Hausa Novels

Kawarta Ce Sila Hausa Novel Complete

Kawarta Ce Sila Hausa Novel

Wasu mata ne zaune cikin wani katafaren falo, dukkan su sanye suke da Vail banda daya wance take da alaman cikin gidanta take, duk fuskokinsu looks sad, daya daga cikin Matan mai kama da matangidan tace
“Ni har yanzu ban gane wannan abunba…ya zaayi cikin shekara daya maneman auren yarinyan nan su dinga ja da baya?… Kuma duk sai sun kawo lefe amma daga baya su fasa?…” Bata idaba wata ta katseta dacewa
” kema dai kin fada….wannan abun da gani ba haka nan bane…there is something big behind this… Yarinyan nan ba wani mugun hali gareta balle ace kilan bincike suke kanta….nidai gaskiya Hadiza mu mike tsaye…. ” tafada tana kallon matan gidan, Ahankali Matan ta cire hannun ta daga tagumin datayi ta kallesu Sannan tace
“Yanzu sis me zanyi?…hmmm…nidai nasan kawai lokacin aurenta ne baiyi ba….besides by daughter is just 20 years old.. Name zan dami kaina?…” Tafada cikin sanyin murya,
“Daman abinda zakice kenan…to let me warn you… Wannan abun dake faruwa is not just like that….this is a bad omen,…ya zaayi yarinya son kowa kin Wanda ya rasa ta zama tamkar abun wasa wurin maneman auren ta?…gaskiya dole mu mike tsaye…” Wata babban cikin su ta fada , Dan tsayawa nayi na kurawa dukkan su kallo naga suna dan kama da juna da alaman dukkan su biyar a related ko kuma ince are siblings. Matan gidan kallon wacce tayi magana tayi
“Sisters… Kar muyi staining hannuwanmu da zunubai kan matsalolinmu…yanzu in mukaje wurin malamai..abubuwa daban2 zasu fara fada mana….kawai mu kai kukan mu ga Allah batare da Mun je wani wurin ba….” Mikewa babban cikin su tayi
“Ki zauna nan …ai kin ga zama….” Tafada tana daukan wani hadadden hand bag tare da Vail da ke kusa daita, kallon ta Matan gidan tayi ta kalli wata mai aiki dake jera abinci kan dinning Sannan tace
“Anty ki zauna ki ci abinci mana…” Matan galla mata harara tayi
“Ke Allah ya sauwake halin ki….wato ta abinci kike?…mtssss” ta fada ta bar sauran nan zaune. Hanyen waje tayi. Matan gidan mikewa tayi jiki ba kwari ta dan raka Matan Sannan ta dawo. Sauran mikewa sukayi Tana karasowa cikin falon ta kalli sauran Matan Sannan tace
“Sisters.. Muje muci abinci…” Tafada cikin sanyin murya, dukkan su mikewa sukayi Sannan daya daga cikin su tace
“Ina ihsan din take?…”
“Tana upstairs…” Matan gidan ta amsa mata. Wacce tayi tambayan ta kama hanyan upstairs sauran suka nufi kan dinning table.

A upstairs kam cikin daya daga cikin dakunan wasu beautiful black beauties biyu ne zaune kan gado, daya bata da Dan kwali tana zaune kan gado don har kafafunta suna kan gadon, da ganinta cikin tunani take, daya kuma zaune bakin gadon hannun ta daya kan cinyan wacce ke zaune kan gadon,
“Babe am so sorry about this… Kiyi hakuri..Allah zai baki Wanda ya fishi…” Inji wacce ke zaune bakin gadon, itadai bata ce komai ba don banda tunanin rayuwan ta babu abinda takeyi, tacigaba dacewa
“Shahid doesn’t deserve you… Ki kwanta da hankalin ki Allah zai kawo Wanda ya fishi…” Tafada tana massaging yatsunta Ahankali, Ahankali yarinyan dake zaune kan gadon ta daga manyan idanuwanta Sannan tace
“Ni har yanzu abinda ke bani mamaki shine duk basu cewa ga laifina agaresu…ko jiya kwana mukayi da shahid…amma…” Bata idaba ba kuka ya kufce mata
“Sis what have I done wrong?… What is happening to me?…in one year… 3 wedding date amma non is coming through…” Tafada cikin kuka sosai, da sauri dayan budurwan ta haye kan gadon, ta rungume ta tana cewa
“Babe…please don’t cry…you know how much I hate to see you cry…please stop it….” Tafada cikin comforting tune, itakam kaman ance ta ta kara volume, rungume kawarta tayi ta cigaba da kuka,
“In kina kuka ni ince me?…remember we are of the same age amma babu namijin da ya taba kawo kudin Neman aurena gidanmu… So kinga yours is better…” Da sauri mai kukan ta fara girgiza kanta tana cewa
“Wallahi naki ya fi….nida sai ansa rana an kawo lefe sai a fasa fah?… Yanzu mutane sai suyita tunanin wani mugun Abu nakeyi yasa ake guduna….Wallahi am tired….” Da sauri kawarta ta rufe mata baki tana cewa
“Shhhh….stop saying that…komai jarabawa ce…Allah ya baki ikon cinye wannan jarabawan….” Bata idaba ba wayanta ya fara ringing, da sauri yarinyan dake kukan ta daga kanta tana kallon wayan kasancewan tasan mai kiranta cos he’s ringing tune is different, itama kawarta kallon wayan tayi, ihsan zata dauki wayan kawarta tayi saurin daukan wayan tayi picking tafara cewa
“Munafiki…Allah yaisa tsakanin mu da kai…wallahi yanda ka sa aminiyata hawaye kaima sai kayi Wanda yafi nata…. Shege….” Tana kaiwa nan ta katse wayan, ihsan tsaya kallon ta tayi,
“Haba husna….what did you do that for….” Da sauri ta fara cewa
“Yo ai is better in zage shege….in badan ya rainaki ba ya zaayi ya fasa auren Sannan ya kiraki Dan uwarshi….”
“Kilan hakuri zai bani…” Tafada ahankali,
“Kam…Allah ya sauwake…” Bata idaba wayan ya dauki ringing kuma da sauri Husna ta dauki wayan ta kashe shi ga baki daya, itakam ihsan bata kara cewa komai ba tacigaba da kukan bakin cikin abinda ke damunta, itakuma husna sai lallashinta take, kofan dakin aka bude wata ta shigo
“Ambaby Ashe haka aka karayi?…” Matan ta fada, da sauri ihsan ta mike ta fada jikin mata ta kara fashewa da kuka,
“Kai…stop crying… Meye abun kuka?…..” Inji Matan,
“Abinda nake fada mata kenan anty Zainab…” Inji husna
“To kinji kawarki ta fiki ahankali… Ki shuru abinki.. Meye cikin auren in badan yana sunnan manzo ba….” Anty Zainab ta fada tana shafa bayanta,
“Amma anty kilan aljanu gareni….”
“Shush…ki bar fadan haka…komai daga Allah ne…ko aljani sai da izinin Allah…. Maza muje ki ci abinci…” Da sauri ihsan ta girgiza kanta
“Anty ban iyacin komai…” Anty Zainab Dan tureta tayi tana cewa
“Ki sauko kici abinci in ba haka ba in kira maki anty Zuwairat…” Da sauri ta kalli Anty Zainab
“Ta zo ne?….”
“Eh..tana downstairs…” Da sauri ta goge hawayenta tare dashiga bathroom ta wanke fuskan ta ta fito amma still idanuwanta ja ba kaman kasan idanuwanta abinda da farar yarinya.
“Babe muje muci abinci…” Ta fadawa husna cikin sanyin murya dukda tasan ko kadan ba abincin zata iyaci ba amma tana tsoron anty Zuwairat don duk cikin yan uwan mom tafi tsoron ta cos she’s a no nonsense person. Dukkan su fitowa sukayi.
Suka zauna kan dinning, mom sai kallon ta take, duk mutane sai cin abinci suke amma banda ihsan dake wasa da spoon dinta,
“Wai baki cin abincin ne?…” Wata mata ta daka mata tsawa da sauri ta fara cin abincin, da gani Matan itace anty Zuwairat, itakam husna ko daga kai bata Iya yi don ba karamin tsoron anty take ba.

Kawarta Ce Sila Complete

Leave a Comment