Kaddarata Hausa Novel Page 1
Misalin karfe daya da rabi nadare samira ta tashi dawani matsanancin ciwon kai Wanda ya haddasa mata da zazzabi mai zafi juyi kawai take akan makeken gadon da yake manne da bangon dakin ga damuwar gobe zaa daura mata aure d yaya fahid Wanda tasan duk duniya babu wanda ya tsaneta sama dashi tun tana er karamarta yake nuna mata tsantsar kiyayyah wanda tarasa dalilin dayasa yake nuna mata tsanar nan tuno maganganun daya fada mata jiya da daddare tashiga yi daya aiko yusuf dan karamin kaninsu yace yakirata bayan tashiga dakin saukar baki gabanta na faduwa dan idan taga yaya fahid tamkar taga mala’ika sam bata son suhadu dashi tun tana karama har yanxu da takai shekara 19 tun daga ranar kuma da su ummah suka yanke shawarar zasu hadani aure dashi taga wata sabuwar kiyayyah wadda tafi ta da yafara nuna mata bayan na zauna akasa kaina a sunkuye jikina sai bari yake yakalleni cike da kiyayyah fal idanunsa sannan ya zauna a kan kujerun alfarmar dake zagaye a daki yasa kafarsa daya kan daya yace samira kike dasuna ko meye kinje kin kulla munafirci zaa hadani aure dake ko to ki tabbata dacewa karma kitaba sawa a ranki waini fahid zan daukeki a matsayi matata danni kamar baiwata na daukeki ke koh baiwata mah tafiki mahimmanci a gurina wllh na tsaneki na tsaneki sam bana son ganinki jinake kamar nakasheki kuma idan mah kina farin ciki zayi mana aure to kisani gidana yafi makabarta dan zan gana miki a zabar daban taba yimiki bah banza yar kauye kazama kawai mara kamun kai er gidan talakawa wllh da in aureki gwanda na dauri karya kuma koda an kawoki gidana karki sake ki nuna min Wannan mummunar fuskar nan taki dan bana son ganinta ko dan Yana gama fadar haka yasa kafarsa ya hankadata sai da ta fadin har sai d goshinta yafara fitar d jini d gudu ta tashi tafita daga dakin tana kuka tashi tayi zaune jiri na dibarta kuka tashiga yi mai sauti amman babu Wanda yasan mah tanayi dan daga ita sai ubangijin da ya haliccemu ne kadai yasan tanayi dan babu mai jinta dakin ita dakadai ce tunda bikin yazo mommy tasa aka ware mata bangarenta daban dan acewar mommyn a hakane zata samu ayi mata gyaran jiki innalillahi wa inna ilaihi raju’un tashiga maimaitawa ya Allah ina rokanka da kyawawan sunayenka ya Allah kaikace mu rokeka zaka amsa mana ya Allah ina rokanka ka dauki raina tun kafin akaini gidan yaya fahid nasan irin kiyayyar d yayi min ba karama bace yaki min tsanar da tun a rayuwarsa bai taba yiwa wani irinta bahh a kullum maganarsa dayace idan har suna magana wani akan ya rage yimin irin wannan kiyayyar yace ya tsani samira tsanar da ban tawa yiwa wani ko wata bah narasa Menayi masa narasa takarasa maganar cikin kuka a kana jin kasan na tsantsar bakin ciki d kuma Dana sanin sanin yaya fahid a rayuwarta tayi kukanta mai isarta sannan ta tashi cikin jin jiri tashiga toilet alwala tayi sannan tadawo ta shimfida dadduma duk d tanajin bazata iya yin sallar a tsaye bah amman a haka ta tada sallah sai d tayi raka’a 2 sannan tashiga yin addu’ar Allah yakawo mata sauki d zaa raba wannan auran kafin gobe
Kaddarata Hausa Novel Page 2 and 3
Bayan ta idar d sallah tashafa addu’a akan daddumar ta kwanta cike d damuwa ahankali hankalinta yafara kwanciya tafara jin dan sanyi a zuciyarta sam ko kadan bataji zata iya komawa bacci tana nan kwance aka fara kiraye kirayen sallar asuba cike d rashin kuzari ta tashi tayi sallar asubah kan gadon nata takoma zauna tazabga tagumi hawaye fal idanuwanta ita tasan haka kaddararta take bazata taba yin farin ciki a rayuwarta ta duniya bahh tun batasan kanta bah tafara fuskantar matsalolin rayuwa kaddarori suna zuwan mata ko wacce d irin tata tashin hankalin Kifa kanta tayi akan gadon duk addu’ar dataxo bakinta yinta take a haka bacci barawo yayi azan gaba d ita
Waye fahid??
Fahid babban danne ga ministan kudi na jihar Abuja Alhaji Ibrahim bukar sai kuma kannansa umar shine mai binsa sai Ibrahim mai sunan mahaifinnasu Wanda suke kiranshi da daddy sai kuma dan karamin kaninsu yusuf mahifiyarsu hajiya rahma ‘yace ga sarkin garin bauchi wanda su biyu allah yabasa amatsayin ‘ya’yansa hajiya sadia itace babba sai hajiya rahma, rahama macece mai son mutane ko kadan bata d wulakanci kyakkyawace sosai dan idan kaganta zakayi zatan balarabiya ceh mahaifinnasu mai martaba Abdullahi Yana son rahma saboda kyawawan dabi’unnata kwata kwata batayi halin yar uwarta sadiya bah dan sadiya macece mai kyamatan mutane kuma t tsani talakawa mahaifin fahid Alhaji Ibrahim yaga hajiya rahma a gidan er uwarta sadiya dake garin Abuja dayake mijin aunty sadian abokinsa neh dan haka baiyi kasa a gwiwa bah gurin fada mata Yana sonta bah itama ta amince cikin kannanin lokaci akayi biki aka gama ya gina mata tafkeken gida a cikin garin abujan tsayawa kwatanta irin yadda gidan ya tsaru bah mah bata bakine dan bazai taba kwatantuwa bah haka aka zuba mata bayi a gidan kai kace gidan wani sarkinne Fahid kyakkyawane na akin karshe dan kamar mahaifiyarsa kadebo gaba daya yayi karatunsa akasar newyork tun daga sec har zuwa university duk a can yayi yatasone cikin gata dan kakanninsa har iyayensa duk suna ji dashi fahid yarone miskili dan sam yammata basa gabansa duk da irin yadda yammatan suke kokarin suga sun mallakesa a matsayin miji saudat er aunty sadia wacce itace erta tafarko itace take son fahid din kamar hauka dan har samunsa tayi tafada tada mata shi kuma yamuna mata bai shirya fara soyayyah yanxu bah kuma baya ra’ayinta a matsayin matarsa gwanda tun dare bayi mata bah tasamu wanda yake sonta ya aureta amman duk da haka ita ko kadan baza iya cire soyayyarsa bah a zuciyarta saboda tana ganin su din Yan uwane indai iyayensu sukaji zasu goyi bayanta kodan zumincinsu yayi karfi sosai
Kaddarata Hausa Novel Page 4 and 5
Wacece samirah
Samira yar asalin wani kauyece mai suna fayauna mahaifinta bukar isah d mahifiyarta Aminatou haifaffun kauyenne mokobtane dan ga gida ga gida suke bai wani sha wahalar neman aurenta bah tunda daman suna son junansu mahaifin bukar ya mutu tun baa haifeshi bah su tarane a gurin mahaifiyarsu maza hudu mata biyar haladu shine babbansu sai mai bi masa Ayuba, zubairu, sai kuma bukar matan kuma lantana, zilai, abu, talatuwa sai kuma autarsu falmata koda bukar yaxo yafadawa mahaifiyarsa yana so ya auri Aminatou tayi farin ciki kuma yabasa goyan bayanta dan tasan yarinyar akwai hankali d nutsuwa yan uwansa mah sun nuna farin cikinsu haladune kadai ya nuna kin amincewarsa amman yasan ko ya nuna kin amincewarsa bazasu taba goyon bayansa bah dan haka yabar abin acikin ransa bangaren iyayen Aminatou mah sunyi matukar amincewa d aurenta d bukar din dan kowa a kauyen yana shedar bukar mutumin kirkine kasancewar ita kadai Allah yabasu suna d rufin asiri baa wani bata lokaci bah akayi aurensu suka tare a gidan d bukar din ya gina dayake yana d zuciyar yi madaidaicin gidane ciki d falone sai bandaki d gurin wani dan karamin waje d yaware dan dafa abinci watansu hudu d aure mahaifiyarsu bukar tarasu mutuwar data girgiza kowa a dangin musamman mah bukar dan yana sonta sosai aka share zaman makoki kowa yakoma gidansu sai laulayi yasa Aminatou agaba dan ko abinci taci sai ta amayoshi ga wani zazzabi mai zafi d ciwon kai datake fama dashi hankalin mijinta bukar yatashi dan kowajen aiki baya xuwa wannan ashe wata matsalar d sabuwar kiyayyah yakara shiga tsakanin bukar d Aminatou har yatara yan uwansa yana fada musu cewar Aminatou ta asirce dan uwansu gashi ko wajen aikinsa mah yadena zuwa ita kuwa Aminatou da mijinta bukar basu san maike faruwa bah haka haladu yatara yan uwansa suka nufi gidan bukar suna shiga suka Tatar d bukar yanawa Aminatou wanki ita kuma tana kwance a tabarma nan kuwa suka sa salati kuma suka tabbatar d cewar yayannasu ba karya yake musu bah Aminatou ta asirce dan uwansu bukar shi kuwa bukar tashi yayi fuskarsa dauke d murmushi yanawa yan uwannasa sannu da xuwa
Download Kaddarata Hausa Novel Complete Here
Download Mahabeer Hausa Novel Complete
Download Mijin Kwaila Hausa Novel Complete