Health Care

Minene Amfanin Gemun Masara

Minene Amfanin Gemun Masara

Minene Amfanin Gemun Masara

  1. Ciwon suga(diabetes)
  2. Matsalar fitsari(urinary infection)
  3. Fitar da dutsen qoda(kidney stone)
  4. Ciwon hawan jini(hypertension)
  5. Ciwon sanyi mai riqe gabobi(arthritis)

Yadda Ake Maganin Ciwon Suga Da Gemun Masara

Amfanin Gemun Masara: Za’a sami gemun masara cikin Kofi sai asami ganyen yadiya cikin Kofi sai ganyen mangwaro cikin Kofi sai akirbasu,bayan ankirbasu sai azuba atukunya adafa idan ya dafu sai a sauke, asha Kofi daya da safe daya da yamma kuma duk lokacin daza asha sai an dimamashi, ayi haka har zuwa sati uku sai aje ayi gwaji agani, kuma yana da kyau akiyaye abinci da zaariqaci kamar yadda likitoci suka qayyade.

Yadda Ake Maganin Matsalar Fitsari Da Gemun Masara

Zaa samu gemun masara cikin kofi sai asami lemun garas shima haka sai adafa ‘ ariqasha kaman shayi.

Yadda Ake Maganin Dutsen Koda Da Gemun Masara

Asami gemun masara cikin Kofi sai yayan zogala rabin Kofi sai ganyen zogala shima rabin Kofi sai akirabasu ko ayi blending azuba ruwa kofi daya da rabi aciki sai atace ashanye ayi haka sati uku.

Yadda Ake Maganin Hawan Jini Da Gemun Masara

Asami gemun masara Kofi uku sai jan zobo kofi daya sai yayan zogala rabin Kofi adafasu atace azuba awani abu ariqasha safe da yamma Har sati daya ” bayan angama ana iya sakewa.

Yadda Ake Maganin Ciwon Gabobi Da Gemun Masara

Asami gemun masara kofi uku da tafarnuwa rabin Kofi da kanunfari cokali Bihar abusar dasu ayi garinsu ariqasha acikin madaran shanu ,bana gwan-gwani ba.

Minene Maganin Nankarwa

Leave a Comment