Auren Kwangila Hausa Novel Page 1
Safa da marwa yai tayi a tsakar falon, hannuwanshi goye a bayanshi.
Kallo daya zaka yimashi kasan yana cikin tsananin damuwar da yake Neman mafita.
Tsaki yasake ja a karo na ba adadi.
“Kai impossible wlh!” Yafada cikin qaraji.
“Wlh bazai ta6a yiwuwaba… Bankrupt? Ni? Ni? The whole Alhaji Shamsu bankrupt kema barazana? No, bazai yiwuba, dole insamu mafita, dolene!”
Ya kai zancen yana kaiwa bango naushi.
Qara kai dubanshi yayi ga agogo, 5:55pm.
Tsaki yaja don lokacin be mashi gudu, cigaba yayi da parade dinshi har saida agogon yabuga 6 dot.
Hannu na kyarma ya dauki wayarshi dake kan center table yashiga Neman lambar, har zufa yake don bala’i.
Saida takusan tsinkewa sannan aka Daga.
“Hello sir” muryar wata ta doki kunnenshi.
“Hi Helen…so what’s up, komai yayi daidai” ya tambaya yana dan Waro idanu kamar mai jin tsoro.
“Yes sir, at last ya Baka appointment…”
“Really?!.. Oh am grateful, thank you thank you Helen” yafada yana katseta.
“It ok Sir, Saidai fa sai ranar Monday kuma yace 8 dot zai ganka kuma kasan baison sa6a…”
Qara katseta yayi da “ohh don’t worry, Tun seven ma zanzo, thanks zan maki kyauta idan komai yatafi successfully”
“Alright sir, bye and thanks”
“Ni keda godiya” yafada yana latse wayar.
Zubewa yayi kan cushion din bayanshi yana sauke ajiyar zuciya.
“Wuhh! Allah na godema, atleast nafara jiyo qamshin nasara”
“Don Monday, duka duka yau Friday, ay ko nanda sati yace injira zan jira indai zan samu nasara, Nidai Allah ka dorani akanshi kabani sa’a, bari in rama sallolina, Haba tension ba dadi”
Haka yayi gaba yana ‘yan sabbatunshi, sai lokacin yasamu kwanciyar hankalin yin sallolinshi na azahar da la’asar.
*********************************
“Ok.. Insha Allah… No you don’t have to worry ai munada cika alqawari insha Allah… Sosaima and I bet you zakuji dadin mu’amala damu…hhhh mu keda godiya…. Alright bye thanks for patronizing us”
Katse wayar tayi tana sauke ajiyar zuciya.
“E be like say wannan satin sai munfi shiga chakwakiya” tafada tana kallon wata budurwa dake gabanta riqeda wani qaton littafi da Biro.
Murmushi budurwar tayi tace ” wallahi kau ma’am, nima naga alama ”
“Hmm yanzufa sufee’s family mukayi waya dasu Wai suna buqatar snacks na birthdayn autarsu, kuma this coming Friday, sati daya kenan, ga order din bikin sir Wilson, Wanda ko farawama bamuyiba”
“Aikaudai don yanzu haka bamu gama na ordern savannah hotel ba” inji budurwa tana kada kai.
“Wuhh! Ba damuwa ai, kin gane maryam, kawai yawan ma’aikata zamuyi yadda komai zai tafi fast and smoothly, kinsan an sanmu da cika alqawari banaso mu 6ata wannan image din namu”
Maryam tace “hakane ma’am, hakanma yakamata Ayi”
“So kije kiyi Duk yadda ya dace, ni zan tsara komai zan turomiki anjima ta email…”
Ringing din wayarta ya katseta.
Dauka tayi tana duba mai kiranta.
Da hannu tayima maryam nuni da tana iya tafiya, Dan russunawa tayi sannan tajuya tafice tareda janyo kofar.
Daga wayar tayi cikin fara’a
“Assalamu alaikum”
“Wa alaiki salam, jewel” aka amsa ta dayan bangaren ciki fara’a.
Cikin jindadin yanayinda taji muryarshi tace “Na’am sweet daddy, ina wuni?”
“Lfy jewel, ya kike? Ya aiki”
Marairaicewa tayi tana cewa “as usual dad, ganinan kamar inyi kolo saboda gajiya”
Dariya yayi yace ” maganinki ai, ba yadda banyi dakeba akan kiyi White collar job kina zaune cikin AC babu wahalar komai abiyaki Duk wata da albashi mai tsoka kinqi, yanzu ai ga irinta nan”
Itama dariyar tayi tana jujjuyawa saman kujera don inda sabo tasaba da qorafin daddy.
“Yanzu daddy ya lbr?” Ta tambaya trying to switch the topic.
“Akwai lbr shalele, mai dadi kuwa” yafada cikin zumudi.
“Haba?!” Itama ta tambaya cikin zumudi.
“Wlh, kawai ki qaraso kisha labari” yafada yana yar dariya.
“Aikau yanzu zaka ganni Dama nayi closing”
“To saikin zo shalele”
Kit ta katse wayar tana murmushi.
Saurin tashi tayi tana tattara komatsanta, ta qosa taje taji meya chanza mood din daddynta, yau dasafe ko magana beson yi sbd damuwa, dakyar ta tausashi ta tattausan kalamai sannan tasamu yayi break, Amma yanzu shine hardasu dariya, lallai addu’arta ya qarbu.
Rataye jakar tayi ta gyara rolling din gyalenta ta feshe kanta da turarenta mai sanyin qamshi sannan tafita.
Bakwana tayi da ma’aikatanta kamar ba itace boss dinsu ba sannan ta hau motarta ta kama hanyar gida…✍
Auren Kwangila Hausa Novel Page 2
“Kai alhamdulilah! Amma daddy na tayaka murna!” Tafada cikin murna tana rungumo kafadunshi.
“Ai shalele nafiki murna, Allah dai ya dorani kanshi, naji ance Dan ji da Kaine, shegen kanshine, jibi yadda gaban wahala kafin ya hada mana appointment” yafada yana yatsina fuska.
“Ai tunda dai kwalliya tabiya kudin sabulu shikenan ai, chan ta matse mishi”
“Ai kwalliyar bata kaiga biyan kudin sabulun ba kidai tayani addu’a”
“Insha Allah daddy, komai zaizo da sauki, Allah will be in control”
“Ai ingayamiki, Saidai na hada azahar da la’asar, kasama sallan nayi sbd fargabadon nasan koda nayima sai nayi kwa6a”
Dan shan mur tayi tace “Haba Dad kawai sbd abin duniya saika qi yin Sallah kan lokacin?”
“Wlh shalele nashiga tension ne, shiyasama nakasa tashi nayi”
“Haba Dad, ai Allah baya dorama bawa abinda be iyawa, memakon ace a lokacin tension din zaka yawaita ibada ko Allah zai jiqanka ya dafama?” Ta qarashe mgnr tana turo baki.
“Au nafa manta da ustaziya nake mgn, yi hqr to, kamar yadda nafada tension ne, hakan bazai sake faruwaba” ya fada cikin sigar lallashi.
Sake turo baki tayi tana cewa “ai Dama haka kake cewa, dad kafison abun duniya bisa na lahira, please karage, money Is not everything, marassa shi na living life dinsu comfortably, da arziqin duniya so kwara na qiyama tunda itace dawwamamma”
“Hmm you won’t understand, wlh kudi Sune komai, idan kanadasu kanada komai don duniya da mai kudi take harka, yanzu duba wannan guy din is just 25+ ga yadda aka gayamin Amma bakiga yadda ake binshiba, a haife na haifeshi Amma ji wulaqancin dayayiman, muryarshima kadai haryanzu banjiba, Saidai muyi magana da secretary dinshi, Duk me yaja wannan? Money”
Dan ta6e baki tayi tace “manzon Allah dai yace Ku nemi duniya kamar bazaku mutuba haka zalika Ku nemi lahira kamar bazaku wayi gari a duniyaba”
“To naji ustazziya, alarramiya SAUDATU”
Murmushi tayi tamiqe tana Dan miqa.
“Dad zan haye Kaga magrib ta gabato, zan watsa sai inyi Sallah”
“Ok nima bari inwuce masjid, Adai tuna damu a addu’a, Allah ya dorani kanshi”
Dariya tayi tace “kai daddy? Insha Allah yama doraka, Kaga amfanin self dependent, ni yanzu waya isa yatadamin hankali, wuri nawane, nice boss din kaina, business nawane, ba bashi, ba barazana…”
“Anji wuce kije kiyi Sallah wahallaliya, wannan aikine ko wahala?”
Haurawa tafarayi tana dariya “ai dad Neman halak da wahala”
“Kyaji dashi” yafada yana ficewa.
Saida akayi isha’i sannan yadawo gida inda yayi addu’a sosai na Allah yabashi sa’a akan wannan mutumin don yasan idan yarasa wannan damar to ya kad’e har ganyenshi.
Abinci sukaci duka danyi fira sannan kowa yawuce makwancinshi.
Washegari Saturday, babu mai zuwa aiki cikinsu, yau gida SAUDART ta wuni, tayi musu girki kamar yadda al’adarta take, dukda sunada yan aiki hakan baisa idan tana gida taqi tayasu musanmman fannin girki.
Girki shine favourite hobby na saudart don hakama yasa tana kammala degree dinta tasa daddynta ya budemata qaton bakery idan take hada dangin snacks tana siyar wa.
Saudart macece maison Neman gashin kanta tanada ra’ayi na rashin dogaro da wasu, shiyasa Duk nacin daddy yabarta tayi yadda takeso.
Washegari Sunday, shima babu aiki, fita tayi zuwa gidan mamanta, kasancewar sun rabune da daddy tayi aure wani wuri (zakuji bayanin komai nan gaba)
Acan ta wuni har magrib sannan tadawo gida tahau ayukka a laptop inda Duk ta gama arrangement na gobe…✍
Auren Kwangila Hausa Novel Page 3
MONDAY
Ranar da kowane mahaluki zai tashi busy Bayan hutun weekend.
Hakan take a 6angarensu Alhaji Shamsu, dashi da diyarshi basu koma barciba Bayan sallar asuba
Ita tana shirin zuwa bakery dinta don tantance sabbin ma’aikatan dasukayi applying while Alhaji Shamsu na shirin haduwarsu da life saver dinshi kamar yadda ya rad’a mashi.
Seven daidai taji ana kwankwasa mata kofa.
Zage zip din jakkar laptop dinta tayi tanufi kofar da sauri jin ba’a bar bubbugowaba.
Tana budewa fuskar daddynta ya bayyana.
A mammakince take kallonshi.
“Dad? Lfy?” Ta tambaya cikin mammaki.
Hararar wasa ya gallamata
“Da akayi me?”
“Naganka ciki shiri”
“To da cikin me kikeson ganina? Mtcheew Nidai am off” yafada zai juya.
Saurin tsayar dashi tayi dacewa “please kajira mutafi tare, nima na shirya bari na dauko laptop”
“Mtcheew kiyi sauri fa” yafada yana duba wristwatch dinshi.
Sauri tayi ta dauko tafito suka sauka inda sai anan tasamu zarafin gaisheshi ya amsa ataqaice don Duk hankalinshi baya taredashi.
Gannin ta nufi dinning yasashi cewa “where are you going to?”
“Dad breakfast zamuyi ko?”
Tsaki yaja yajuya yana cewa “in that case, bye saimun hade”
Saurin biyoshi tayi tana mashi magiyar yabari su karya Amma ko tankata beyiba.
Tasan Dama za’a Rina Dama haka daddy yake indai Abu na ranshi ko abincin kirki be iyaci, kuma ya dinga tsaki kenan kamar wani tsaka.
Rakoshi tayi har bakin motarshi, leqowa tayi Bayan yazauna ciki tace “dad Allah yabada sa’a, Amma please kaci wani Abu don Allah”
“Amin, insha Allah” ya amsata yana tada motar.
Ja tayi baya tabishi da iso harya fice Daga gidan.
Ajiyar zuciya tayi sannan tanufi motarta itama ta shiga tabata wuta ta fice.
A.A INTERNATIONAL ENTERPRISES
Tsaki yaja a karo na ba adadi yana kallon wrist watch nashi.
“Wai Helen are you sure yau yace inzo? Wannan wulaqancin dame yayi kama, ace Tun seven thirty inanan yanzu har nine thirty?”
“Please kayi hqr sir, wlh nima narasa dalilin rashin zuwanshi haryanzu kuma wlh boss Beda African time”
“Mtcheew, wannan ai wulaqanci ne, ki kirashi mana, mutane sai wucewa suke suna Kallona wannan ai ba girmana bane”
Waro idanu tayi tace “me? Kace injawa kaina firing, kawai kayi hqr, kamayi hqrin kwanaki bare yan awwanni”
Ya bude baki zaiyi magana, maganar ta maqale sanadin shigowarsu.
Saurin gyara zama yai yana sakin fuska.
As usual, fuska a tamke yashigo, ko kula da Helen mai gaisheshi beyiba bare Alhaji daketa yaqe baki.
Wucesu yayi mutane hudu na takemishi baya, daya daukeda suitcase dinshi while others na empty handed.
Saida yashige sannan Alhajin ya kalli Helen yace “to ya? Nashiga?”
Harara ta 6alla mashi batareda tasaniba.
“Lallaima sir, babu iso babu komai?”
Daidai nan qattin dasuka rakashi uku suka fito banda daya Wanda Dama ba bodyguard bane ko ga yanayin shiga zaka gane.
Tattara wasu files tayi tace “5mins sir”
Kada mata kai yayi yabita da kallo harta shige, ajiyar zuciya ya sauke yana addu’ar samun nasara cikin zuciya.
Bayan minti goma, sai gata tafito daukeda wasu files din.
Binta da kallo yayi harta ajiye saman desk dinta sannan tajuyo tace “Sir kana iya shiga”
Gabanshine yafadi, ya rasa dalilin nervousness din dayakeji Tun wayewar garin yau.
Miqewa yayi a sanyaye ya nufi kofar
Knocking biyu yayi sannan akayi mishi iso.
Ahankali ya tura kofar yana summoning din courage dinshi.
Da sallama yashiga, amsa sallamar dayan mutumin dake ciki kawai ya iyaji shiko gogan ko dago kai beyiba.
“Bismillah” inji dayan mutumin yana nunamishi kujerar dake facing dinsu.
Ja yayi ya zauna sannan ya miqama mutumin hannu sukayi musabaha, juyowa yayi wajen gogan ya miqamishi hannu shima don su gaisa.
**************************************
Duk yadda take zaton aikin zai ca6emusu yawuce hakan.
Sosai suka Zage wajen tantance sabbin ma’aikatan tareda rarrabasu bangarorin da yadace.
Idan Kaga Saudart lokacin saita burgeka sbd kazar kazar dinta, ga iya mu’amala da jama’a, take ta saye zuqatan sabbin ma’aikatan, haka taita zagaya bangarorin bakery din, idan ka ganta Baka cewa itace mai bakery din don har 6il6ishin flour ke akwai ajikin apron dinta.
Haka sukaita zagaye suna distributing aiki…✍
Download Auren Kwangila Hausa Novel Complete Here
Download Kaddarata Hausa Novel Complete
Download Mahabeer Hausa Novel Complete
Wlh inason novel din sosai