Tarihin bayajidda Kafin Zuwanshi Daura
Tarihin Bayajidda AKasar Hausa: To kamar dai yadda tarihin ya nuna cewar asalin sunan Bayajidda abu yazid dalilin ma da yasa a ka sa masa baya jidda shine da bay jin maganar hausa daga kalmar baya ji. Shidai bayajidda mutum ne jarumi wanda kusan kamar yadda tarihi ya nuna cewar ya taso ne daga kasar Bagdad wato kasar bagadaza a hausance inda yake ta tafiya har iso a garin Borno wato a karon farko.
A inda daga bisani kafin ya baro garin Borno Akwai dalilan da suka sa haka Sune a cen garin Borno sakin Borno na lokacin ko a ce Mai ya aura ma shi Bayajidda diyarsa a inda daga nan suna zaune ya samu rade radin cewar sarkin zai kashe shi.
Daga nan bayan sun samu labarin haka sai matarsa ta umarcesa da su gudu su bar garin inda daga nan suka kama hanyarsu har zuwa kasar hausa. Wani sashen na masu tari yana nuna cewa a tarihin bayajidda ya taso ne yana ta tafiya har sai da yazo a garin daura ya sauka a garin da daddare a cikin gidan wata mata tsohuwa.
Yadda Bayajidda Ya Kashe Macijiya
A yayin da ya sauka a lokacin yana jin tsananin kishirwa inda ya tambayi tsohuwar nan da ya iske ta bashi ruwa ko kuma ina rijiya take yaje ya debo ruwa don sha sai tace masa ai su basu dibar ruwa da daddare a sanadiyyar sarki wato shi wani katon maciji ne dake hana mutanen garin dibar ruwa daddare.
Daga nan fa ne sai bayajidda ya nufi wannan rijiya ba tare da razana ba inda yaje zai debo ruwa sai macijin nan ya yo kansa da niyyar hana sa to fa daga nan ne ya fiddo takobinsa ya sare kan sa. To a lokacin da ya sare macijin nan ya manta waren takalminsa a bakin rijiyar.
A lokacinda gari ya waye sai mutanen da ke cikin gari suka zo dibar ruwa a inda suka tadda macijin nan kansa a sare sai suka kama murana tunda yanzu ba wani abunda zai hana su dibar ruwa a wannan rijiyar kuma suka tarar da takalminsa ware da kuma kan wannan maciji.
Mutane suka taru a fadar sarauniya daurama wadda ke mulki a kasar daura suna ta murna inda suka shaida mata cewar an kashe wannan maciji amma ba’a san waye ba amma fa wanda ya kashe wannan maciji ya bar rabin takalminsa a gindin wannan rijiya.
Daga nan fa ne sarauniya ta saka babbar kyauta inda tace ta yi alkawarin zata auri wanda ya kashe wannan maciji kuma zata basa rabin gari amma azo da waren takalmi domin tantance wanda yayi abun. Ana cikin wannan yanayi dai kwatsam sai ga wannnan tsohuwa a inda tazo ta ce ta san wanda ya kashe wannan maciji. To daga nan ne ta kwashe labarin abinda ya faru sai sarauniya ta auri bayajidda kuma ta basa rabin gari.
Tarihin bayajidda AKasar Hausa
Tarihin Aminu Daurawa Kundin Tarihi da Tambayoyi 20