaeanta ta karasa . Tasowar Amra agidansu Alitu tasowar gata ne abinda takeso shi ake mata yadda kowa keji da ita ko yayan gidan ba’aji dasu haka . Amra na primary 4 tayi commen inda yai dedai da gama secondry din Alitu an gama masa komi dan tafiya waje yin degree dinsa tun alokacin suka fara batawa da Amra dan baisain shagwaba ko kadan bare raini yayinda in ana neman shagwabbe karon farko asamu amra gashi babu dama adaketa yanxu mami ko dady sa hauka da fada. Lokacin da yazo hutu ne gaba daya alakarsu taja baya domin da yasata abu zata xunburi baki aiki nake ko kai yaya na gaji wannan kesawa yake doketa da yaga mami ko dady basa kusa hakan yasanya taja baya dashi ko yana guri bata zuwa sai in mami ko dady na gurin. Duk shagwaba da gatan da ake ma amra hakan besa duk wani aiki na gida da yakamata diya mace tayi ba ta iya dan mami gwanace bata yadda yan aiki suyi mata girkiba konai tare suke da diyarta tarbiya kuwa iya iyawa suna baima amra basu bari ta lalace ba . Hakan yasa tun tasowar amra mami ke burin Aliyu ko sauran kannensa wani ya auri Amra dan batasan yarinyar ta fita da ga zurriyarsu sai dai ina ko wannensu kallon uwa daya uba daya sukema junansu. Lokacin da dady ya buga mata waya yakeabinda ke ransa kenan fada mata yadda akai da iyayen mukli ne taga ga dama tadamu ta fadawa dady ra’ayinta akai sa’a shina ya amince dan shima abinda ke ransa kenan . Da yake maman Amra tabasali tazo gun bikin ananma ta kwana babanta ma yazo gun dauri daurin aure yasa mami da dady suka tun tubesu kan ya suka gani sukace ai bakomai diyarsu ce duk hukuncin da suka yanke yai dedai su yan kallone bako abata lokaci ba dady ya bugana wakilinsa wato kaninsa kan adaura auren da amr. *Ci gaban labari* Cikin kuka mami ke jijjigata da sauri dady ya bude firji ya dauko ruwa dabsauri ya balle kansa ya shafa mata ta saki wani ajiyar zuciya ahankula ta bude idanunta akan mami ta dorasu wadda ke faman sharar hawaye da sauru ta fada jikin mamin mami kice mun mafarki nake dan Allah mami ta dagota ba mafarki kike ba amra komai gaskene nice sila yanxu zansa a warware aurannan bansan zai cutar dakeba da sauri ta cire jikinta daga na mamin ta sa hannu tana goge mata hawaye mami ki dena kuka banasan ganin hawayenki na dena amra mami indai aurena da yah Aliyu farin cikinki nai miki alkawarin zama dashi har rayuwata ta kada. Dagaske kike yata haba mami kin wuce komai aguna tasaki murmushi naimiki alkawari ta shafa kanta maza mike muje kiyi wanka kafin an gwaye su fara shigowa ta mike da kwarin guwa duk dan farrantawa iyayen nata ta shige bayin dady. Shidai dady kallonsu kawai yake ya rasa ta cewa mami dakanta ta dauko mata kayanta ta kawo mata nan dakin . Koda amra ta shiga wankan zaman dirshan tai tasha kukanta ta koshi saida taji mami na cewa tai sauri ta shessheka ruwanta ta fito duda hawata kwalliya akai mata ba tai kyau sosai fiye da zaton me karatu iya yinta tayi dan kar agane tana cikin damuwa haka ta daure tana ta yake koda angwaye suka shigo haka akaita hotuna tun tana dari dari harta saki jiki. Yinin ranar yini amra tai tana kuka data saci jiki saitai inda ba jama’a ta kwashi kukanta ta a haka har lkcin daukan amarya yy Dady dakansa ya kamo Amra zuwa dakinsa Aliyu na zaune ya zaunar da ita da addu’a ya fara sannan ya fara yan nasihohi kamar yadda kuka sani yar tangar dar da’aka samu yasamu hada auranku dan kuma kaddararku ce zama ma’aurata bawai mun hafaku aure bane dan cin xarafin dayankubsai dan kara xumuncin dake tsakaninmu Aliyu kaine babba dole kaxamto me hakuri hakkin amra gabaki daya yadawo kanka auranta da kake bashi ke nufin xaka mata duk abinda kaga dama ba amra amanace agunka inka zalince Allah na gani xaka iya tafiya wani takaici yakara rufeshi wato ita bama za’a nuna mata matsayinsa ba wato tayi masa abinda taso gashi sarkin hakuri Ke kuma amta Ali mijinki ne ki guji abinda baiso kiyi masa biyayya aljannarki na karkashinsa kinji ko diyata insha Allahu dady tace daki daki yadinga kaita aka mata nasiha da kansa yasata amota direba yaja tunda suka fara tafiya take kuka tun ana bata baki har tsoffi suka fara fada. Ankai amarya an watse an barta daga ita sai halinta dan kawayenta sun gaji sun tafi tsoro duk ya cikata dan bata saba xama ita daya ba lokaci lokaci take daga ido tana kallon agogo 11:00 ta gani wani tsoron yakuma cikata shiko gogon nata yanacan dakyar abokansa suka sha kansa ya yarda zasu rakoshi tana cikin kukanta bata san abokanan ango sun shugo ba qasa qasa taji maganan su suna cewa amaryanmu barka da wannan lkcin,ba tayi musu mgna ba suka xauna daya daga cikinsu da suka kirashi da Ammar ya fara bude taro da addu’ah sannan suka yi musu nasihohinsu har suka karu surutunsu batace musu uffan ba kazalika angon nata suka gaju suka musu sallama ya fita tare dasu domin yi musu rakiya.Amra ganin sun fita tayi maxa tashi tare da sanyawa qofan makulli . Koda ya dawo ya tadda kofar akulle wani takaici yaxo masa wuya lallaima yarinyar nan ta raina masa hankali to mai ta maidashi xuciyarsa nace na mamajo yaja tsaki gami dayin nasa dakin. Da safe ta tashi bacci ta duba agogo innalillahi wanna wane irin baccin ne nayi past nine Amman banyi sallar asuba ba ta dirko daga gadon tare da wucewa bayi sannan tayo alwala ta wuce bedroom ta shinfida sallaya ta tayar da iqama idar da sallanta ke da wuya taji kaman ana kallonta ta baya juyawarta suka hada ido da Yaya Aliyu tace ina kwana yace”ban kwana ba xaki ganni da rashin tarbiyya yanxu akeyi sallan subhi?”tace”cikin murya kamar xatayi kuka Allah Yaya Aliyu vaccine kuma bansan nakai wannan lkcin ba “ya harareta ai dole kice haka tunda kin saba mummy ta shagwaba ki. Ni ba surutu nazo muyi dake ba naga jiya kin rufe kofa ai da baki wahalar dakanki ba kedin baki isa maceba aguna baki isa kallo ba aguna wallahi banxa kwaila inbanda abun iyayenmu mexanyi dake kema kinsani likamin ke akai bake nakeso ba inada wadda nakeso kuma kisani nan gidanane dan haka baki isa kizo kidinga mun abinda kika ga dama ba kinsaba komai saidai amiki nan gidan aurene gidan bauta kishiryama duk wata wahala dole kiyi aikin gida dan bani da ra’ayin yar aiki kuma inasan kisan dasanin daga rand kika shugo nan gidan kinyi ban kwana da kwanciyar hnkli saboda haka ki shirya wa tarban rashun mutunci daga gareni sannan kisani gidana sirrinane dan haka ki kiyayemin sirrin gida wallahi koda wasa naji maganar halin da muke ciki dake awaje saikin raina kanki koda kuwa gun su mami ne inkunne yaji jiki ya tsira fuuuuu yai waje Tunda yafara maganar batace uffan ba sai da ya fita taji saukan hawaye a fuskarta tabbas haka yake yah Aliyu bani ce wadda kakeso ba nakuma sani ban isa zama matarka ba zanyi hakuri zan jure duk abinda zaka mun indai zaisa iyayenka farinciki dan sun fice na guji jininsu akowane yanayi. Saida tai kukanta ta koshi sannan ta mike tai bayi dan wanka batason tai baki su zaci wani abun. Saida tai wanka tai kwalliya tai kyau sosai baxa ka taba cewa tana da damuwaba sannan ta hafo shayinta me kauri tafara sha tana cikin sha taji bugun kofa tana budewa taga su bilki da aunty Aisha sai murna da abincinsu suka tawo mata sako daga mami aiko tai murna taci tai dam sukai ta hira sai dare suka bar gidan. Tana kitchen taji bude qofa alamun mutun ya shugo ba taje ta dba ba domin yasan Yaya Aliyu ne can taji hayaniyar kamar bata mutun da ya ba ta leqa wa xata gani mummyne da daddy sai Aliyu ana hira bata San saboda murna sanda taxo ta dare cinyar mummy ba a guje mummy tace autata me yasa har ynxun bakya girmane tayi murmushi wlh mummy murnan qaninkune sannu da xuwa bari in kawo muku abinsha da ci ta wuce kitchen ta dawo sannan ta rarrafa wurin daddy tace”daddy ina wuni” yace “qlw ‘yar daddy yau kuma tuta ta ta koma qasa tunda kk ga mummy ko kallon inda nake bakiyi ba” Tayi murmushi Allah daddy farin cikin xuwanku ne wlh duk ya rufe mini ido yace “Fatan dai kuna xaman lfy ” Tace “lfy qlw daddy” Yace”in kinsan bakwa xaman lfy ki gaggauta sanar dani domin magance abun kunsa hausawa nacewa ta yaro kyau take bata qarqo so if there is any problem u are free to say it we are ur parent u can’t hide any thing from us Tayi saurin dagowa ta kallo inda Aliyu yake shima ita yake kallo yako sakar mata harara tayi maxan saukar da kai tare da cewan Allah daddy bb komai inda da akwai tun kan kuxo xan buga muku waya in fada muku “toh Allah yy muku Albarka ya qare fitina a tsakaninku ya baku xaman lfy da xuri’a dayyiban” Aliyu yy saurin cewan ameen ameen daddy mungode harar da ya wurgo matane yasata cewa amin batare data shirya ba. Kafin daddy su tafi saida aka qara musu nasiha sannan suka rakosu har mota da xasu tafi Amra ta fashe da kuka😭kan lallai tare da ita xa’a tafi dakyar aka lallashe ta sannan suka tafi. Bayan tafiyarsu suna daidai bakin qofan shiga falonsu ya ja mata kunne Wanda saida tayi qara sannan ya sassauta ruqon tare da fadin Allah ya soki baki gaya musu ba da yau jikinki yy tsami yarinya kuma inaso in fada miki wallahi koda wasa wani ya kuma zuwa gidan bawai momy ko dady ba kika ce zaki bishi bawai kuka ba kawai zakiga abinda zan miki shasha kawai ya tureta yai dakins bai kula da kukan da take ba yai dakinsa yana tsaki. Da asuba ta sheqa wankanta taje tayi sallah.har qarfe tara ta bata bude dakinta ba,bayan ta idar da sallar walha ne ta bude dakin dan xuwa ganin menene xata sanyawa cikinta.A falo ta tarar dashi kwance daga shi sai singlet da dogon wando yana kwance yana kallon wani Indian film a zee cinema Player. Ta gabansa ta wuce ta shige kitchen ya bita da kallo yace lallai ma yarinyar nan.ta fito hannunta dauke da mug na tea tana juyawa sai da ta zauna sannan tace ina kwana yaya hara ya watsa mata gami da tsaki bata ce dashi uffan ba taci gaba da juya tea dinta .wani takaici yakara cikashi wato yari yar nan me ta maidani ke ya fada afusace tai saurin sauke kofin da take shirin kaiwa baki me kike nufi ne nanfa gida na ne nufinki ni zan shiga ingirka abinda xanci ko me kallonsa kawai tai gami da mikewa tai kitchen ruwan shayi ta hado masa hade da soyayyan chip agabansa ta dire yako watso mata shayin wato ga mahaukaci ko dan tsabar wula kanci bama xaki tsaya kiji abinda nake cewa ba balle samun matsayin kiji me zanci ko sa’arta daya akafa ruwan ya zubo mata yakuma dan huce hakan yasanya bata kone ba yi kofin ta dauke gami da durkusawa tana tsince dankalin tsaki yaja yai dakinsa sai da ta gama tsincewa ta goge ko ina sannan tai dakin data ga ya shiga da sallama ta shiga baya falon hakan yasata shiga ciki tsawar da ya daka mata ce tamugun firgita ta har batasan sa’adda tai hanyar fita ba ke dakata jikinta na kyarma ta tsaya me yajawo ki dakina daman daman ta fada tana rawar murya daman what daman tambayar ka zan me za’a dafa ma yaja tsaki inda abinda ke bata haushi be wuce tsakinnan ba banaso jeki kawai harta kai bakin kofa yace bakiji ba tai saurin juyowa ki hadan kunin gyada da kosai to tace tai waje. Da yake mami ta aiko mata da gyada hakan yasanya komai yaxo mata da saumi yunwa takeji sosai dan haka kaskon farko na kosan ta cinyeshi kunu tai mai gardi da zafinsa ta zuba akula ta fido kenan da zummar kai masa daki ta ganshi yana waya har ya wuce taga alamar fita zaiyi tai saurin cewa yaya abinci zankiraki taji yace daga bisani yace love u too sweat heart sannan ya cilla wayar a’aljihu bai juyoba yace kibaima almajirai bai jira me zatace ba yai ficewarsa wani hawayen takaici ya gangaro mata. Tunda ya zauna kamshin abincin ke kwakularsa dadinsa da yarinyar ta iya girki yana zaune ji yake kamar yaje yace ta kawo masa girman kai ya hanshi koda ta kawo masa cewa yai baya ci ya shiga kitchen danna tukunnyar ya maida yawunsa ya hado shayi yai dakinsa bata ko kalleshi ba ta cigaba abinda ya dameta. Zaune yake yana rubutu taxo tazauna adan kai kaice ya kalleta tace sannu da gida yaya bece da ita kala ba tace daman yaya magana naxo muyi nanma bece kala ba kusan minti biyar ya mike zai bar gun tace yah nace xamuyi magana ina kunne ne keji dolene sainayi magana ai dan kar inyi kahauni da fada eyye wato inhauki da fada ko watakan ga mahaukaci ta turo baki gami da juyar da kayya eyye lallai yarinyar nan. “Ki kiyayeni,wlh na kula baki sanni ba ko dan na lura mummy na tare miki fada shiyasa kk rainani?toh xaki san koni waye Aliyu very soon” yajuya zai shiga daki tako saki tsaki karaf akunnensa yako jiyo a fusace. Finciko ta yayi,saida hannunta yayi qara ya matse bakinta sosai har saida idonta yayi ja,ya hankade ta. . kadan kk ka gani ki kuma yimin tsami agudannan sai na fasa bakin naki mara mutunci kawai. Hawayen takaici ya kara zubo mata. Gaskiya yaya sulaiman nai fishi ace tunda aka kawoni sai yau zakaxo ganina yai dan murmushi kema kinsan kina raina abubuwa suka min yawa mun kusa fara final exam ne tasaki dariya kace mun kusa zama likitoci yai dariya ah kun kusa kam to Allah ya temaka ta mike bari na kawo maka abinci kai saidai ki xuban in tafi dashi axumi nake ta hade rai wato baxaka sha ruwa ananba yadanyi murmushi karkiji komai xanyi xuwa na musannan yini xanyi. Yanxuma dady ne ya aikoni yace ki bada takardunki jibi kuma zai turo kamal ya kaiki xakiyi register ta jamb tai dariya kace har anfara yace eh shinema yace naxo infada dan yasan baku sani ba inba nai fishiba tunda ashema da dady be aiko kaba vaxakaxo ke dai kin fiye mita kinga maxa ni dauko min xan wuce ai suna can gida kace mami ta duba durowar da nake ajiyewa duk komai na ciki ban tawo dasuba ya mike se naxo din to yahya ka gaida mami yafice da flask din data xuva masa abincin. Kwana Biyu bata sanya Aliyu a idonta ba,Sam abun bai taba damunta ba,ta tsaya tsayin daka ayi n ibadarta abu daya ke damunta tsoro dan baya shigowa sai dare ya tsala dabadan ma in ta tashi tanaganin kofa abude ba baxa ce agidan yake kwana ba. Ranar da yamma tana xaune da yamma tana sauraran wani wa’axin Sheikh kabeer Haruna Gombe akan biyayyar mata ga maxajensu da irin axabar da Allah ya tanadarwa matan da bata biyayya ga mijinta koda kuwa wani irin miji ke gareta ko talaka,mai kudi,dan iska,mara mutunci kar kiyi la’akari da abinda ke tsakaninsa da mahallicinsa ne,yau idan mijinki dan fashine ko dan yankan kai ne ya xamo wajibi kiyi masa biyayya kamar yanda Allah da manzonsa sukayi umurni iyakacin abinda xakiyi kiyi qoqarin xakulo shi daga axabar Allah addu’ah domin yin haka tamkar jihadine sbd haka ‘yan uwanmu mata ya kamata mu dage Allah yasa mu dace. Amrah hankalinta ba qaramin tashi yayi ba dajin wannan bayanin domin tabbas ya xamo wajibi tayiwa Aliyu biyayya matuqar tana son saduwa da rahamar ubangiji…duk runtsi duk wuya. Fargabar amra daya itace yadda yah Ali zai karbi maganar karatunta dan ta fiskanci yanxu salo salo na mugunta yake fito dasu duk dan ya bata haushi da maganar take kwana take tashi ta rasa yadda zata fada masa cewar yau zata register na jamb. *Qarfe sha Biyu* Taji knocking a qofa taje ta bude was xata gani class mate dinta ne a secondary school su Zainab I Tukur,Ruqayya Abdullah, Nafeesa Shehu Lawal,Zee yabour,Hussy suka shugo tana mmki tace sannun da xuwanku Xee harda ke tace hmmmm ai wlh Amrah bamu taba sanin xaman da mukeyi dake kenan a skul ba ace auranki ya tashi bb gayyata kawai ji mukayi daga sama Hussy tace ke kuyi shuru ai Amrah ni nayi niyyan inxo in xaxxaga Miki nawa masifanne ace duk kirana mummy da kk yi wai daughter xata yi aure ban sani ba wannan ai abun kunyane kinason mutane suyi mana dariya koh daughter😡tayi mgnan cikin rashin jindadi. Amrah tace kuyi hqr abunne ba’ayi tsammani ba sannan tayi musu bayani sun jinjina lamarin tare dayin musu Allah sanya alkhair ya bada xaman lfy da qasantar daki tace ameen tagode tana jinjina kaman qaxantar daki a ranta wato ‘ya’ya ta amsa ameen ne domin kar su San akwai wani matsala tattare da ita sannan kuma a ranta tayi alqawarin xama da Yaya Aliyu koda kan kullum xai dinga yanka naman jikinta yana ci. Sunyi hira sosai na tsakanin qawaye domin sai qarfe shida suka yi mata sallama kan cewan xasu tafi gida da xasu tafi kamar kada su rabu haka nan suka bata gift dinsu kan cewan suna tare kuma xasu yi xumunci ta rakasu suka tafi kowa da kewan dan uwansa Zaune yake yana hira da mukli dan duda sunyi aure da Amra ya kasa rabuwa da muklinsa kullun suna tare a waya danma bata kasar shiyasa nake sanki wallahi Amra dake tsaye tace yah yadago mata hannu alamar ina xuwa I will call u back sweat heart ya kashe wayar afusace ya kalleta ke lpy tace yah magana zamuyi shine xakixo ki damen ke bakisan mutun in yana waya ba yi hakuri tace sai afkin ki cuci mutun ki bashi hakuri me zaki cemun daman jiya yah sulaiman yaxo yace gobe yah kamal zaizo yakaini danyin register din jamb afusace ya kalleta kina nufin karatu xakiyi ba zaman aureba gabanta ya fadi cikin kin kina tace dady ne ya aikoshi to ni atsarina mata ta baxatai karatun jami’a ba kin gane to kawai tace tai daki tana kuka. Koda yah kamal yaxo tace masa ai ita ina yanxu bata sha’awar karatu yadda ya ganta yai tunanin da wata akasa yadda yasan kanwar tasu da dan banxan san karatu rana daya tace ta fasa koda yakoma gida ya fadama dady mami tace ina ai tasan Ali ne xai hanata hakan yasa dady kiransa ya ci masa mutunci dole ya hakura ya barta. Amra tai sa’a jamb tayi kyau dan taci maki sosai aiko murna bakama hannun yaro kasantuwar an soke post UTME yasa tunda akai jamb din akaga taci dady ke ta cuku cuku har saida yaga tasamu admission randa kuwa aka kawo mata admission ko bacci batai cikakkeba minti kadan sai ta juya ta dauki admission letter din takalla ta saki murmushi gani take kamar ma burinta ya gama cika. Amra yau xa’a fara daukan lectures a class da doki ta shirya cikin jin dadi yau an xama yan university😜ta gama shiryawa ta fito falo dan jiran Yaya Aliyu ya shirya ya kaita sbd yace matanshi ba xata yi driving ba taji shuru×2.kamar tayi kuka ta dai daure domin xuwa dakin shi taga lfy xuwanta ta tarar da yana bacci tayi turus ynxun kada in tashi masifaffe ya fara man fada ta kai batasan sanda ta shagala da kallonsa ba sai yau ta taba yima yayan nata kallon tsaf baccinsa yake cikin kwanciyar hankali sai yau ta yadda da su bilki da suke cemata yayanta me kyaune tsawar da ya daka mata ce ta dawo da ita daga hankalinta lpy kika wani xuban idanu cikin jin kunya tace daman yaya lokacin sch yayi naga baka tashi ba xan makara se akai yaya kuma kace baxan tuki ba ok jeki yanxu xan fito yah nafa makara nace kije ko tai waje yafi minti shida sannan ya fito dinning ya kalla me kike nufi ina abinci na yah nafa cema na makara ke kikaga xaki iya karatu ni auro ki nayi inkinga kin bar gidannan kin dafan abinci rai abace taje ta ta daba masa tsaye ta ganshi xuban a flask har bakin mota ta kaimai ta bude xata shiga yace na makara ki kirawo sulaiman ko wani a babban gida su kaiki bai jira amsarta ba yaja motarsa yai waje hawayen takaici ya xubo mata dan tana san makarantar ne da wallahi baxata ba haka ta kira yah nasir ya kaita sun sha hira nanma yake fada mata kwanaki mami bataji dadi ba tai ta mita tace xata je ko da daddare ne. Yana zaune yana cin abinci ta zauna kusa dashi baiko dago ba balle yasan da ita tace yah lpy yace daman yah Nasir yace mun mami bataji dadi ba shi ne nace dan Allah ko xaka temaka ka kaini daga nan inasan inje sabuwar kofa wato asalin gidan iyayenta ce miki akai ni direbanki ne eyyi tai shuru to ba inda zan kaiki bakuma xakije ba batace uffanba sai hawaye kawai da take yafi minti uku yana kallonta yaja tsaki shirya muje tasaki murmushi nagode yaya tai daki. Tayi shigarta dingin bingil material ce pink ta amsheta sosai,ta fito falo sai kamshi take yi shi har ya saba da cin abinci mai dadi da kallon kwalliyar kallo daya yai mata ya dauke idonsa yana gaba tana biye da shi. A can gidan mami hira suka sha ita da yan uwanta ji take kamar karsu tafi jin zata gida yasa mami hada mata tsara sosai dan kai musu. Acan sabuwar kofa ma dai sun taba fira dayake in kadauke shakuwa irinta jini basu wani saba ba kannenta ma bakuwa suke daukanta mamanta tace ina dai kuna zaman lpy tai dariya eh mama to Allah ya dawwamar bata ce uffan ba dan kunya yawwa inasan fada miki nasani Hajiya Aisha uwa ce agunki anman kisani Aliyu danta ne dole saikinyi hankula da kai mata kararsa ko sukarsa kinji ko diyata tai dariya to mama tare ma muke dashi babanta dake kan tabarma yna cin tuwo yace jaji ja’ira bakya bakya cewa yashigo wallahi baba nace yashigo yaki ya mike hara haje yana ganinsa ya durkusa yana gaisheshi haba Ali se kace wani bako yai dariya to muje mama na ganinsa tace dan nema wato surukuta kame damu kenan ai da kanka tsaye kake shigowa yai dariya yana sosa keya ananma sun sha fira sai goma suka koma goda…..

Download Amratu Hausa Novel Complete

Zaku Iya Bibiyarmu ta

Download Dream Girl Hausa Novel Complete
Download Bahagon Layi Hausa Novel Complete

Leave a Comment