Magungunan Gargajiya Guda 15
Amfanin Jan Tumatur
Maganin Gyambon Ciki
Wasu daga cikin Likitocin Musulunci bincikensu ya tabbatar da cewa Mai fama da matsalar gyambon ciki, idan yana shan jan Tumatur guda uku kullum da safe kafin yaci komai, zai samu chanji sosai. Kuma zata dena yi masa mummunan tashin nan da takeyi.
Maganin Sikila
Hakanan shan Jan Tumatur guda uku kullum da safe zai amfani sosai ga mutumin dake fama da ciwon Sikila (sickle cell anemia) da kuma masu fama da ciwon Zuciya in sha Allahu. Domin tumatur yana bude hanyoyin jini, yana samar da manyan sinadarai irin wadanda jiki ke bukata.
Idan za’a sha anemi wanda ya nuna, kuma banda rubabbe.
Amfanin Kabewa
Maganin Bushewar Ni’ima, Yawan Maniyi
Asamu kabewa ayankata adafa. Sannan adauki ruwanta kofi guda ahada da Madara ko Nono, a zuba Sugar sannan asha da dumi-duminsa (kwana 7). Wannan in sha Allahu zai magance matsalar Olsa ko kumburin ciki. Kuma zai magance matsalar mutuwar Mazakuta ga Mazaje. Da kuma matsalar bushewar ni’ima ga mata. Namijin da ba ya haihuwa ta sanadiyyar Qarancin ‘ya’yan Maniyyi (Low Sperm count) shima idan yana shan wannan za’a dace. Amma shi zai sha da nonon Rakumi ne, amma wanda bai fara lalacewa ba.
Amfanin Furen Albabunaj
Maganin Basur, Kumburin Ciki da Olcer
Asamu furen Albabunaj na ainahi (mai kyau din) anikashi, a samu kamar cikaken cokali 7 na garinsa. A hada da garin Habbatus sauda cokali 7, sannan arika diban cokali guda da rabi ana dafawa da ruwa kofi guda. Idan ya dafu sai a tache sannan asha haka, ko kuma da zuma. In sha Allahu wannan zai magance matsalar Basur, Kumburin ciki, da Olsa.
Maganin Ciwon Koda
Masu fama da ciwon koda ta kumbura in sha Allahu zata sace. (za’a sha har sati 6).
Maganin Rashin Barci
Masu fama da matsalar rashin barci, idan suna sha zasu samu barci sosai. Hakanan mai fama da natsalar rikicewar kwakwalwa idan yasha zai samu sauki.
Maganin Rikicewar Jinin Haila
Matar da take fama da matsalar rikicin jinin Haila ko toshewar Mahaifa idan tana sha zata warke in sha Allahu.
Amfanin Bawon Ayaba
Maganin Karfin Mazakuta
Asamu bawon ayaba ko Plantain a shanya a inuwa sannan a dakashi bayan ya bushe. Asamu kamar garinsa cikin cokali 7. Arika zuba cokali guda na wannan garin acikin Madara rabin Gwangwani a sanya zuma mai kyau sannan asha. Za’a maimaita har tsawon kwanaki 10 ko 14. Ana sha kullum safe da yamma. In sha Allahu za’a warke daga Olsa, za’a samu Qarfin Kuzari na Namiji, Mace ma zata samu ni’ima ajikinta. Sannan za’a samu wataka daga Qugi ko rikicin ciki. In sha Allah.
Amfanin Bawon Ruman
Maganin Dattin Ciki, Gyambon Ciki
Asamu bawon rumman adakashi agauraya da zuma tare da garin Kwallon Kankana (daidai rabin wancan). Za’a sha har tsawon Wata guda. In sha Allahu za’a samu waraka daga chutar gyambon ciki, Daukewar sha’awa, Dattin ciki, Majinar Ciki, da sauransu.
Amfanin Man Habbatussauda
Maganin Ciwon Hanta
Cokali guda na Man Habbatus sauda, Cokali uku na Zuma, Cokali guda na garin ‘bawon rumman, ahadasu waje guda asha. Bayan an sha sai kuma asha kofi guda na Nono (tsala ko Kindirmo) ko kuma Madara Gwangwani guda. In sha Allahu za’a samu lafiya daga chutar Olsa, Basur, da kuma ciwon Hanta.
Amfanin Garin Tafarnuwa
Maganin Sanyin Kirji
Garin tafarnuwa cokaki goma, Garin Habbatus sauda cokali goma. A hadasu da zuma arika shan cokali guda da safe kafin karyawa. Sannan cokali guda duk bayan awa uku Har zuwa dare. In sha Allahu za’a samu waraka daga ciwon Olsa, sanyin Qirji (Pneumonia) da kuma chushewar ciki.
Amfanin Furen Banafsaj
Maganin Ciwon Daji
Idan ana dafawa ana shansa yana magance ciwon daji, Olsa, da sauransu.
Amfanin Dankali
Maganin Ciwon Daji, Olsa
Asamu dankali ‘dan hausa (Sweet Potatoes) anikashi a blender sannan adebi kofi biyu na ruwansa asha. Sannan bayan awa daya da rabi asha ruwan Shammar. In sha Allahu Za’a samu waraka daga chutar Olsa, daji, da sauransu.
Koda ana amfani da wani daga cikin wadannan laqanin, to wajibi ne a kiyaye daga abubuwan dake kawowa motsawar jinya ga masu fama da Olsa ko Kumbutin ciki ko Basur. Misali kamar :
- Dole ne a dena ci ko shan abubuwa masu tsami, Ko masu Kaushi, ko masu tsananin sanyi ko zafi.
- Dole ne adena dadewa cikin yunwa.
- Adena kwanciya da zarar an ci abinnci har sai bayan an motsa jiki, ko kuma ajira kamar Minti 30.
Yadda Ake Gane Mace Yar Madigo (Lesbian)