Entertainment

Yadda Ake Wankan Janaba, Haila, Biki da Juma’a

Wannan wanka da malam yayi bayani ya kunshi yadda ake wankan janaba, haila, biki, juma’a da sauransu, banbancin shine kawai niyya.

Yadda Ake Wankan Janaba

Yadda Ake Wankan Haila

Yadda Ake Wankan Biki

Yadda Ake Wankan Juma’a

Wannan bayani ya fito ne daga bakin marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam [Rahimahullah], inda yake cewa. Wankan Janaba yana da siffa guda biyu: Akwai “Siffatul Ijza (Suffar Wadata)” da kuma wacce ake kira “Siffatul Kamal (Suffar Kamala)”.

Wannan wanka da malam yayi bayani ya kunshi yadda ake wankan janaba, haila, biki, juma’a da sauransu, banbancin shine kawai niyya.

Yadda Ake Wankan Janaba A Siffar Sa Ta Kamata

Idan ka zo za ka yi wanka ga ruwa a gabanka. Farkon abin da zaka fara yi shi ne: Za ka karkato bakin mazubin ruwanka, ka wanke hannunka sau uku, sannan sai ka tsoma hannu a cikin ruwan sai ka debo ka wanke gabanka, a dai-dai lokacin da za ka wanke gabanka a lokacin za ka kulla niyya ta wankan Janaba (Ko waninsa wato wankan biki, haila, juma’a da sauransu) wanda yake wajibi ne, idan ka wanke gabanka ma’ana ka yi tsarki kenan, to daga nan kuma sai ka yi alwala irin yanda kake alwala ta sallah, abin da duk kake a alwala ta sallah za kayi sai abu daya shi ne wanke kafafu to wannan za ka kyale shi ba za kayi shi ba, to daga nan sai ka tsoma hannuwanka guda biyu a cikin ruwan ba tare da ka debo ruwa ba sai ka murmurza kanka saboda kowane gashi da ya bude a lokacin da maniyyi yake kokarin fita daga jikinka ya koma yanda yake, don gashin dan Adam yakan bude musammam gashin sa na kai, idan ka zuba ruwa a haka yana iya haifar maka da ciwon kai ko wani abu daban, bayan haka sai ka debi ruwa a cikin tafin hannunka daya sai ka zuba a kanka ka tabbatar ya game ko ina a kanka, ka sake kanfata na biyu ka tabbatar ya game ko ina a kanka, haka na uku ka tabbatar ya game ko ina a kanka.

To idan ka yi wannan sai ka debi ruwa ka game dukkanin jikinka da shi kana mai farawa da bangaren jikin ka na dama kafin na hagu, sannan na hagu ka tabbatar ruwa ya taba ko ina. To idan ka yi wannan ne ka kammala, abu na karshe shi ne sai ka wanke kafarka ta dama sannan kafarka ta hagu shi ne cikon alwalar da ka riga ka faro.

Yadda Ake Wankan Janaba A Siffar Ijza

Idan mutum zai yi wanka siffa ta Al Ijza wadda ta wadatar ba sai ka yi alawa a cikin ta ba, kana zuwa ka yi niyyar yin wanka din kawai sai ka dauki ruwan ka watsa a jikin ka ya game ko’ina, in ma wani kududdufi ne ko rami ko swimming pool sai ka yi tsalle ka fada a ciki, dama ka kulla niyyar ka kafin ka shiga, daga ka fito abin da za ka yi shi ne abubuwa guda biyu, kurkurar baki da kuma shaka ruwa a hanci da fyacewa. Shi kenan, kuma ya halatta ka yi sallah da wannan wankan. Hadisi cikin Sahihul Muslim ya nuna haka. Sai dai wanda ya yi wanka na farko ya fi ka cikar kamala da kuma lada saboda ya bi dukkan sharuddan.

Maganin Kurajen Fuska Ga Mata Da Maza

Leave a Comment