Dream Girl Hausa Novel Complete
File Name: | Dream Girl Hausa Novel |
File Part: | Complete |
File Type: | Text File |
File Format: | .txt |
File Language: | Hausa Language |
Written By: | Deejah Abdul |
Uploaded By: | Hausa Drama (https://arewangle.com.ng) |
Tsaye nake bakin titi amma hankalina gabadaya baya jikina, tinanina kachokan ya dunguma a tunanin dream man dina, inata tsara irin rayuwar da zamu tsara a gidan aurenmu, amma abinda zai baka haushi shine kwata-kwata wanda nake tinanin bai masan abunda nakeyi ba, hasalima ko sunansa bansani ba, qarar wata babbar motace da ta doso wurin ta dawo dani hayyacina, da gudu na tsalakka titin tareda haushin kaina da nikeji, watarana sai na halakka kaina akan tinanin abunda bazan ta6a samu ba. A haka na doshi gidanmu, na tura dan qyauren gidanmu na shiga gida, na kama hanyar wucewa dan akurkin dakina naje na dasa aya a inda na tsaya na tinanin abunda bazai fishsheni ba, tsawar da mama ta dakamin ita ta katsemin hanzari, wai ke meh yake damunki zaki shigomin gida ba ko sallama, sannan maimakon ki gayamin saqon da na aikeki, kin wani wuce soqoqo zaki wuce daki, ki kwanta kina tinane tinanen iskancin da kika saba, dan narasa meh yake damun qwaqwalwarki, juyawa nayi da niyar inkoma inyi sallamar da banyi ba, mama ta katseminb hanxari hanyar tambayata saqon da ta aikeni. Nace mama wlh hajiya abu tace wai ita batada kudin da zata ranta miki, ko wanda ta baki kwanan baya sai daqyar kika…….. Mama ta dagamun hannu ya isa haka, badai biyan buqata karki isheni da surutun banza wuce ki ban wuri, na wuce dan dakina ina qunquni, toh ni miye laifina daga zanfadi abunda aka gayamin, mama cikin tsawa tacemin ni kike zagi? Na wace dai ban tanka mata ba. mama kenan mutum ce mai fada da saurin fushi, amma kuma akwai saurin sauka, ni har na saba da halinta shiyasa ma idan tana masifarta bana tankamata.
Download Dream Girl Hausa Novel Complete
Zaku Iya Bibiyarmu ta
Download Bahagon Layi Hausa Novel Complete