Health Care

Maganin Ciwon Mara Lokacin Al’ada

Maganin Ciwon Mara Lokacin Al’ada

Wannan ciwo kusan yana addabar mata da yawa ‘yan mata da matan Aure kusan wasu duk lokacin Al’ada idan zata zo suna yawan samun ciwon mara wasu ma Al’adar tasu tana rikicewa ko jinin ya rika zuwa kadan kadan ko yazo yaki tsayawa. To duk mai fama da irin wannan damuwa insha Allah indai aka bi wannan hanya insha Allah zaa samu waraka.

Abubuwan Dake Maganin Ciwon Mara Ga Mata

  1. Garin Habbatussauda.
  2. Garin Tafarnuw.
  3. Garin Zogale.
  4. Garin Kusdul hindi.

Yadda Ake Hada Maganin Ciwon Mara Na Mata

Zaa samu garin kowanne daga cikin abubuwan kamar chokali 5 sai a hade waje daya a rika diban chokali 1 ana dafawa da ruwa kofi 2 idan ya dawu sai a sauke a tace a sha kofi daya safe daya yamma, zaa iya saka zuma ko sukari kafin a shah.

Maganin Ciwon Mara Lokacin Period

Mafiya yawa daga cikin mata na kuka da ciwon mara wanda kan hanawa wasu rawar gaban hantsi. So dayawa xakaga mace na xullumin tsayuwar wata domin tasan irin axabar datakesha duk adalilin ciwon mara. Ciwone dakan tsananta agurin wasu yakuma galabaitar dasu wasuma har amai xakaga sunayi yayin da wasu numfashinsu ke daukewa yakaisu ga suma. La’akari da hakan yasa aka fadada bincike domin kawo ma ‘yan uwa mata wasu daga cikin hanyoyin daxasubi dan ganin Allah yasauwake yakuma basu lafia.
1. kisamu dabino mai kyau sabbin tsinka guda bakwai, kici dasafe kafin kici komai.
2. kisamu xogale kadan da tsamiya kisa akofi, sannan kisamu tafasashen ruwa kixuba akofin idan yadan huce kishanye a lokacin. Kiyi haka har sau uku. Insha Allahu xaki samu sauki.
3. kisamu dawa kamar rabin mudu kijikata akwano natsawon kwana biyu sannan ki mutssiketa kitace sannan kisha. Yana maganin ciwon mara sosai yanakuma tsinka jini gawadda ciwon yadameta jini baixoba idan dai tai hakan jinin xaixo ciwon yayi sauki. Allah yabama masu fama da wannan matsalar lafiya ameen.

Maganin Ciwon Mara Lokacin Al’ada

1. TSAMIYA: A samu sabuwar Tsamiya a jika aruwa tare da bushashiyar gauta arika shan ruwan tun kwana biyu kafin zuwa haila, har lokacin da hailar zata fara zuba. Wannan Mataye da dama sun jarraba kuma sun dace. 2. MAN ZAITUN: A sami man zaitun sai a Karanta ayoyin Alqur’ani acikinsa sannan Mace ta rika shan cokali guda safe da yamma kullum har zuwa lokacin zuwan Jinin al’adarta. Kuma zata rika shafawa ajikinta har Mararta (Amma banda al’aurarta saboda ayoyin da aka tofa). Shima wannan idan anyi shi za’a dace. Koda Aljanu ne suke rike mata Marar, ko suke sanya mata ciwon jikin to zata samu waraka.
3. KUSTUL HINDI: Idan an jikashi a ruwa ana shansa safe da yamma shima yakan Magance matsalar ciwon mara ko rashin zuwan jinin sosai, ko kuma rikicewar jinin Al’ada. Kuma koda ajiyar Aljanu ne a marar mace ko mahaifarta, in sha Allahu zata samu waraka.

Maganin Ciwon Mara Da Sanyin Mara Na Mata

Leave a Comment