Mijin Haya Hausa Novel Complete
Mijin Haya Hausa Novel Part 1
Gidane d’an ‘karami mai dau’ke da d’akuna
biyu ,falo d’aya,sai tsakar gida,kwance take a
falonta mai tattare da ‘kazanta,tana sanye da
zani daban ,riga daban ,haka zalika
d’ankwali,munshari take zabgawa,tayi wata irin
kwanciya,ta ware kafafu kamar ba mace
ba,miyau yana mai dilala daga
bakinta,sanadiyar mafarkin da takeyi wai gata
chan tana cin tsiren hanta da madara,firgigit ta
farka tana sosa kanta tare da tand’ar bakinta
kamar wata mayya,agogon da’kin idanunta
suka yi mata tozali da,2:00pm idanunta suka
gane mata,da hanzari ta suri mayafinta dake
kan fanka,tayi bol da kwanon da taci
d’anmalele tun shekaranjiya dake kwance a
tsakiyar falon,ta shuri silipas da
‘kafarta,sannan ta fice daga gidan tare da
‘kulle ‘kyauren gidan da kwad’o… * * * Zaune
yake akan benci,ya zabga uban tagumi yana
mai tunanin rayuwa,jin ana buga gate da ‘karfi
yasa ya dawo hayyacinsa tare da tashi da
hanzari ya nufi gate d’in yana tambayar
wanene, ‘ni ce!’ ta bashi amsa da ‘karfi,da
sauri ya bud’e gate d’in tare da cewa ‘HIBBATU
lafiya ,meya faru’ ,harara ta zabga mai tare da
tureshi gefe ta shigo tana cewa ‘ina lafiya kuwa
ga talaka irinka ,da har zakayi tsammanin
lafiya a kowanne lokaci,cefane na biyoka in
amsa’ tana mai yatsina fuska,a sanyaye
yace’cefane kuma hibbatu!’ ,’eh cefane,ko ka
bani ne kafin ka taho nan?’,’amma naga akwai
ragowar kwakin dana siyo jiya,kiyi ha’kuri ,ki
kwad’anta kici mana’,da sauri ta dakatar da
shi tana cewa ‘nayi maka kama da matar da
kwaki zai samu matsuguni a tumbinta,wallahi
ni tsiren hantar danayi mafarki nake son
ci!’,’tsiren hanta kuma?’ ya maimata ,tace ‘eh
tsiren hanta mai zafi da wadatacciyar
‘kuli_’kuli’ ,’bani da kud’i!’ ya bata amsa yana
mai kauda kansa gefe ,tsalle tayi ta dire,ta cire
mayafi ta d’aure a ‘kugunta,tana tafa
hannayenta tana cewa ‘kan ubanchan d’arin
biyun ce baka da ita dan jaraba,wallahi BILAL
dole ka nemo kud’i yanzunnan,in ma ta kama,
ka shiga cikin gidannan kayi masu fashi da
makami mana ,ka tsaya kana ce mini baka da
kud’i,rashin kud’inka bazai sa in fasa cin tsiren
hanta ba,ahtoi!,kai kunya ba kaji ,in taho maka
da karamar bukata irin wannan amma ka kasa
biya min ita!’ ta cigaba da surfa mai masifarta
da bala’i ,bai tanka mata ba,ya zuba mata na
mujiya kawai… Karar Horn! Din da akayi ne
daga wajen gate ne,yasa Bilal ya juya ya bar
ta anan,da sauri ya wangale gate d’in,wata
arniyar azababben mota mai numfashi ce ta
danno kai…..ido,hanci da baki bud’e hibbatu ta
bi motar da kallo.
Mijin Haya Hausa Novel Part 2
wata had’addiyar balarabiyar matashiyar
budurwa daga motan yasa bilal ya biyewa
hibbatu wajen kallon wannan had’addiyar
budurwa a ransa yana mai tasbihi ga
Allah…hibbatu ta maido dubanta ga bilal,ganin
ya saki baki shima yana kallon wannan
budurwar ma’abociyar kyau yasa a take kibiyar
kishi ya soketa,tasa hannu ta bugi ‘keyarsa
tana cewa ‘haba bilal,akwai wata halitta da
zata gigita ka bayan ni?’ ,murmushi yayi a
sanyaye yace ‘babu kam hibbatuna,ina ni ina
yar masu gida,tsakanina da ita sai dai kallon
,ke d’in ma danake aure ya na ‘kare ,malajawa
kawai kike dani’ ,dariya hibbatu tayi tare da
kunce d’amarar da tayi da mayafinta tana cewa
‘ashe baka manta da matsayinka,hakan na da
kyau ‘,sannan ta yafa mayafinta tana mai cewa
cikin rad’a ‘kace kuma yar masu gidan ce,waya
gaya maka haka’ ,ya bata amsa da cewa’alhaji
da kanshi yake ce mini wai yau d’iyarsa MEERA
zata dawo daga cyprus domin ta kamalla
karatu’ ,hannu akan kirji hibbatu ta maimaita
‘sifurus?’ ,sannan ta juya ta nufi cikin gidan
tana cewa ‘banga ta zama ba,dole in ‘kulla
aminci da wannan ‘yar ,ko nima zan yagi
rabona’ wuf ta shige kofar da zai sadata da
cikin gidan,bilal ya koma kan bencinsa ya
zauna bayan ya rufo gate d’in yana mai
mamakin hibbatu,ajiyar zuciya ya sauke tare da
cewa ‘ALLAH yasa kar hibbatu tayi sanadin
rasa aikina’
DOWNLOAD BELOW
Nigerian Super Eagles
We pray that Nigeria wins this upcoming match