Health Care

Amfanin Darbejiya A Jikin Dan Adam

Amfanin Darbejiya A Jikin Dan Adam

Amfanin Darbejiya Ga Dan Adam

Amfanin Darbejiya: Darbejiya ko dogon yaro wata bishiya ce a kasashen hausa da sauran kasashen duniya. Tana da manyan rassa da kuma ganye launin kore (green leaves). Kusan komai na darbejiya daci keg are shi kama daga saiwarta(root) sssakenta (extract) ganyenta (leaves), sai dai kuma diyanta idan suka kosa to suna canja launinsu zuwa yellow masu dan zaki haka.Ana amfani da ganyen darbejiya da sassaken ta da hurenta dakuma diyantaduka a matsayin magani. Sai dai ba’a cika amfani da saiwarta a matsayin maganin sha ba saboda hatsarin dake tattare da shi. Darbejiya na dauke da wasu sinadarai masu matukar muhimmanci da karfin gaske wadanda samuwarsu ya maida darbejiya magani a gida. Ga kadan daga cikin su; Sodium ,Potassium ,Salt ,Chloriphyle, Calcium, Phosphorus, Iron, Thiamine, Nicocine, Vitamin C, Carotene, ODatic acid, Gliserida acid, Asetilolfuranile, Dakahidro Tentramatil, Okanone, Fenantone, Acetate acid da sauransu.

Maganin Ciwon Ciki

A tafasa ganyenta kwara bakwai (7) a cikin glass biyu na ruwa sai a tafasa ruwan ya koma kamar misalin glass daya sai a tace da kyau a ajiye ya huce sannan a sha. A nemi waje mai nutsuwa a kwanta dan yana sa ganin juwa ko aji kamar za’ayi amai.

Maganin Gudawa/Zawo

Idan an ci wani abinci ko abin sha da ya gurbata ciki to sai a tafasa ganyen darbejiya tsiyaye ruwa na farko a sake zuba wani ruwan a tafasa sai a na biyun za’a tarfa zuma kadan sai a sha.

Maganin Ciwon Suga

amu diyan darbejiya misalign rabin gwangwanin madara sai a saka ganyen mangoro fresh kwara uku a tafasa da kyau a misalign kofi daya na ruwa sai a sha da safe bayan an karya.

Maganin Malaria

Za’a iya shan ruwan ganyen darbejiya dai dai kada a sha dayawa a dinga shan kadan kadan saboda kada ayi amai dan ana so ya tsaya a jikin ka dan ya maka aiki. Daga bisani ana iya tafasa ganyen sai ayi wanka dashi ko ayi surace da shi.

Maganin Wankin Ciki

Lokuta da dama jinni kan gurbata saboda wasu kwayoyin cuta haka za’a iya iya tsabtace jinni ta hanyar amfani da ganyn darbejiya inda za’a tafasa ganyen kwara bakwai 7 kacal sai a sha wannan zai baiwa jinni damar gudana a yadda ya dace.

Maganin Ciwon Hanta

Dukbda cewa ita hanta bata son abu mai daci kuma yawan amfani da kayan daci na illatata amma indai za’a kiyaye da yanda ake sha to wannan magani ne.Anan diyan darbejiyane ake amfani da shi inda za’a tafasa rabin gwangwanin tumatir karami a tace da kyau a tarfa gangariyar zuma sai a sha da safe.

Maganin Ciwon Gabobin Jiki

Kasancewar darbejiya na dauke da sinadarin magani kamar Azachdirichtin, ODituranoe, Aceatyl acid, Gliserda oil wannan yakesa yake warkar da ciwon gabobin jiki.

Maganin Kazuwa, Makero, Kurajen Fata da Dandruff

Sai a nemi man darbejiya wato neem oil ayi amfani dashi a inda ake bukata. Amma fa a kula ba’ayi man darbejiya domin a sha ban a shafawa ne kawai wanda shansa wani lahanine na musamman.

Maganin Basir Mai Tsiro

A duk san da basir ya daura maka aure yana ta wahalar da kai inda yake haifar maka da fitan baya ko tsananin zafi ko tsagewar dubura ko wahala a yayin yin bayan gari da zubar jinni da jin kaikayi a dubura to ka nemi sassaken darbejiya dana gasgery ka wanke mai kyau ka tafasa ka sha kuma zaka iya zama a cikin ruwan inda zaka tsoma duburarka a ciki na tsawon mintina goma ko fiye da haka a kullum sau biyu safe da yamma har basir din ya zuke. Haka kuma zaka daka garinsu ka gauraya da Vaseline idan ka wanke gurin mai kyau sai kana shafawa.

Maganin Tsarin Iyali

Darbejiya na baiwa ma’aurta damar yin tazarar haihuwa ba tare da ansha kwaya ko anyi allura ba wacce zata janyo wata matsala ta daban. Dan haka namiji ko mace mai fuskantar karancin haihuwa ba zaiyi amfani da darbejiya ba. Idan ana bukatar tazarar haihuwa a gargajiyanche to ana amfani da man darbejiya insha Allah zaa samu biyan bukata.

Maganin Kurajen Gaban Mace da Namiji

Leave a Comment