Tarihin Aminu Daurawa
Tarihin Iyayen Malan Aminu Ibrahim Daurawa
Mahaifina Shahararren malami ne, wanda ake kira Sheikh Ibrahim Muhammad mai tafsiri, gidan Zakara-Mai-Neman-Suna Fagge. Yana gabatar da tafisiri duk ranar Litinin da Alhamis, a unguwar Fagge, kusa da tsohuwar tashar kuka. Tsawon shekaru arba’in, kuma yana karantar da ilimi a zauren gidansa, bayan kasuwanci da sana’ar dinki, domin dogaro da kai.
Sunan mahaifiyata Hajiya Sa’adatu Al-Mustapha, daga unguwar Bachirawa, karamar hukumar Ungogo.
Tarihin Aminu Daurawa
An haife ni a ranar 1 ga wata Janairu shekara ta 1969, a cikin garin Kano, a gida mai lamba 32 unguwar kofar Mazugal, a karamar hukumar Dala.
Na fara karatun Al-Kur’ani mai girma tun ina dan karami, kuma na haddace shi a lokacin ina da shekara 14 zuwa 15. Bayan firamare da sakandare, da na yi, na kuma ci gaba da neman ilimi, domin fadada karatun addini, a wajen wadansu manyan mashahuran malamai na Kano: Wasu na Alqur’ani da tafsir, wasu na Alqur’ani zalla, wasu na ilimi da fannoninsa daban-daban.
Jerin Malaman da Malan Aminu Daurawa Yayi Karatu Wurinsu
- Alaramma Umaru Adakawa (Malam Tsoho) wanda na yi karatun Alqur’ani a wajensa.
- Alaramma Salisu Bahadeje, layin tagwayen gida, wanda na yi karatun Alqur’ani a wajensa.
- Alaramma Malam Na-Ande, makarantar Arzai, wanda na yi karatun Alqur’ani a wajensa.
- Alhafiz Malam Abdullah Quru gwammaja.
- Alaramma Malam Laminu Arzai, wanda na yi gyaran tilawa a wajensa.
- Sheikh Auwal Isa ‘Yan Tandu, wanda na yi lugga da fiqihu da hadith a wajensa.
- Sheikh Al-Mustapha Bazazzage layin tagwayen gida, wanda na yi lugga da fiqihu da tafsir a wajensa.
- Sheikh Idi Kajjin ‘Yan Awaki, wanda na yi hadith da lugga a wajensa.
- Sheikh Zakari Mai littafi, wanda na yi lugga da fiqihu a wajensa.
- Sheikh Dogo Mai Mukhtasar Sabon Titi, wanda na yi nahawu da fiqihu a wajensa.
- Sheikh Usman Gwammaja, layin azara, wanda na yi hadith da lugga da fiqihu da tarikh a wajensa. Wannan malami, na yi tsawon shekara ashirin ina karatun ilimi a wajensa. Allah ya ji qansa da rahama!
- Sheikh Abubakar Basakkwace Qoqi, wanda na yi fiqihu da lugga a wajensa. Wannan malami, a wajensa na sauke Alfiyya din Malik, da Muqamatul Hariri, da Shu’ara’ul Jahiliyya. Malami ne mai haquri da juriyar karantarwa.
- Dr. Kabiru M. K. Yunus BUK, wanda na yi nahwu da lugga a wajensa.
- Dr. Aminuddeen Abubakar, shugaban Da’awah, wanda na yi tauhidi da hadith a wajensa.
- Dr. Ahmad Bamba BUK, wanda na yi hadith a wajensa. Wannan malami uba ne, kuma mai ba da shawara.
- Dr. Abubakar Jibirin, wanda na yi Kitabut Tauhid a wajensa.
- Sheikh Abdulwahab Abdallah, wanda na yi Musdalahul Hadith, da Qadarunnadah (nahawu), da Subulussalam (hadith) a wajensa. Wannan malami uba ne, kuma mai ba da shawara.
Littattafan Da Malam Aminu Daurawa Ya Karanta ?
Akwai wasu malaman da suka yi mini tasiri a rayuwa, amma ta hanyar karanta littattafansu da sauraren kaset-kaset dinsu:
- Sheikh Muhammad bin Saleh Usaimin. Wannan malami ne, na kwashe tsawon shekara goma ina bin littattafansa da kaset-kaset dinsa na audio da bidiyo. Na tasirantu da shi kwarai da gaske.
- Almuhaddith Sheikh Muhammad Nasiruddeen Albani. Wannan malami, duk littattafansa da suka fito kasuwa, da kaset-kaset, ina bibiyar su, saboda fa’idoji masu yawa.
- Sheikh Bakar Abu Zaid. Saboda kwarewarsa a wajen sarrafa littattafai. Sauran su ne, Sheikhul Islam Ibni Taimiyya, da Sheikh Ibnul Qayyim, da Sheikhul Islam Azzahabiyy, da Sheikhul Islam Ibni Kathir, da Sheikhul Islam Ibni Hajar Al-Asqalani.
Wacce Aƙida Malam Aminu Daurawa Yake ?
Aqidata ita ce aqidar ahlussunnah wal jama’a. Ma’ana, imani da Alqur’ani da hadisan Manzon Allah (SAW) a kan fahimtar magabata na kwarai.
Takaitaccen Tarihin Dr Ahmad BUK (Bamba)
Matakin Karatun Malam Aminu Dauarawa
Na ci gaba da karatu na zamani a Jami’ar Bayero, a bangaren jarida, Mass Comm. Wasu dalilai suka tsayar da ni. Na yi diploma a computer data processing.
Yawan Iyalin Malan Aminu Daurawa
A yanzu ina da mata biyu, da kuma ‘ya’ya tara.
Kasashen Da Malan Aminu Daurawa Yaje Wa’azi
Daga cikin kasashen da na je domin wa’azantarwa, akwai Nijar, Togo, Ghana, Cote d’Voire. A jihohin Najeriya kuwa, babu jihar da ban je ba domin gabatar da wa’azi ko karantarwa.