Health Care

Maganin Ulcer Na Hausa Mai Kyau

Maganin Ulcer Na Ganyen Gwaba

Duk mai fama da matsalar stomach ulcer insha Allahu Wannan fa’ida zai iya jarrabawa,kuma cikin nufin Allah da yardar sa zai samu waraka. Bayan magance ulcer kuma yana kara kare jikin mutum daga kamuwa da wasu cutuka masu karya garkuwar jiki.

Abubuwan Da Zaa Nema
1. Ganyen Gwaba guda 6-10
2. Ruwa lita 1

Yadda Ake Hada Maganin Ulcer

Za’a samu ganyen mai kyau sai a wanke shi, sannan a jajjaga shi kadan sannan a hada da ruwan lita daya a tafasa shi har sai ruwan ya sauya kala. Sannan a sauke a tace, idan ya huce a rika shan karamin kofi sau 3 a rana, ga babbam mutum yara daga shekara 6 zuwa 15 sau biyu rabin karamin kofi. Mace mai ciki ma zata iya sha domin yana taimakawa sosai, haka na mace mai fama da matsalar al’ada ma zata iya wannan hadin.

Amfanin Bagaruwa Ga Mata Da Maza

Leave a Comment