Amfanin Agwaluma Ga Mata Guda 5:
- Agwaluma na maganin zazzabin Malaria mai naci ko wanda bai jin magani. Binciken wanda aka wallafa a kundin BMC Complementary and Alternative Medicine ya bayyana cewa wannan magani ka iya zama sabuwar karbabbiyar hanyar magance zazzabin duba da rashin nasarar da ake samu da sauran nau’ikan magunguna.
- Agwaluma dai na dauke da sinadarin Vitamin C, wanda ke da matukar amfani a jikin dan adam.
- Agwaluma na da matukar amfani ga mai dauke da juna biyu. Shan agwaluma na tsayar da amai da jiri wanda juna biyu ke haifarwa.
- Sannan idan mutum baya so yayi kiba day a wuce misali sannan yana bukatar sinadarin gyaran idanu da zuciya toh agwaluma na taimakawa sosai wajen cimma hakan.
- Yana kuma taimakawa wajen samun bacci cikin kwanciyar hankali. Sannan kuma yana rage ciwon gabbobin jiki.
Amfanin Agwaluma 5 A Jikin Dan Adam
Maganin Karin Kiba Da Gudu Cikin Sauki