Hausa Novels

Download Rufaffiyar Zuciya Hausa Novel Complete

Rufaffiyar Zuciya Hausa Novel Page 1 and 2

” Amma lalle wato duk wahalar damuka sha amma ace bamu samu wannan ‘kwangilar ba to Wllh sede kowa yarasa nasha alwashin Wllh sede Alhaji Isma’il yayi wannan ‘kwangilar a lahira ”

” idan kayi haka kayimin dede Alhaji Sambo dan Alhaji Isma’il yari’ke mana wuya komi shi haba ay gara muyi maganin matsalar mu kawai ”

Cikin tashin hankalin wanda ke la’be yanajin komi dasuke tattaunawa yayi saurin barin gurin Cikin sauri yashiga cikin motar shi gudu yakeyi sosai cikin wata anguwa yanufa kai tsaye wani katafaran get yanufa kimanin 2 sannan aka wangale ‘katon get d’in yana shiga yanufi parking space ko gama gyara parking baiyiba ya kashe motar yanufi ciki

Knocking yayi sannan aka bud’e Cikin damuwa yace

” kayimin iso gurin Alhaji ”

Murmushin yayi sannan
yace

” ay barrister bakada shamaki da ganin Alhaji amatsayina name kare lafiyar shi yace idan har kai to nabar ka kashiga kai tsaye ”

Godiya barrister yayi sannan yashiga cikin babban parlour yasami Alhaji Isma’il gani barrister a wannan lokacin yasa Alhaji Isma’il mamaki dan basu dad’e da rabuwa ba umarnin zama yabashi sannan yace

” barrister Allah yasade lafiya ? ”

d’an jim Barrister yayi sannan yace

” gaskiya Alhaji babu lafiya ”

Nan ya kwashe komi dayaji yasanar da Alhaji cikin tashin hankalin da damuwa yace

” karka damu Barrister babu wanda ya’isa yayi min abinda Allah bai yarda ba nide abinda nikeso dakai dan Allah koda sun kasheni kari’kemin amanar dukiyar Affan wadda ke wajan ka sannan kakulamin da shi shida mahaifiyar shi su kad’e gareni ”

Jinjina kai Barrister yayi sannan yace

” in sha Allah Alhaji amma ni senike gani dakabar gidan nan harzuwa wani lokaci ”

Murmushi Alhaji Isma’il yayi sannan yace

” barrister ay baka gujema ajalin ka idan Allah yasa sesun kashe ni to duk inda naje bazan tsiraba amma zuwa gobe kazo kad’auki Affan nikam shi nikeji ”

Cikin damuwa barrister ya amsa sannan yayi mai sallama yafita cikin sauri Affan yabar jikin ‘kofar dan yaji komi

Misalin 09:00 pm

Affan nakan cinyar mahaifin shi wato Alhaji Isma’il Affan yarone d’an kimanin 14 years shi kad’e Allah yabasu shiyasa yake cikin tsananin gata Cikin tsantsar soyayyar d’an nashi Alhaji Isma’il yace

” Affan ina kake son in kaika kacigaba da makarantar gabada Secondary ? ”

Shiru babu amsa ta’be baki Hajiya Aysha tayi wato mahaifiyar shi tace

” gaskiya Affan wannan miskilancin naka yana bani haushi wai ace hadda mu iyayen ka yaro tun yana ‘karami se shegen miskilan cin tsiya to idan kagirma yaya kenan am……. ”

” a ‘a hajiya kibarshi karki takura shi nazari yakeyi ”

Tashi Affan yayi sannan yace

” Abba Saudiyya nikeso dan banason naje wata ‘kasa na d’akko halin yahudawa dan natsani rayuwa marar tsafta ”

Yana ‘karashe fad’ar haka yanufi cikin bedroom d’in shi Kallo suka bishi dashi cikin farin ciki Alhaji Isma’il yace

” nagode ma Allah koda bana raye inasa ran insha Allah Affan ba zaiyi abunda babu amfani a rayuwar shiba ”

Tashi Alhaji Isma’il yayi yabishi har cikin bedroom d’in shi hannun shi yamako suka nufi bedroom d’in Abban suna shiga yasama door d’in key sannan ya zaunar dashi kan cinyar shi system d’in shi yakunna yanunama Affan yadda password d’in bud’e ta yake sannan yacigaba da nunamai wasu documents nashi aciki masu mihimman cin tashi yayi ya d’akko wani d’an box wasu numbers yasaka sannan yabud’e

Nuna ma Affan yayi takardun Companys da na gidaje da filaye se keys na offices dana motoci sannan yarufe Kallon shi yayi sannan yace

” kasaka duk Numbers d’in da kake ganin yayima kuma zaka iya ri’kewa guda 6 Sabida nasan nan gaba kaine zaka bud’e wannan box d’in kuma inaso karka sake kanunama kowa koda mahaifiyar kace Sabida nasan tanada son abin duniya zata iyayin komi sabida kud’i ”

Cikin wani yanayi Affan yasaka wasu Numbers sauka yayi daga jikin Abba yace

” Abba maiyasa bazamu bar gidan nan ba koso kake nazama maraya tun ina ‘karami na ? ”

Cikin damuwa Abba yace

” karka damu Affan koda bana nan katambayi Barrister duk abinda kake son sani kuma kake bu’kata kaji nayarda da barrister bazai cutar dakai ba ”

Kuka Affan yafarayi yace

” Abba idan har babu kai a duniya to zan zama mai RUFAFFIYAR ZUCIYA Abba ina kakan nina suke ? kasan…… ” jin ‘karar harbin bindiga yasa Alhaji Isma’il saurin kama hannun Affan had’i da d’aukar wannan box d’in da System wani d’aki yaturashi yami’ka mishi wannan box din da System yace karya sake yafito komi zaiji key d’in d’akin yami’ka mishi sannan yasumbaci goshin shi saurin rufe ‘kofar yayi ya gyara labulan babu yadda za’ayi kasan akwai d’aki agurin hawayen idanun shi yashare sannan yafita parlour bedroom d’in Hajiya Aysha yanufa cikin tsoro da fargaba

Rufaffiyar Zuciya Hausa Novel Page 3 and 4

Yana shiga Hajiya Ayshat tayi saurin ‘karasowa gareshi cikin tsoro da fargaba tarungume shi shima rungume ta yayi yana sauke wani irin numfashi jin sautin maganar mugayen dasuka shigo yasa Alhaji Isma’il saurin maida matar shi bayan shi cikin d’aga murya d’aya daga cikin su yace

Alhaji karka ‘bata makanka lokaci muma ka’bata mana gara kafito idan kuma ka’ki fitowa to zamu bankama gidan ka wuta kowa ya’kone kaga kasa’ba mana tsarin aykin mu sabida kai kad’ai akace mukashe ”

Jin haka yasa Alhaji Isma’il sauke wata irin ajiyar zuciya juyawa yayi kan Hajiya Aysha yace

” ina ro’kon ki da kiri’ke min Affan kamar yadda zan ri’ke shi kibashi farin ciki kamar yadda zanbashi karki bari Affan yayi kukan rashina dan Allah dukda nasan tsakanin d’a da uwa se Allah nasan zaki kuladashi fiye da yadda nizan kulama da sha kinga yanzu ke kad’e gareshi kisanar dashi al’kawarin auran ‘yar d’an uwana Seeyama karki bari wani yacinye dukiyar d’an ki ku tattara komi kukoma ‘kasar mu San……. ”

Jin sun’karayin magana yasa Alhaji Isma’il yafi cikin sanyin jiki bayan shi Hajiya Aysha tabida Kallo cikin zuciyar ta tace

” nikam wannan lamarin yayi min dad’i yanzu zan juya acikin d’aula duk wanda yasa aka kashe ka nikam yayi min dede lokacina yayi Affan dukda kake d’ana bazan tausaya makaba akan wannan dukiyar wannan tawace kaje kanemi taka ”

Jin ‘karar harbi yasa Hajiya Aysha sakin murmushi shiko Affan yanajin haka yayi saurin fitowa kai tsaye parlour yanufo sukam makasan harsun bar gidan kan Abban shi yayi yana kuka yana kiran sunan shi cikin sar’kewar murya Abban yari’ke hannun shi yace

” kayi ha’kuri Affan zanfati nabar ka alokacin dakake tsananin bu’katata ina maiyima nasiha da karka sake kabud’ema kowa zuciyar ka se Wanda kayarda dashi tsananin yarda dukda gashi ni wa inda nayar da dasu sune suka ayko akashe ni ina mai umartar ka da idan kakammala karatun ka kaje Sudan ka amso auran ‘yar uwar ka Seeyama ‘yar wajan ‘kanina ce dukda bakasan ta’ina zakafara neman suba amma katambayi mahaifiyar ka zatasanar da kai komi ”

Zoban hannun shi yacire yasama Affan cikin hannun shi sannan yace

” Affan karka sake kayi wata ‘kazamar rayuwa bayan ‘kasa tarufe idanuna ban abince da hakan ba kuma idan kayi bazanyi farinciki ba Affan …….. ”

Wani irin tarine yatasoma take yafara fidda jini cikin bakin shi kafin wani lokaci Alhaji Isma’il yatafi inda kowa zaije cikin kuka Affan ke ‘kwala kiran Momy Momy jin haka yasa Hajiya Aysha tayi saurin fitowa

Cikin kuka tayo kan Alhaji Isma’il amma kukan baikai cikin zuciyar taba tanayine dan ganin idanun Affan cikin tashin hankalin Affan ke cewa

” Momy kisa drive yad’akko mota mukai Abba asibiti ”

Kallon shi tayi sannan tace

” Affan lokaci yayi sede muyi ha’kuri zuwa asibiti bazai dawo da ran Abban kaba ”

Cikin kuka Affan yabud’e hannun shi zoban da Abban yasaka mishi yazubama idanun take maganar da Abban yata’bayimai akan zoban tadawo cikin kanshi inda yake cewa

” bayanzu zan baka wannan zoban ba se ranar dazanyi wata tafiya mai nisa aduk lokacin da wannan zoban yazo hannun ka to kari’ke shi da matu’kar daraja sabida wani dalili kuma zaisa kadinga tunawa dani akoda yaushe nasan zaiyima a wancan hannun tunda ni a ‘karamin yatsa yake Affan ina alfahari da kai yarona ”

Wasu irin hawaye ke shatata a cikin idanun Affan cikin kuka yace

” nima ina alfahari dakai Abba na kuma sena gano duk wani mai hannu acikin kisan ka Abba bazan bari ranka yatafi abanza ba komin dad’ewa sena ganosu ”

Cikin sanyin jiki yasaka zoban cikin hannun shi mi’kewa yayi take nan jiri yakwashe shi yafad’i a sumai cikin gigita Hajiya Aysha tanufi bedroom d’in Alhaji Isma’il wayar shi tad’akko cikin rawar hannu tadanna kiran Barrister adede wannan lokacin Barrister yana cikin parlour shi yakasa koda zama ya’kosa gari yawaye yaje yasa Alhaji Isma’il barin garin kota halin yayane ganin kiran shi yasa shi d’aga kiran cikin sauri

Jin muryar Hajiya Aysha kuma cikin kuka yasa Barrister zama cikin tashin hankalin take yaji wata’irin zufa tana ketomishi cikin sauri yatashi yanufi bedroom d’in shi bindigar shi yad’auka sannan yakira jami’an tsaro yasanar dasu fita yayi yana shiga motar shi yafige ta aguje cikin mamaki matar shi ke Kallon fitar shi ta window jin maganar ‘yata yasata juyowa cikin sauri Kallon ta tayi sannan tace

” Kausar lafiya bakiyi bacci ba har yanzu ? ”

Cikin damuwa Kausar tace

” Momy bazan iyayin bacci ba sabida tunda Dady yashigo naga yana cikin damuwa kuma gashi yafita a cikin yanayina tashin hankali ”

Jawota Momy tayi jikin ta lallashin ta tashiga yi Kausar yarinyace yar kimanin 10 years dukda kasan cewar ta yarinya tanada hankali dakuma tsantsar tausayi gatada raunin zuciya

Kafin Barrister ya isa jami’an tsoro sun rigashi isa tuni aka nufi asibiti da Affan cincike a kashigayi tun cikin daran har zuwa wayewar gari misalin 10 akayima Alhaji Isma’il sutura aka kai shi makwancin shi bayan likitoci sunyi nasu gwaje gwajan shigo Affan seda yayi kwanaki 3 batare daya San inda kanshi yakeba

A ranar kwana na 4 misalin 03:30 ahankali Affan ke bud’e idanun shi sauke su yayi kan mahaifiyar shi da Barrister cikin sauri Barrister yatafi kiran doctor babu jimawa sukadawo tare gwaje gwaje doctor yayi mishi sannan yace subiyo shi office tare suka bishi bayan ‘yan rubuce rubuce doctor yafuskance su sannan yace

” Affan yakamu da Ciwon Zuciya kuma mai ‘karfi sakamakon mummunar bugun zuciya dayasamu na lokaci d’aya zai iyasamun lafiya amma idan anbi dokoki zaku d’inga sashi cikin farinciki sannan karka dinga takura mishi da hayaniya a inda yake duk abinda kukasan zai tada hankalin shi to kar a kuskura ayishi zai zauna acikin asibiti nan har na tsawon wani lokaci muga yadda jikin nashi zaiyi ”

Cikin matu’kar damuwa barrister yace

” to amma doctor zai iya warkewa duka ko ? ”

Jinjina kai doctor yayi sannan yace

” warkewar shi tana tarene da irin farincikin dakuke sashi amma fa kusani wannan ciwon yanada mugun had’ari idan ba’a kiyaye ba to zaku iya rasashi lokaci d’aya ”

Kuka Hajiya Aysha tasaki sannan tatashi tafita komawa gurin Affan tayi zuba mishi idanu tayi tana wani sa’kesa’ke cikin zuciyar ta

Yau kimanin tsayin lokaci da kashe Alhaji Isma’il dan har Hajiya Aysha tafita daga takaba ayanzu Affan yazama mugun miskili bayayi makowa magana kullum yana cikin bedroom d’in Abban shi misalin 2 pm Barrister yashigo cikin babban parlour adede lokacin Affan yana zaune kan cushion idanun shi akan TV amma hankalin shi baya kan TV cikin tausayawa Barrister ya’isa gareshi hannun shi yakama cikin sanyin murya yace

” haba My son kasan banason wannan tunanin da kakeji fa ? to yanzu de nazo makada wani albishir mai dad’in gaske ”

Wasu ta’karsu yami’ka mishi sannan yace

” sakamakon jarabawar ku tafito kuma komi yayi kyau nasan burin ka shine katafi Saudiyya karatu to nagamayima komi akan haka zaku tafi a ‘karshen watannan kaida d’an uwan ka Ashiraf ina Hajiya ne ? ”

Ha’ki’ka Affan yaji dad’in haka amma yaso ace mahaifin shi shine zaiyi mai komi segashi azzalumai sun kashe mishi shi cikin yanayin rashin son magana Affan yace

” nagode dady Momy kuma tafita dama inason ganin ka Dady ina zuwa ”

Tashi Affan yayi yanufi bedroom d’in Abban shi cikin wannan gurin yashiga system da box d’in da Abban shi yabashi ya d’akko yana zuwa yami’ka ma Barrister yace

” Dady wannan box d’in akwai suwa dagacikin takardun kadarorin Abba wannan system d’in kuma zantafi da’ita skul sabida Abba yabani ita kafin akashe min shi banaso kabama kowa dukiyar Abba koda kuwa Momy nace idan tamatsa karaba kabata hak’kin ta nima nayar da dakai kamar yadda Abba yayar da dakai ”

Affan na kaiwa nan yatashi yanufi bedroom d’in Abban shi wanda yamaida nashi ayanzu binshi da Kallo Barrister yayi sannan yace

” janko ri’ke amana Affan ko nera d’aya bazata salwanta ba cikin dukiyar ka my son koda zan mutu wajan kare dukiyar ka to nayi al’kawarin kareta ”

Tashi barrister yayi yafita motar shi nafita tasu Hajiya da ba’kinta suka shigo kallon motocin barrister yayi cikin mamaki da razana yace

” Alhaji Sambo kuma ? anan gidan to mai yazoyi ? ”

cikin sauri Barrister yajuya akalar motar yakoma gidan a babban parlour Hajiya tayima su Alhaji Sambo masauki sawa tayi aka kawo musu abin sha dana motsa baki cikin wata irin murya Alhaji Sambo yace

” shikenan Hajiya yaude komi yazama dede kinzama matata babu sauran damuwa yanzu kikira Barrister kisashi yatattaro muku duk wata dukiya taku dake hannun shi shikuma yaron ki kibud’e mishi ido yayi miki bayanin inda sauran dukiyar Alhaji Isma’il take dan yafikowa sanin inda take kinga semu had’a datawa dukiyar mu bun’kasa kasuwanci a tsakanin mu musiyi hannun jari a Company Company dake ‘kasashen ‘ketare ”

Jin jina kai Hajiya Aysha tayi Alamar gamsuwa shiko barrister daya tsaya jikin ‘kofa yagamajin komi cikin sauri yakoma baya yana salati afili yafurta

” amma Hajiya Aysha kinyi kuskure maiya kaiki auran mugu azzalumi Alhaji Sambo lalle kam babu yadda za’ayi nabaku dukiyar Affan wannan amanace ”

Cikin mamaki Affan ya idasa fitowa sabida shima yaji komi Kallon shi Alhaji Sambo yayi cikin zuciyar shi yace sena tarwatsa rayuwar ku amma kafin nan sena gama kwashe dukiyar ku duka ”

Cikin mamaki Affan yake Kallon Momy shi murmushi tayi tace

” Affan kwantar da hankalin ka wannan da kake gani shine saban mahaifin ka shize cigaba da kula damu kazo kayimai bayanin duk wata dukiyar mahaifin ka dakasani shima Barrister zansa yakawo tawajan shi semu bashi ya adana mana tunda kaga kai yanzu yarone bakasan yadda zakatafiyar da dukiyar kaba ”

Cikin mugun ba’kin ciki Affan yace

” Momy gaskiya abinda kikayi bai daceba kwata kwata wata nawa da rasuwar mahaifina amma wai har kinyi aure to Wllh bazan ta’ba d’aukar shi amatsayin ubana ba har abada kuma bazan bashi dukiya taba mahaifina ba’a banza yatarataba seda yasha wahala sannan ace darana tsaka nabamawani ita bazai yiyi ba dan Allah Momy idan har kinason farincikina to ki warware wannan auran nacuta ”

Afusace tami’ke tawanke shi damari tace

” baka isaba yaro kuma dole kayima Dadyn ka bayanin inda dukiyar take kuma katattaro ta yanzu kaji nagayamaka ”

Cikin ba’kin ciki Affan ya kalli Alhaji Sambo da Momyn shi ta danganta da Dadyn cikin zafin zuciya Affan yace

” Wllh Momy bazanyi miki biyayya ba akan wannan lamarin idan har bazaki warware wannan auran ba to bazaku zauna a gidan mahaifina ba idan kuma kukace dole anan zaku zauna to Momy sede ni nabar muku gidan nasan banida hurumin hanaki aure amma aysekibi abin a tsari wannan fa abokin Abba ne kuma kinsan basa shiri sabida muguntar Alhaji Sambo ”

Cikin tsawa Hajiya Aysha ta dakatar dashi sannan tace

” lalle Affan kazama fitsarare ni mahaifiyar ka kake gayama irin wannan maganganun to bari kaji naza’bi Alhaji Sambo akan ka sede kabar gidan ”

Cikin razana Affan yayi saurin isa gareta hannuwan ta yakamacikin kuka yace

” haba Momy taya zakirabu da d’anki akan wani Momy nifa bazaki iya canzaniba amma shifa zai iya canzaki Momy kituna ni kad’e gareki idan kika rasani bakida tabbacin zaki samu wani haba Momy karkisa wannan mugun ciwon nawa yatashi akan wani bare agurin mu dan Allah Momy ”

Fizge hannuwan ta tayi sannan tace

” Alhaji Sambo ba bare bane yanzu acikin mu ubane agareka idan har bazaka yarda da abinda nace makaba to sede kabar gidan nan kuma nasan zansamu wasu ‘ya’yan dama mahaifin ka keda ‘kwai d’aya a duniya amma baniba ciwon ka kuma idan yatashi kai kaja sabida kai ka’ki amsar umarnina ”

Cikin kuka mai sauti da tsuma zuciya Affan yadafe setin zuciyar shi yace

” Momy tabbas zantafi kuma zan manta dake kamar yadda kika za’bi ma’kiyin mahaifina akai na tun da Abbana yarasu nazama mai RUFAFFIYAR ZUCIYA agurin kowa amma ban dake toyau gashi kinsa Zuciyar tawa tarufe duka babu wanda zankuma bud’ema Zuciya ta har abada Momy kinsa natsani duk wata ‘ya mace a duniya Wllh daga yau natsani mace koda jaririya ce duk macan data sake takusanto inda nike to Wllh sena yagamata mutunci Momy dagayau namanta dake har abada kema kimanta dani ”

Fita yayi afusace yana dafe da Zuciyar shi sabida wani irin bugu da Zuciyar keyimai da matsanan cin ciwo cikin sauri Barrister yakamashi suka fita cikin harabar gidan jin Affan zai fad’i yasa Barrister saurin d’aukar shi ay kafin yakai shi cikin mota numfashin shi yatsaya cikin tashin hankalin yasashi amota yanufi hospital

Download Rufaffiyar Zuciya Hausa Novel Complete

Download Babban Yaro Hausa Novel Book 1 To 3

Leave a Comment