Mahabeer Hausa Novel Page 1
“A garin kaduna a kuma cikin G.R.A.
ta ‘Yan majalissu, Anguwa ce wacce ta tara manya manyan masu hannu da shuni zaune a cikin ta,
‘yan siyasa da masu hali kenan, sannan kuma a koda yaushe cikin unguwar zaka jita tsit babu hayaniya bisaga sauran anguwanni.
Gidan alhaji mu’aazam saraki shine gida mafi d’aukan hankalin mai kallon sa a layin,
Gida ne tsararre na gani a fad’a, duk da gidajen Suma fitattune a tsari da kuma kyau to amman kuma nasa ya d’ara nasu.
In ka shiga cikin Harabar gidan kuwa ba q’aramin girma ne da ita ba,
Daga can gefe kuma tampal tampal ne shaq’e da motoci na yayi sama da nawa a ciki, dan sunfi q’arfin a tsaya q’ilgasu komin sa idon mutum kuwa,
gudan gefen kuma injinan motsa jiki ne kawai sai lambu daga can side d’in Wanda babu kayan marmarin da babu a cikinsa, sannan kuma ga swimming Wanda ke cike da q’ananun kifaye sunata shawagi a cikinsa da fararen ruwa a cikinsu,
Sai d’ayan swimming d’in na wanka shima wani q’aton gaske ne cike da blue d’in ruwa a cikinsa,
daga gefensa ga Wasu kujeru da kuma fararen matakalu na shiga da fitowa a swimming pool d’in, sannan an ajiye wani d’an q’aramin gado da tebur na ajiye kayan buq’atu na Wanda in ka fito wankan zaka iya kwantawa dan hutawa,
ga kuma bukkar dake kewaye da gadon gwanin sha’awa dai abun,
Sam wurin inwa ce zalla babu rana haka wajen yake rayuwar sa.
Hakama q’aton falon gidan inka shigesa komi yayi, Wanda Keda d’akuna Sama da 7 a cikin sa, kowane d’akin babu abinda babu cikinsa najin dad’in rayuwa.
A hnkali ta ke saukowa daga saman benen kaida ganinta kuma zakasan lallai ita d’in matar mnya ce, fara ce tas da ita a q’alla shekarunta bazasu Gaza 37 ba, dayake bafulata na ce ita sosai.
(Hj umaima knn) hannayenta d’auke da wani dogon file ta q’araso ta zauna inda mai gidan nata yake wato Alhj mua’azzam saraki, zaune yk yana aikin duba wasu files files d’in dake gabansa na ofice d’inshi a nutse.
Zama tayi bisa 6arin jikinsa idanunta sunyi rau rau sun cika taf da q’walla, nan danan kuma ta sakar masa kuka mai cin zuciyar mai sauraro.
da sauri mu’azzam saraki ya maido hankalin sa gareta gaba d’aya bayan ya ture aikin da yake yi a lokaci d’aya.
Hannayenta ya ruq’o ya sanya cikin fuskarsa yayi shiru yakasa furta komi bayan duba file d’in hannunta d’in da yayi shima, hankalinsa ba q’aramin tashi yayi ba ganin irin baya nan da file d’in ya q’unsa a cikinsa.
Cikin muryan kuka tace “nuree kaga alamu sun nuna bazan ta6a haihuwa ba a rayuwa ko?!”
Tun da likitoci sunce wai ita d’in mahaifana bazata iya d’aukan cikin kaba nuree?,
Nuree mike faruwa ne damu haka?
Allah yayi mana Arziq’in dukiya Amman bai bamu yara ba yau shekara 17 knn da aurenmu nuree Amman na Gaza haifa maka d’a?
wayyo ni Allah na”!
Nan da nan ta sake fashewa da wani matsanancin kuka mai girgiza jiki d’in nan.
Kamota yayi yana shafa bayanta alamun rarrashi shima kukan zucin yk wnda yafi na sarari ciwo.
Ya zasuyi da ikon Allah ne to?
inda dai Allah bai basu ba sai suyi haq’uri, wataq’il ma d’an ba alheri bane a garesu yanzun shiyasa Allan bai basuba sai dai ya azurtasu da arziq’in Wanda har kullum suke temakon bayin Allah dashi.
Sauke ajiyar zuciya yayi ya rufe idanuwa sannan ya sake bud’esu jin tayi shiru da kukan alamun tayi tayi har ta gaji sai sauke ajiyar zuciya da takeyi,
minti wajen 11 suna a haka sannan ya duba yaga har tayi barci mai tattare da wata irin sabuwar shessheqar ajiyar zuciya sbd wahalar kukan nata data sha.
Girgiza kai yayi na tsananin tausayinta sannan ya gyara mata kwanciya anan wajen sannan ya sumbaci gefen ha6arta ya miq’e kai tsaye ya shiga part d’in mahaifiyarsa wato *Annah*,
farar bafillatanar dattijiwa mai Addini da sanin yakamata.
Ganin ta zaune kan carpet sanye da farin hijab tas dashi tana lazumi Wanda hakan ya tabbatar masa da sallar walha ta gama tana lazumi,
Agogon hannunsa ya kalla yaga 11 saura a lokacin, waje yasamu ya zauna kan d’aya daga maka maka grass carpet d’in dake falon Annah d’in, dan jiyayi Sam bazai iya hawan kujeran ba Dan har yanzu zuciyar sa bata samu sukuni ba, bakomi a cikin ta sai tsananin tausayin umaimah dan gane da rashin haihuwar da batayi ba,
Tagumi ya rafka tareda rufe idanunsa zuciyarsa na wani irin d’as d’as,,,,
Jin an janye hannunsa daga tagumin ne yasa yayi saurin kallo wajen,
Annah ce ta zauna gefensa har lokacin hijab d’in na jikinta da cazbahar ta tana ja, dan ita abin ma ya zame mata jiki kullum cikin lazumi take, kokuma taita karanta addu’oe cikin hadith hadith nata.
A hnkali mu’azzam saraki ya sunkuya tareda furta “ina kwana Annah?
An tashi lpia?”
“Alhamdulilla yarona, Amman dai kasan tagumi ba abu ne mai kyau ba ko?
Baice komi ba sai Murmushin da ya d’an kalato da q’yar sannan ya miq’a mata file d’in hannunta yace
“Annah wannan shine sakamakon da wannan baturen Dr nayz yayi a bincikensa na zuwan da umaimah tayi jia Egypt dan duba lpiar mahaifar nata”!
amsar file d’in tayi sannan ta janyo medical glass d’inta ta sanya mai q’ara q’arfin ido,
sannan ta bud’a file d’in ta fara dubawa itama,
Takusan minti 5 tana q’ara maimaita karanto file d’in itama sannan ta d’ago kai cikin yankewar zuciya ta dubi mua’azzam tace
“yarona?”
D’agowa yayi ya dubeta ya sake maida kansa q’asa yace
“na’am Annah”
Annah taci gaba da cewa “Kuyi haq’uri, insha Allah komi yayi farko zaiyi qarshe, Allah kad’ai yasan nufinsa akan hakan shiyasa bai Baku haihuwan ba, bakomi Allah yasa hakan shi yafi zama mana alheri gaba d’aya”.
nan ta dunga tausar sa da rarrashinsa tana mai q’ara fad’i masa yawan ladan da wad’anda Allah bai basu haihuwa ba suke samu sakamakon haq’urinsu da juriya kan jarabawar da ubangiji ya saukar musu a Kansu.
Cikin lokaci q’anqani kuwa yaji ya rage damuwar sosai Annah tace
“tashi to katafi office Allah shi taimaka,
kuma zan shiga wajen ita umaimah d’in itama zan tausheta abinda haq’uri bai bayar ba ai kuma dai banga dalilin da tsiya zata kawo sa ba,
Mubar komi ga Allah zai kawo mana mafita insha Allah”
“Hakane Annah nagode q’warai,,,, madalla da uwa ta gari “!
Haka mua’azzam
saraki yaje ya shirya direbensa yaja su suka fita zuciyarsa a d’an sauqaqe sosai.
Saida dare ne suna kan carpet d’insu na nan falon inda suka saba cin abinci,
da yake ita Annah Sam bata iya hawan dining table d’in suyi dinner shiyasa suke zama q’asa indai tana nan gidan nasu bata koma can mahaifar su ba wato (katsina).
suna cin abincin ne bayan sun gama anan ita Annah d’in ta dingi tausar zuciyar umaimah itama kamar yanda taiwa mu’azzam saraki shima d’azun gameda result d’in doctor,
har ta q’ara da cewa “kuma ay bnda abinki d’iyata miye ma na damuwar to? ay result d’in doctor bana Allah bane, kawai dai mu d’auka cewar Allah bai kawo haihuwar bane shiyasa.
Dayake Annah ta iya tafiyar da lafazinta a tsanake cikin *Fasaha* shiyasa komi na jikin umaimah yayi sanyi ta shiga furta Astagfurullah cikin zuciyar ta na ganin kamar tayi bore wa Allah ne akan abinda bai basu ba a lokacin da suka so su kuma.
Haka koda zasu kwanta saida sukayi nafilolin su suka roq’i ubangiji Allah ya kawo musu mafita….
Asalinsu…
Mu’azzam saraki shine cikakken sunan sa,
babban ma’ikacin government ne Wanda a q’alla Albasshinsa duk wata zai tasamma 5 million, sannan gefe guda ga manyan kasuwancin sa da yake yi na shigo da gold, diamond. motoci, yana saidawa ‘yan kasuwa, sannan kuma ga gidajen mansa Suma Sama da guda 15,
shiyasa kaf fad’in nijeria babu inda zakaji an ambaci sunan *Alhj “mu’azzam saraki*” ba’a san shi ba,
Yana yawan zuwa kai temako a gidajen marayu, isslamiyyu, data Almajirai, haka nan inya samu change yakansa direbensa ya jasa ya kai sa anguwannin dayasan akwai talakawa sosai mabuq’ata ya dinga yi musu kyautar ban girma Harda masu muhalli duk yana basu wa marasshi, irin wadanda ruwa ya zubdawa gidaje,
Shiyasa har murna suke marassa q’arfi ace yau ga Alhj mu’azzam saraki yazo sunsan ranar take salla a wajen su, dan zai basu abinda zasu yi shekara 3 dashi suna juyawa dan kasuwanci,/ noma, ammanfa ga masu burin cikinsu,
Shiyasa addu’a kullum Shanta mu’azzam saraki yakeyi a maban bantan bakunan Al’umma.
Asalinsa d’an katsina ne, mahaifinsa Alhj muntari saraki ya rasu tun yana Q’arami, a hannun mamansa hajara ya taso wacce yake kira da Annah, Ta haihawa kafinsa Amman duk Allah yayi musu rasuwa yaran tun suna q’ananu,
mu’azzam ne yayi tsawon rai cikin rayawa ta ubangiji Allah.
Cikin dangi suke luntsum shiyasa mua’azzam Sam bai san maraici ba, Allah yabasa dangin baba da mama masu zuciyar yi.
Q’anen mamansa shine ya tsaya kan karatunsa har ya girma ya had’asa aure da babbar d’iyarsa umaimah dashi mu’azzam d’in ya nuna yana sonta Wanda dama itama umaimah hakan yake a cikin zuciyar ta.
Lokacin har ya fara Aikin gwamnati harma ya gina gidan sa plate house mai kyau, anan suka fara zama kusan tsawon shekaru 12, sannan akai masa q’arin girma Wanda hakan ya kaisa aiki garin Kaduna shekara 5 kenan da komawar tasu kd, Wanda tun tsawon shekarunn nan Allah bai basu haihuwa ba, lokacin arziq’in sa kuma sai q’ara bunq’asa yake,
Duk bayan lokaci sukanje katsina su d’auko Annah tai musu kwanaki a gidan takoma can katsina,
Bacin sunyi sunyi da ita kan ta dawo gidan da zama taq’i fur, sai dai a zuwan tazo musu Hutu ta koma can.
Wanda yau kwananta 11 kknn da zuwa gidan d’an nata Hutu,
dan su kansu ‘yan uwansa ba q’aramin cin arziq’in Alhaji mu’azzam sarakin suke yiba,
Wannan kenan.
***
Washe garin ranar ta Asabar dukkan su 2n mua’azzam saraki da matarsa umaimah suka dinga jinsu cikin farin ciki haka nan, bayan sun gama break fast ne nan umaimah ta shige jikin Annah tanawa mu’azzam gwalon tarigasa d’alewa jikin Annahn tasu.
Lokaci d’aya kuma ta tashi tace “yawwa Annah daman nai niyar bazan fad’i wannan mafarkin nawa a gabnsa shi d’aya sai anan gabnki, dan wataq’il abinda Nike so yai mun kmr ynda nasa rai zaiq’i amin cewa ammn in agabnkine zakisa yayi mun”
ta q’arshe maganar kanta a langwa6e.
dukkan su daga mu’azzam saraki har ita Annah sun zubawa umaimah ido da tunanin mita mafarkato??
Annah tace
“to shiknn ‘yata fad’a muji muna sauraronki,
Cikin sunne kai qasa umaimah tace
“Annah jiya ne nayi wani mafarki,
Wato bayan munyi nafilar dare mun kwanta barci,
Nayi mafarki ne wai gani da wani yaro ga hannuna Wanda bai wuce shekara 3 ba, wlh Annah yaron kyakkyawan gaske ne kuma,
nazo wucewa nagansa zaune cikin wasu yara da yawa suna wasa, yana ganina yazo da gudu ya rungumeni kamar ya sanni yana fad’in “Mammy na !” “Mammy na !”
zan zauna dake,
ki kai ni gidan ki wajen babana….!!!
“Annah wlh nan muka zauna da yaron cikin yaran munata wasan tare Amman yaron nan yana manne jikina nima naji banson rabuwa dashi,
Dan a lokaci d’aya naji q’aunar yaron a raina, to muna nan zaune zuwa bayan wani lokaci saiga wata mata tazo ta kwashi yaran har dashi yaron Wanda da q’yar ta samu yabar jikina suna tafiya naga yanata waiwayena tareda mun bye bye,
nima bnsn snda na d’aga hannuna ina masa bye bye ba, har naga sun shiga wani babban gida Wanda naga an rubuta a saman gidan saman wani q’aton symbol, *GIDAN MARAYU*,
to kuma a dai dai nan na farka hankalina a tashe ,,
D’an dakatawa tayi sannan ta miq’e zaune tayi durq’uso a gabnsu tareda had’a hannayenta biyu muryarta na rawa taci gaba da cewa “Annah? nuree? dan Allah Ku yarda Ku amince muje gidan marayu mu samo yaro Wanda zai yayemun damuwar rashin q’waina a duniya, wataq’ilama ta sanadiyyar kulawa da marayan Allah ya jiq’anmu ya bamu namu rabon, Dan wnda ya temaki mabuq’aci tabbas Allah bazai q’i saka masa da mafi alherin sa ba,
Annah nasan kunsan haka kuma, dan Allah Ku amshi q’oqon barana da nazo muku dashi” magana takeyi wasu siraran hawaye na sauko mata a fuska.,
dukkan su sunyi tsit Sai Annah ta dubi mu’azzam saraki shima ya dubeta kuma,
Duban umaimah Annah tayi tare da girgiza kanta tace….
Mahabeer Hausa Novel Page 2
“Duban umaimah Annah tayi tareda girgiza kanta tace “anya kuwa ‘yata hakan mai yiyuwane?”
Shiru umaimah tayi kanta na a q’asa idanunta na zubda hawaye.
Kan Annah ta q’ara cewa wani Abu mu’azzam saraki yayi saurin cewa
“To jeki in mun d’auko shi yaron ma mun riq’eshi inya girma kinsan da sanin dai cewa zai tambayemu inda haq’iq’anin iyayensa suke dai ko?
Sai muce masa mi to a lokacin to knn?
Cikin rawar muryar kuka ta d’ago tace
“kayi haq’uri nuree,
in muka d’auko shi zamu nuna masa mune iyayensa ay har girmansa kaji nuree dan Allah ku taimaki rayuwa ta ku amince wlh jinake kamar zan mutu in zuciyata bata samu abinda take so ba.
Ajiyar zuciya Annah ta sauke tace “to in muka nuna masa hakan mu mune iyayensa mutanen duniya fa ai sun sani,
Cikin sauri da kyarmar murya na wacce ta gaji da kuka umaimah tace “A’a Annah ba zasu sani ba indai mukabi tsarin da nike tunanin zan fad’a muku shi yanzun.
Annah tace to fad’i tsarin naki sai muji ai,
“Annah zaki buga musu waya can family namu na gida katsina kice ashe jimawar da kikayi kina rashin lpia har na tsawon wata 8 baki zo ba to ashe inada ciki Wanda mukaso muyi shiru har sai na haihu dn inkunji labari kuyi mamaki, to zuwanki shine kikaga cikin a jikina wnda harma ya isa haihuwa to shine kuma kika bugo danki fad’a musu sutayamu murna da addua,
faq’at Annah hknma in kikace musu ya wadatar dan nasan zasu yarda ne duka,
To kinji wannan shine shawarana nasan kuma Kun aminta da ita.
ganin sunyi shiru babu wnda yace komi tsakanin mu’azzam saraki da ita Annah yasa taji zuciyar ta ta sake karewa tasan ma q’ilan bazasu amince ba, nan ta fara rusa musu wani sabon kukan tana binsu da rarrafe tana kama q’afafunsu tana zubar da hawaye.
Cikinsu Babu wnda zuciyarsa bata kare ba ya tausaya mata ganin ynda ta q’wallafa ranta akan son ta ganta tana renon d’a.
A zuciyar mu’azzam saraki q’warai yaji tausayin umaimar tasa har yaji cewa a zuciyar sa indai daga garesa ne to ya amince zasuje gidan marayu d’in su dauko yaro.
Sai dai bai San ita a zuciyar Annah d’in tasa ba ya abun yake ne?
Kamo hannayenta Annah tayi ta kwantar da kanta bisa 6arin jikikinta na dama tana rarrashin umaimah tace
“Tabbas Wanda ya temaki wani Allah zai temakesa kamar yanda kikace umaimahtu, to sai dai kuma nidai a zuciyata dukkanta na amince da wannan tsari naki Amman saiki nemi amincewar mijinki gashi nan,
inya amince to Alhamdulilla gobe kam lahadi insha Allah zamuje can gidan marayu d’in mu samo yaro d’in.
Mu’azzam saraki yace “Annah ai inda har kin amince nima wajena babu sauran tantama na amince.
Murmushi Annah tayi tace “to shiknn ay Alhamdulilla masha Allah Allah tayamu riq’o,
gaba d’ayansu suka amsa da
“Ameeen”.
Tsananin farin cikin fuskar umaimah kuwa kasa 6oyuwa yayi a ranar,
dan kamar wadda akaiwa albishir da samun shigar ciki a jikinta abin nema.
da dare yayi kuwa kwana sukayi tana gigita mu’azzam saraki da salon ta na soyayya a shimfid’ar auren su, shiyasa har cikin jini da tsoka yake jin bashi ba iya jin zai q’arawa umaimah di’nsa kishiya har iya muddin rai kuwa!.
Washe Gari bayan sun gama komi da misalin 4 na yamma suka fito harabar gidan a shirye,
wani kurtun soja wnda a q’alla shekarunsa zasu kai 58,
baq’i ne q’aqqarfa, wato d’aya daga masu tsaron gidan knn, shi ya jasu a mota suka fita.
dai dai q’ofar q’aton ofis d’in gidan marayu d’in motarsu ta tsaya.
Har ciki suka shiga bayan an musu iso a babban ofishin marayun.
Bayan sun zauna an gaisa mutumin shugaban wajen har lokacin bai bar rawar jikin ganin Alhj mu’azzam saraki ya ziyarcesu ba ynxu kuma
ba kamar tym d’in da ya saba zuwan musu ba.
Anan mu’azzam saraki ya fara fad’a masa abinda ya kawo su wajen. mutumin yace
“babu matsala Alhj, Amman bamusan kamar ‘Yan shekara nawa kuke son a bakun ba?,
duban umaimah yayi cikin murmushi ta d’aga masa q’aramin yatsan hannunta murmushi yayi shima dan ya gane nufinta da yayi, inda Annah tk ya kallo yaga tana lazuminta batasan mima suke ba.
Mu’azzam saraki ya dube mutumin sannan yace
“kunada jarirai sabuwar haihuwa ne?”
da sauri mutumin yace “yes Alhj akwai su dan cikin satin nan suma akafi kawo mana akan manyan, so ynxun zamu iya shiga ciki dan ku duba.
hakan kuwa suka shiga cikin gidan d’akin da ake ajiyar jariran, anan suka shiga kai tsaye,,
duk yawan jinjiran wajen shigarsu da tsayuwarsu a minti 5 bai hana tun daga nesa umaimah ta hango wani baby kyakkyawan gaske nannad’e cikin farin showel a hannun nanny d’in su wacce Ke sanye da fararen kaya itama a jikinta sai farar hijab da farin glass a saman fiskarta tana riq’e da babyn tana basa madarar sa a feeda.
da sauri umaimah ta isa wajen su ta kar6i yaron batasan
Sanda ta furta “tsarki ya tabbata ga mahallicin wannan jinjiri ba, yanda kasan d’an larabawa haka jinjirin yake hanci har baka gashin kansa baqi kwance saman inda hular kansa take,
gashi idanunsa biyu ammn Sam Sam baya da hayaniya,
Kar6arsa Annah tayi baccin ta iso wajen, itama tana kallon sa babu abinda ya fito bakinta sai “tubarakalla masha Allah.”
Shima mu’azzam saraki haka jinjirin yayi matuq’ar shiga ransa shima.
Nan mutumin ya q’araso yace
“Alhj yayi muku wannan jinjirin ko?
Da sauri umaimah tace “eh yayi,
shi mike so abamu.”
dunan nanny d’in su mutumin yayi
yace
“nanny d’anki yazo a sa’a, duka duka yau kwanansa hudu da kawowa,”
Har a cikin zuciyar nany d’in tasu bataso rabuwa da jinjirin ba kamar zatayi kuka batasan miyasa ba tafi jin sa akan sauran,
kodan bashida fitina akan sauran ne oho?
Ammn Koba komi taji sauq’i 2 inda mutumin kirkine zai kar6esa ya renesa.
Daurewa tayi tareda murmushi tace “hakane muna roq’on Allah ya tayasu riqo to”.
Anan suka koma ofis d’in suka zauna,
Umaimah kuwa na rungume da balaraben jinjirinta kamar ta lashesa take ji.
Bayan sun zauna
Anan ogan yace
“to Alhj Amman da sauran bayani.,
Mu’azzam saraki yace “kamar Yaya knn mlm mukhtar?”
Gyara zama yayi sannan yace
“to wannan yaron yau kwanansa had’u knn da wata dattijuwa ta kawo mana shi a rud’e ta ajiyesa sannan tace bayanin komi na cikin wata farar takarda wacce Ke jikin jinjirin zata dawo d’aukarsa in komi ya lafa,
Daga haka ta juya ta fita tana waiwayen jinjirin yaron tana kuka.
Bayan fitarta ne na kirawo ita wannan nany d’in nasu mai kula dasu jinjiran,
Nan Nasa ta d’auko yaron, saiga wata takarda fara ta fad’o jikin showwl din yaron.
Bacin mun bud’a takardar abinda Ke a rubuce ciki shine
”Nice mai aikin mahaifiyar shi wnn jinjirin,
iyayensa masu mutuncine da temakawa bayin Allah,
katsam aka haifi yaron wnda haihuwarsa ta tsonewa wata mata daga cikin family nasu ido,
wato matar babansa ta 1, sakamakon yawan dukiyar uban yaron, ita kuma tana uwar gida ace bata haihu ba, sai amaryace zata zo ta haihun tagaje dukiyar gidan knn ma duka?
To wlh bazai yiwuba,!
dare nayi wai zata sa aje a sace jinjirin a kashesa.
ni kuma sai Allah ya q’addareni dajin mugun q’udurin nata lokacin da nazo kawo mata jinjirin data aika In d’aukosa dan aminanta.
Mafarin knn najuya da sauri na maida sa ga mamarsa Nace tace bazata kar6i yaron ba.
To dayake mamar yaron tasan rashin kirkin waccen matar kishiyarta, sai tayi murmushi kawai batace komiba.
Nakasa nutsuwa nikuma nasan kona fadawa uwar d’akin nawa wannan maganar zatace jita jita ne,
Ni kuma ina son tai rayuwa da d’anta, mafarin knn naje na d’auko yaron a boye lokacin mamarsa ta shiga wanka na kawo muku shi nan ajiya da nufin in komi ya lafa zan dawo in kar6esa nan bada jimawa ba.
Gashi nn na barshi riq’o @ hannun ku, Allah shi raya mana kai *MAHABEER*!!! zan dawo lokaci kad’an insha Allah na sadaka da mahaifanka bisslam saina sake kuma juyowa gareka d’an uwa ta gari….!
Yana kawowa nan yace to wannan shine taq’aitaccen tarihin na jinjirin nan *MAHABEER*,:da muka tsinta a tare dashi, kuma da
wannan ne muke roq’onku da cewa koda yaushe ne ita wannan baiwar Allah ta dawo da zummar kar6ar yaron to zamu kawota nan wajenku ta kar6i yaron su kamar yanda mukayi alq’awali da ita.
Yana kaiwa nan
ya miq’ewa tsaye ya d’auko wani q’aton photo album na ajiyan hotunan tarihi na gidan marayun snn ya budo wani shafi yace “wannan hotunan suma still mun samesu ne a jikin showl na jinjirin,
Anan nagane harda ita dattijuwar matar a hoton,
Kungan ta nan ma.
Nan yafara nuna musu kowa na gani cikin mamaki, Wannan daga ganin kamarsu itace mamar shi jinjirin *MAHABEER* nikega,
inda gashinn hannunta kuma.
Sannan ya q’ara nuna musu wani photo inda aka d’auki MAHABEER d’in shi d’aya yanata barci abinsa lpia.
Tashin hnkali ya ziyarci zuciyar umaimah a lokacin dataji abinda mutumin Ke fad’a na zai rabata da MAHABEER d’in ta in iyayensa sunzo karbar abinsu, Wanda takeji duk duniya batajin akwai abinda zaisa ta iya rabuwa dashi dan a shirye take data bada ranta fansa ga jaririn…
Mahabeer Hausa Novel Page 3
Qara ware idanunta umaimah tayi kan hoton tana kallon mamar shi mahabeer d’in, wnda kowa ya gnta kuwa yasan tabbas itace dai mamarsa sbd kamarsu d’aya sak,
Sannan ga kuma ita wannan dattijuwar matar da akace ita ta kawosa a gefen mamar MAHABEER d’in suna dariya aka d’auki photon. Maganar da taji mu’azzam sarakin na cewa ne yasa hankalinta dawowa wajen kacokam!
“To shiknn mlm mukhtar bakomi, Allah shi kaimu lokacin da rai da lpia kuma,
ay kasan shi cika alq’awali abune muhimmin gaske a dukkan rayuwar d’an Adam.”
Nan mu’azzam sarakin dai ya cike file d’in da shi mlm mukhtar d’in ya basa ya ciken,
da kuma dai sauran abubuwan daya kamata yayin duk yayi su lokacin gaba d’aya,
Sannan da zasu tafi kuma ya cikasu da kyaututtuka suda kingin marayun gidan,
A lokacin kuma suka kamo hnya suka dawo gida.
Suna shiga falon gidan kuwa umaimah tayi saurin kar6ar yaron daga hannun Annah tana murmushin murna ta shige d’aki dashi ta goyeshi ram a bayanta ta fito falo tana zagayawa dashi,
shi kuwa sai mutsu mutsu yake yana q’oqarin tura hannunsa a baki ga alama mamansa yake son sha bai ishesa ba.
Annah kuwa sai binta da murmushi kawai take yi,
Sannan Annah d’in ta d’auko wayanta tafara gayawa ‘yan uwa da abokan arziq’i haihuwar,
nan da nan kuwa akaita kiran iyayen jaririn ana musu murna sukuma suna amshewa cikin farin ciki.
Ranar kamar umaimah ta zuba ruwa a q’asa tasha Dan murna,
nan mu’azzam ya kirawo family doctor d’in su yace yana so ya siyo masa madarar da yasan ana bawa jinjirai in ruwan nono yaq’i biyawa.
Ba’a d’au tsawon lokaci ba sai gashi kuwa doctor d’in ya kawo madarar katan katan.
shima yai mamakin ganin jinjirin nasu.
Amman kuma da suka fad’a masa abinda suke fad’awa sauran sai ya yarda shima, duba da shi kansa ma yajima rabon sa da garin sai kwanan nan ya dawo sakamakon canjin wajen aiki daya samu.
Nan aka had’awa baby milk d’insa,
ita ya wuni sha abinsa.
Washe Gari kuwa abokanan umaimah sukaita zuwa ganin jinjirin kowa ya gnsa sai yayi santin yaron matuq’a.
‘Yan katsina suma tun ranar suka fara durowa gidan haihuwar har zuwa ranar suna inda akasha shagali na kece raini kusan sati ana shagalin kuwa bai q’are ba,
Hatta abokanan mu’azzam saraki sukan zo takanas dan ganin jinjirin tareda ajiye masa kyaututtuka masu nauyin gaske.
Gskia kam baby yasamu dukiya ta ban mamaki, shiyasa babansa mu’azzam saraki ya bud’e masa account kawai yana zuba masa kyautarsa daya samu.
Kullum Annah tana tare da MAHABEER itama bacci kawai ke maidata d’akinta dan tana matuq’ar son sa itama sosai.
Haka suke rainon d’an nasu cikin farin ciki har yau gashi yayi wata 6 zuwa lokacin harya karya qafarsa wato ya fara rarrafawa knn abinsa gwanin sha’awa.
A lokacin ne Annah ta koma katsina cike da kewar MAHABEER.
Amman tun zuwan MAHABEER gidan Annah bata d’aukar tsawon lokaci bata zoba gidan d’an nata ba kamar da ba da zasuyi ta fama da ita ma akan tazo sai ta q’iya wai a cewarta jikin tsufa ciwo baison tafiye tafiye…
Shima MAHABEER ya fara sanin Annah shiyasa daya ganta tazo gidan har wani murna yake da zullon son ta d’aukesa Dan ya tantanceta a yanzun shima sosai.
Kullum kyansa q’ara fitowa yake na sak jinin larabawa….
‘Yan magana sunce shekara bata gadon shekara yau har MAHABEER ya cika shekara 5,
A lokacin har an sanyasa nusry one a school.
Akwana a tashi har gashi ya gama nusry t primary har ya shiga secondary lokacin.
Allah yai masa brain shiyasa yai suna a school d’in su kowa a frnds d’insa zakaji suna fad’in
Gifted MAHABEER.
Tun su umaimah na zullumin yau ko gobe za’a zo d’aukar MAHABEER har suka daina dn ganin an Shari wad’annan shekarun haka Amman kuma shiru kukeji .
Kulawa kuwa ta fannin iyayensa kullum sai abinda yaci gaba kuwa takai yanzun in dai ya samu Hutu shida kansa yake matsawa dadynsa yakaisa katsina wajen Annah Hutu.
Haka zasu tafi kuwa su kaisa shida momynsa umaimah….
Haka lokaci yaketa tafiya kwanaki na zama shekara har gashi yau MAHABEER yayi degree d’insa da masters degree yagama duka.
A lokacin kuma ne
Ya zama wani irin murd’adden mutum q’arfaffa, wato irin giant d’innan ne,
ya ida riked’ewa ya zama hands some guy wani muskilin mutum naq’in q’arin kansa, d’an shekara 29.
A cikin satinne kuma mu’azzam saraki ya tursasa masa fara zuwa office d’insa dashi yayi murabus a kan kujerarsa ya d’ora MAHABEER akai a cewarsa yanzu ba kamar daba, ayyukan zasuyi masa yawa, q’wamma ya tsaya kan fita q’asashen wajen sa yana fiddo da kayan business d’insa abun zai zamo masa da sauq’i hatta al’amurran gidajen man sa da motocinsa na company dinsa ya damqa ragamar komi ga MAHABEER d’in,
Giant man knn,
nera kamar tai masa kuka ga kyaun usuli,…
‘Yan mata kuwa komin nacensu garesa jin kansa da isarsa bazai ta6a iya bari ya d’aga kai ya dubesu ba, muddin bashine yaso ba dan Karin kansa ba.
**
Yau dai a matuq’ar gajiye MAHABEER ya dawo gida,
Parking motarsa yayi sannan ya sa6o labcote d’insa da brife case d’insa, fuskar nan a had’e ya tura q’ofar falon nasu ya shiga.
Ganin saman q’ofar dak’in ammi d’insa a rufe ya tabbatar masa da tana hospital d’in datace masa zataje ganin diyar q’awarta nahnah.
D’akin sa ya wuce ya tulla kayan hannun nasa kan gado sannan ya cire kayan jikinsa ya d’aura towel iya q’ugunsa ya shige toilet.
Yana fitowa kuwa yaji phone d’insa ta fara ringing a d’an duban harara ya kallo wayar dan baison wani Abu ya gitto ynxu ya damesa a ynda yakejin ya gajinnan over,
Wayar ya d’auko ya duba ganin sunan bash ne yasa shi d’an sakin fuskarsa kad’an shima, sannan ya d’aga yace
“yadai bash kun dawo ne?
Daga can bangaren bash yace
“kai gifted wlh mukhtar d’an iska ne,
yau rabon iv d’in nan na bikinsa da mu kaje nida mas’ud ba q’aramar wahalar damu yayi ba harda imran,
tun safe fa sai ynxun ana magrib muka dawo gida ,
Kai kai kai huhhh,!
Rabon iv ko masifa,
Shiyasa Nace masa
wlh gobe weekend dole ka fito dan a ida rabon nan dakai kaima kaji ynda abun yake inda gobe shine last day na rabon iv d’in.
Ta6e lips yayi yace
“ba inda zanje guys dan kuma sani,
Ni gobe ma KT zanje na dauko Annah ta,
Da sauri bash yace
“kai Dan Allah gifted?
You seriously?
Indai haka ne nima zanje kuwa ka jirani zan zo to muje dan nayi missing Annah wlh a lot nima, Amman Allah sadai ba jirgi zamu hauba?
Dan na sanka kamar tsuntsu kake wajen yawo a Sama.”
ta6e lips ya sakeyi yi dan gajiya da yayi d mgnr sannan yace “don’t mind bash,
a motor zamu indai zaka, but kuma wlh karkamun iskan cinka na lates African time, dan by ten i think zamu wuce ma ok?.”
“OK babu ji ay gifted”
Cewar bash d’in.
Ajiye wayar yayi ya ida goge sauran leman ruwan jikinsa da towel d’in kansa, sannan ya murza sansanyen cream lotions d’insa ya fiddo wata baq’ar Riga irin ta shan iska mai gajeran hannu,
inda ta bayyana masa kwantaccen gashin jikinsa lu6 lu6 gwanin sha’awa. sannan ya zura tree quater d’insa blue shi kuma, fita yayi izuwa kan dining table nan ya iske fried rice wacce Tasha kayan q’amshi, baje baje take da kifi sosai, dama haka yake son ganin fried rice, shiyasa abinda Momy d’insa tafi girka masa knn dan tasan shine choice cook nashi a rayuwa.
Sam baya wasa da cikinsa shiyasa daya zauna sosai yaci abincin sannan yaje yai brush ya nufi wajen games d’insa inda yake motsa jiki nan wajen harabar gidan,
qaton d’aki ne babu abinda ke cikinsa sai kayan exercise a ciki manya da q’ananu an zube su a cikinsa.
Yakai one hour yana exercise a wajaje daban daban na wurin, yayi gudu ya d’aga q’arfe q’aton gaske da hannayen mabanbanta, yayi ta rubda ciki, yayi ta duq’e,
shiyasa lokaci d’aya wani irin mugun gumi ya jiq’esa sharkaf kamar Wanda ya fito cikin ruwa dudda esin dake wajen Sama da guda 5 kuma.
Saida yaji ya gamsu yaji dud wata sauran gajiyar daya kwaso ta ware sannan ya fito yana share zufa a saman fuskarsa da jikinsa da farin towel d’insa,
Nan ya fito ya koma cikin swimming pool yayi iyo nan ma sosai son ransa sannan ya koma d’akin sa ya canzo wasu q’ananun kayan farin jeans da farar Riga mai gajeran hannu Wanda ta bayyana Masa shatin murd’a murd’an qarfin arms d’insa na maji qarfin qarfaffen namijin gsk, yazari keys d’in motar sa ya fito yana shirin shiga motarsa knn yaga shigowr motar mamynsa a gidan.
Da sauri ya nufi wajen cikin takunsa a sassarfa na son ganin momyn tasa.
Amman lokaci d’aya ya tsaya cak dan ganin wacce suke tare da ita a gefenta.
Tuni ya q’ara d’aure d’aurarriyar fuskarsa katamau.
ita kuwa Hannat sai wani fari take masa da idanunta tana karye karye,
Wani dogon tsoki yaja yayi kamar bai gama momyn ba yana shirin kwana ya shige motarsa yaji momyn tasa tace
”ah MAHABEER_? baka ga momyn taka bane ba? ba welcome ba komi alhalin da katafo kuma saika juya?
A hankali ya juyo ya sauke zafafan idanunsa a….
Download Mahabeer Hausa Novel Complete here
Download Mijin Kwaila Hausa Novel Complete