Health Care

Maganin Ciwon Mara Da Sanyin Mara Na Mata

A yau zanyi bayani ne game da maganin sanyin mara dake damun maza da mata, kuma wannan magani ne sadidan mujarrabun. Amma kafin muyi bayanin maganin ya kamata kusan alamominshi domin kada ayi ciwo daban magani daban.

Alamomin Ciwon Mara Da Sanyin Mara

 • Daukewar sha’awa.
 • Fitar farin ruwa daga gaba.
 • Tsagewar farji.
 • Fitar kuraje a gaban mace ko namiji.
 • Saurin inzali.
 • Ciwon idanu, har yakan sa a daina gani.
 • Fitar kuraje a jiki ko wani sashe na jiki.
 • Fitar kuraje a baki da makogwaru.

Maganin Ciwon Mara Da Sanyin Mara

 • Ganyen zogale( moringer).
 • Ganyen raihan(basil).
 • Kanun fari(clove).
 • Citta(Ginger).
 • Tafarnuwa (Garlic).

Yadda Ake Hada Maganin Ciwon Mara

Za’a samu abubuwan da muka lissafa amma kowannen su busashshe ake bukata, sai a hade waje guda a dake su ko ma niƙe su,suyi laushi. Za’a rika diban karamin chokali a zuba a shayi ba madara(Tea) a barshi na tsawon kinti 5 sai a sha,zaai haka sau 2 a rana. Idan mace na ciwon mara da debi chok81 babba ta tafasa da ruwa kofi 2,idan ya wuce sai tasa zuma,tasha kofi 1 safe 1 yamma. Za’ai amfanin dashi na tsawon sati 2 ko wata 1.

Maganin Sanyi Mara Lokacin Al’ada

Leave a Comment