Hausa Novels

Download Bahagon Layi Hausa Novel Complete

Bahagon Layi Hausa Novel Complete

File Name: Bahagon Layi Hausa Novel
File Part: Complete
File Type: Text File
File Format: .txt
File Language: Hausa Language
Written By: Hassana Dan Larabawa
Uploaded By: Hausa Drama (https://arewangle.com.ng)
K’aramin Tsakar gidan mata ne a zaune mabambanta,surutai da shewar su kawai ke tashi kamar su fasa gidan Dan hargowa,ga gyad’a marau marau da tub’us tub’us baje a gabansu sai b’arewa suke yi suna jefawa a bakunansu,Zagaye suke da Harira Me kitso wadda take kitse kan wata Yarinya da ba tafi shekara takwas zuwa tara ba. Hirarsu ta katse a lokacin da suka ji yarinyar ta fasa kuka saboda azababben rank’washin da Harira ta zuba mata a tsakiyar kanta,duk suka maida hankalinsu kan Harirar da take kumfar baki tana yi wa yarinyar masifa tare da matse kanta a tsakanin cinyoyinta. “Ke Dan Ubanki zaki tsaya na k’arasa miki kitson nan ko sai na k’ara zuba miki rank’washin da zaki ga k’wak’walwar kanki tana yarari?tunda kika zo nace miki ki bari nayi miki zane amma kika ce ke kwando(Doka) kike so,Dan haka tilas kisa kanki tsakanin cinyoyina in kina son kitsonki yayi kyau,ban da ni ma waye zai tab’a wannan kan da sunan kitso,aikin banza kai duk gunji da almajiran k’eya,billahillazi kika sake d’agowa ban gama ba idan na zuba miki dundu fes zan b’urma miki baya” Ta k’ara matse kan yarinyar sosai tsakanin cinyoyinta tana ta bala’i da masifa,yayin da yarinyar ke kuka hawaye shab’e shab’e Dan azabar da take ji,ba kuma komai ke sata mutsu mutsu ba sai azabar wari da d’oyin da ya addabeta,da ta saka kanta kan cinyar harira sai wani masifaffen wari ya daki hancinta,ta rasa warin menene haka yake tasowa,ita dai ba zata ce warin tusa bane tunda ba taji k’ararta ba,haka nan ba zata ce warin kashi bane tunda Harirar babbace balle tace kashi tayi a zaune,gabad’aya warin ya dami hancinta har cikinta ya fara ciwo da kumburi saboda warin. Habiba ce ta hure gyad’ar da ta b’are a hannunta ta cilla bakinta ta taune,sannan ta kalli Harira tace. “Gaskiya Harira ke azzaluma ce,haka kawai sai lodar yarinyar mutane kike yi Dan tazo kitso wajenki?kin matse mata fuska ta ya ya ba zata so d’agowa Dan ta shak’i iska ba?wallahi ina ganin k’ok’arin mutanen layin nan da unguwar nan da suke turo y’ay’ansu da sunan ki musu kitso,basu san azabar da kike ganawa y’ay’an bane,idan nice kika yiwa y’ay’ana haka ai kotu ce zata rabani dake,wannan rank’washin da kike mata idan tsautsayi ya gifta kika lotsa mata mad’iga fa? Zahra’u ta kwashe da dariya tana tattara b’awon gabanta tace. ” Kin san kuwa Habiba har na hango idanuwan Harira gaban kuliya manta sabo,ni da gwagwalada. Shafa’atu ta karb’e zancen da cewa. “Ni fa banga laifin Harira ba,ai tana ma k’ok’ari wallahi wajen kama kan yaran Unguwar nan da layin nan,yawancinsu kan a diddige yake,ga tsinannen amosani da kwarkwarta amma haka take daurewa ta kitse musu kai,duk fa yawanci yaran ita ce silar fito musu da gashin kansu,duk diddigewar kai sai ta san yadda ta fito musu da shi,ko kun manta kirarinta ne?wato Hariratu mayyar gunji” Duk suka kwashe da dariya suna kallon Harira da ta kammalawa yarinyar kitso tana soke kibiyar a gefen kunnenta,ta samu dai dai k’eyar yarinyar da ta kame tsaf har wani ja tayi Dan kamuwa,ta saita hannunta ta d’ala mata wani shegen d’ad’o me shiga kwanya,a zabure yarinyar ta d’ago kanta tana zillo saboda yadda dukan ya shigeta sosai,ta kai hannunta tana murza k’eyar hawaye na silalowa a idanuwanta,Harira ta kwashe da dariya har da rik’e ciki tana kallon yarinyar,ta dubi matan da ke zaune a tsakar gidan tace. “Dan Allah ku kalle min goshin Samiha yayi wani rantalele kamar goshin jirgi,wai Dan ma kitson ya rufe goshin kenan,kai gaskiya yarinyar nan Allah yayi miki baiwar gingimemen goshi kina fama,rantaka k’wale kenan” Ta kuma fashewa da dariya matan na taya ta,suna kallon goshin Samiha da yake ta k’yallin man kitso yana shining, Samiha ta share hawayenta ta mik’e tana d’aura d’ankwalinta Dan tafiya gida,ta d’auki man kitsonta tana ficewa a gidan da sauri Dan ciwon da cikinta ke mata ya isheta,suka bita da kallo suna dariya yayin da Habiba ke cewa. “Wannan yarinyar idan har goshinki na arzik’i ne mijin da zaki aura ya more,domin zai dangwali arzik’in goshinki tabbas” “In kuma goshin tsiya ne ya shiga uku ba” cewar Zahra’u tana matsawa gaban Harira,sannan ta cigaba da magana tana kallon Harirar tace. “Yi min shiku Harira,amma gaskiya kar ki matse min kai domin ni ba Yarinya bace,wallahi kika matseni ba zan ji kunyar gasa miki cizo a cinya ba,ba dan k’asimu yace yana son ganin shiku a kaina ba wallahi da Zane kawai zaki yi min na huta” Harira ta kyalkyale da dariya tace. “Au wai shi nan k’asimu har ya san ya zab’i kitson da za ki yi Dan ya gani yaji dad’i?ina ganinsa sumummuka sau Ashe shi ma k’wallon shege ne?wallahi Zahra’u idan na fita na had’u da shi a hanya sai na ganshi sululuf yana tafiya yana mik’a wuya mabayyani,na zaci ko Hannu kika sa masa a baki ba zai gatsa ba” Zahra’u ta dallawa Harira harara sannan ta murgud’a baki tace. “Amma Harira baki da mutunci wallahi,mijin nawa ne k’wallon shege?ke yanzu idan na zagi Sunusi za ki ji dad’i?kece kike kallon mijina sahorami amma wallahi lamba d’aya ne,Wannan maganin fa da kuka k’i siya a wajen dillaliya da na siya na gwada kinga yadda K’asimu ya rud’e?abin da bai tab’ayi ba jiya sai da yayi min” Dukansu suka zaburo wajen had’a baki suna tambayarta. “Me yayi miki? Ta wani juya idanu tana fari tace. ” Wallahi har kid’an k’warya yayi min” Suka kalli juna da mamaki,Habiba tayi hanzarin cewa. “Kid’an k’warya kuma?da me yayi kid’an k’waryar Zahra’u? Ta kwashe da dariya tana turo d’ankwalinta gaban goshi,sannan ta sake yin fari da idanu tace. ” Da d’uwawuna mana,ai kamar kalangu ko k’warya haka ya dinga buga kid’a da hannuwansa a gun yana raira min wak’a saboda tsabar zaucewa” Me kuwa za su yi in ba dariya ba?Harira har da fad’owa daga kujerar kitson ta Dan dariya,wai kid’an k’warya da d’uwawu,kai gaskiya ya kamata su ma su siyi maganin ko sa zauta mazajensu kamar yadda Zahra’u ta zauta K’asimu. Habiba garin dariya har da k’warewa,tari ya sark’e ta amma ta kasa tsaida dariyarta,sai Shafa’atu ce ta dai dai ci tsakiyar bayan Habiban ta d’urma mata shegen dundu tana fad’in. “Luf!Luf!Luf!” Habiba tayi sufa ta mik’e ta wawuro ruwa a randar Harira ta kafa kai tana kwankwad’a,sai da ta gama sha sannan tarin ya tsagaita har da hawaye a idanuwanta na dariyar mugunta,sannan ta fuskanci Shafa’atu ta galla mata harara tace. “In bakiyi mugunta ba ta ya ya za a san ke ba aminiyar Harira ba ce? Ni jaririya ce da zaki d’uma min dundu kina wani Luf Luf ?mugunta kawai ke damunki Shafa,kuma Allah bashi kika d’auka sai na rama” Shafa’atu tayi dariya tace. “Sai dai ki rame,daga taimako sai ki hau sababi?da na sani na k’yaleki da k’warewarki,wallahi sai dai ki jiki a k’abari Dan zaki iya zarcewa daga wannan k’warewar” Habiba ta zaro idanuwa tana rik’e bakin ta,za tayi magana kenan Zahra’u ta rigata. “Don Allah ni dai Harira ki min kitson,Dan gaskiya na fara jin yunwa,gashi ko cefanen ba muje mun yi ba” “Yawwa yau me zamu dafa ne? Cewar Habiba tana Neman gun zama. Shafa’atu tace. ” Kawai muyi D’anmalele,Dan sha’awar cin manja da yaji nake ” Zahra’u ta matsa jikin Harira da ta damk’i kanta ta fara tsagar kitso sannan tace. “Aikuwa mun dad’e ba muyi ba,tun randa akayi har garin zubawa ya k’ona Saratu a k’afa,don Allah yau a yi mu wawwarb’e shi” “Wai ina Saratun ma yau shiru bata shigo ba? Harira ta tambaya tana kallonsu. Habiba tace. ” Da zan kullo gidana na ganta tana lek’en da ta saba,tana hangoni ta yafitoni,shine da naje take gayamin wai Salisu ne baya jin dad’i yana kwance yak’i fita ba zata samu damar fitowa ba,yanzu ma da take lek’e bacci ne ya kwasheshi,amma wai duk abin da muka dafa akai mata nata rabon” “Allah sarki Saratu yau ba sakewa,yadda rumfarta take tsukakkiya ga Salisu jibgege yayi shame shame ya za ta yi?wallahi idan nice duk wucewar da zanyi sai na dai daici muk’amuk’inka zan take a matsayin ban gani ba,ko in samu zundumemen kumatun nan naka na bi ta kai kunga ya sace” Inji Harira da ke wa Zahra’u kitso, Har ta kammala na gaban saboda tana da sauri,duk suka yi dariya yayin da Harirar ta fizgo kafad’ar Zahra’u tana cewa. “Sai ki juyo mu k’arasa na bayan Malama” Ta juyo tana tsaki,sannan tace. “Harira ina jaddada miki kar ki matse min kai wallahi” “Ke dalla Malama sai na matse d’in,k’wandalarki ba biyana kike ba sai wani sharad’i kike kafa min,na rantse da Allah kika isheni ba zan k’arasa ba sai dai ki kwana da rabin kai a tsefe,in yaso K’asimu ya k’arasa miki,Don ba wahala zai masa ba tunda har ya k’ware a kid’an k’warya da d’uwawu” Zahra’u ta yi tsaki tana kife kanta kan cinyar Harira,da wani mugun sauri ta d’ago tana toshe hancinta,ta harari Harira tace. “Kinji jiki wallahi,baki da aiki sai tusa,har wani mak’ak’i take yi kamar nayi amai” Duk suka kwashe da dariya,yayin da Harira ke rantsuwar wallahi ba tusa tayi ba. Zahra’u tace. “To wai idan ba tusa kika yi ba me yake wari haka a tsakanin cinyoyinki?kinji warin kuwa Harira?wani gumus yadda kika san ana kwasar turai” Habiba tace. “Kuka sani ko headquarter ne yake hamami da samami?ai kun san Harira ba ta damu da wajen ba bata gyarashi,shiyasa duk yaron da ta kifawa kai a cinyarta yaita mutsu mutsu,Ashe wari ke addabarsu,gaskiya Harira ki canja hali duk kud’in da kike samu na kitso ai ko d’an miski na d’ari biyar kya siya ki dinga tsaftace gurin,ba dad’i Sunusi ya kai kansa ko bakinsa gun yaci karo da d’oyi” “Harira ta tab’e baki tana hura hanci,cikin basarwa ta share maganar ba tare da ta tanka ba,kawai sai ta mik’e tana sababi tana hararar Zahra’u . ” Kin San Allah,ba zan k’arasa miki ba,tunda iskanci ne abin naki tafi Habiba ko K’asimu su yi miki,wadda taga dama ta tashi muje muyo cefanen,tunda akwai ragowar tsaki ba sai mun siyo ba,wadda take da man ja ta d’akko a gidanta,ni dai ina da yaji,in yaso muje gun D’an Damaso mu siyo tumatur da albasa kawai” Duk suka mik’e,Zahra’u ta d’aure kan ta da ba a kammala kitsewa ba,Shafa’atu ta fara magana da cewa. “Yadda rana ta take yanzu gun D’an Damaso a cike yake da yara wallahi,ko kawai muje titi mu siyo? Habiba ta zaro idanu tace. ” Tafd’ijam! wallahi ba zamu titi ba,kin fa san Babalalo yana shagonsa na aski,idan ya ganni a titi ban tambayeshi ba ai na banu,kawai muje gun D’an Damason,kayansa ma yafi arha da kyau,idan muka ga da cikowa ba sai muyi abin da aka saba ba” Inji Habiba kenan tana zura hijabin ta da ta rataye a kan igiyar shanyar Harira. Tana dire maganarta Zahra’u ta k’yalk’yale da dariya tace. “Aikuwa dai gara ayi abin da aka saba,amma Dan Allah yau Ku barni ni zan mintsini D’an Damaso ko nayi masa cakulkuli,nima dai yau naji abin da kuke ji idan kun mintsineshi” Duk suka sa takalmansu suka yo hanyar soro suna dariya,Shafa’atu tace da Zahra’u. “Ke wallahi D’an Damaso yanzu ya kile baya bari a mintsineshi,kina kai mai mintsini ko cakulkuli zai sa gwiwar Hannunsa ya k’ule ki,Dan haka in kika mintsineshi ya kai miki mangari tsaf zai zubar miki da hak’oran gaba,me zaki gayawa K’asimu?wallahi kuma cas duk soyayyar da kuke da K’asimu kina ganin kin mallakeshi zai iya k’aro aure,Dan banga ta yadda zai zauna da ke ba baki duk wawulo” Suka kuma kwashewa da dariya kamar mahaukata sabon kamu tsabar shakiyancin da suke yi,Zahra’u ta kaiwa Shafa duka tana cewa . “Amma Allah ya isa tsakanina dake Shafa,insha Allahu kafin a k’aro min amarya ke Kamilu zai fara yiwa amarya”. Dai dai lokacin suka fito waje, kowacce ta kalli gidanta da ke kulle,sannan suka dubi gidan Saratu da yake a bud’e an d’an sakayo k’ofar,sai ragowar d’aya gidan da ba a tare ba shi ma a kulle,amma ance sati mai zuwa za a kawo wata amarya ciki,shiyasa suke ta d’okin zuwanta,a ganinsu zasu k’ara yawa su zama su shida. Rukunin gidajen a layin guda shida ne,na wani me kud’i ne wai shi Alhaji Ibraheem,ya kan gida gidaje ya saka y’an haya,gidajen basu da girma sosai,duk da dai suna da tsayi,kuma guda shida ne a jere reras,Harira da mijinta Sunusi na d’aya,Habiba da mijinta Babalalo na d’aya,Zahra’u da Mijinta K’asimu na d’aya,Shafa’atu da mijinta Kamilu na d’aya,sai Saratu da mijinta Salisu na d’aya,sai kuma ragowar d’ayan da wani satin za a tare a cikinsa. Dukkaninsu babu wadda ta cika shekara d’aya a gidan miji,illa Harira da take a shekara ta biyu,shiyasa Duk unguwar anfi saninta akan sauran,musamman da ya kasance tana kitso,kuma kusan duk y’an unguwar ita ce take musu kitso,gidanta ya kasance wajen dabdalar mata da gulmace gulmace,haka nan Harira bata tab’a haihuwa ba,su ma d’in Shafa’atu da Zahra’u ne kawai masu k’aramin ciki. An sawa layinsu suna *BAHAGON LAYI* ne saboda yadda layin nasu yayi k’aurin suna wajen tattara mata marasa kamun kai da shashanci,tamkar ba matan aure ba,duk inda kuma ka Shiga a unguwar zaka tarar ana zund’ensu da maganarsu akan rashin kamun Kansu tamkar wasu mahaukata ko marasa ilimi……! ************** Da gudu Samiha ta shiga gidansu ta cillar da robar man kitson da ke hannunta, tayi bakin rariya ta tsuguna ta fara shek’o wani irin amai kamar hanjin cikinta zai fito. Ummanta da ke tsintar shinkafa tayi fatali da farantin ta mik’e a zabure ta nufi y’arta kamar ta kifa….!

Download Bahagon Layi Hausa Novel Complete

Zaku Iya Bibiyarmu ta

Download Amratu Hausa Novel Complete

Leave a Comment