Maganin Karin Kiba Cikin Sauki
Barkanmu da wannan lokaci sau da dama mutane kan bukaci maganin da zai rage musu kiba, amma a wani bangare daban kuma wasu mutane na neman maganin karin kiba ido rufe.
Ina fata zaa karanta wannan darasi a natse kuma a turawa yan uwa da abokan arziki ta kafar WhatsApp ko Facebook.
Abubuwan da zaku bukata sun hada da:
- Waken soya cokali 2
- Ridi cokali 2
- Dabino cokali 1
- Hulba cokali 1
- Gyada dai dai misali
- Madarar gari cokali 5
Yadda Ake Hada Maganin Karin Kiba
Da farko kusamu waken soya dinku mai kyau (a gyarashi sosai a fitar da tsakuwar jikinsa) sai a soyashi har sai ya fara kamshi, sai a sauke shi, bayan yayi sanyi zaku dakashi sosai yazama Gari.
Haka zalika kusamu ridin shima mai kyau (a gyarshi yadda zai zama babu wani datti a ciki) shima sai a soyashi yadda ya kamata sai a sauke bayan yayi sanyi sai shima a dakashi ya zama Gari.
Suma sauran abubuwan duk haka za kuyi masu ma’ana a soya su sannan sai a daga.
Bayan duk angama dakawa sai a hade garin baki daya a ringa yin kunu dashi in sha allah cikin lokaci za’aga chanji.
Abubuwan Dake Kara kiba
- mutum yana gama cin abinci ya kwanta ba tare da ya mike tsaye ba ya tattaka ko da taku 20 ne zuwa da dawowa.
- shan damammiyar fura da safe da nono mai kauri Kafin aci komai.
- yawan shan alewa chocolate.
- yawan shan kayan cocoa a shayi.
- cin nama mai kitse.
- yawan cin kwai (egg).
- cin farar kaza.
- yawan shan lemon kwalba ko na kwali ko na gwangwani.
- rashin motsa jiki.