Amfanin Zogale 18 A Jikin Mutum
Amfanin Zogale na da yawa a Jikin mutun Mata da Maza duk zogale na masu amfani.
- A dafa ganyen zogale da zuma asha kamar shayi yana maganin olsa(ulcer)
- Mai fama da kuraje ajika ya hada garin zogale da man zaitun ya shafa.
- Wanda ya yanke koya sare ko wani karfe yaji masa ciwo ya Shafa danyan ganyen zogale insha Allah jinin zaibtsaya.
- Ana sanya garin zogale akan ciwo ko gyambo Dan saurin warkewa.
- Ana shafa ganyen zogale agoshi yana maganin ciwon kai.
- Sanya garin zogale acikin abinci yana maganin hawan jini.
- Ana dafa ganyen zogale tare da kanwa yar kadan domin maganin shawara.
- Gamai fama da ciwon ido zai diga ruwan zogale haka mai fama da ciwe kunne.
- Macen dake shayarwa ta dafa furen zogale da zuma don Karin ruwan nono.
- Wanda ke fama da yawan fitsari wato cutar DIABETES ya dinga shan furen zogale da citta kamar shayi.
- Idan aka tafasa furen zogale da albasa kamar shayi ko a dafa zogale da tafarnuwa da citta da kanumfari da tsamiya anasha shafe fa maraice yana maganin sanyi.
- Cin danyan zogale yana maganin tsutsar ciki.
- Ana daka ganysn zogale da Yayan baure asha da nono ko kunu yana maganin ciwon hanta.
- Mai fama da sanyin kashi ko wani kumburi zai soya Yayan xogale adakasu sannan a hada da man kwakwa(man ja) sai ashafa.
- Adaka zangarniyar zogale da Yayan dake ciki da kanumfari da citta da masoro da kimba domin Karin karfin da namiji.16-Adaka saiwar zogale da Yayan kankana asha da nono yana maganin tsakuwar ciki.
- Mai fama da typhoid da malaria da basir ko shawara sai ha yawaita shan ruwan dafaffen zogale.
- Mai fama da ciwon Aids zogale na rage radadinsa ta hanyar shan ruwan dafaffen zogale.
Amfanin Zogale 18 A Jikin Mutum
Amfanin Zogale 18 A Jikin Mutum
Alamomi da Maganin Ciwon Sanyi Na Maza da Mata