Biography

Takaitaccen Tarihin Dr Ahmad BUK (Bamba)

Takaitaccen Tarihin Dr Ahmad BUK (Bamba)

Takaitaccen Tarihin Dr Ahmad BUK

Dr. Ahmad BUK fitaccen malamin addinin musulunci ne, tsohon malami ne a Sashen Larabci a BUK. An haifi Ahmad BUK a Ghana.

Sheikh Ahmad Muhammad Ibrahim Bamba wanda aka fi sani da Dr. Ahmad BUK da Kala Haddasana. Ya kammala karatunsa a daya daga cikin manyan Makarantun Ghana. Ya yi karatu a Saudiyya.

Bayan nan ya dawo Najeriya ya karantar a Jami’ar Bayero da ke Kano inda yayi karatun dakta. Dr. Ahmad BUK. Dr. Ahmad BUK ya auri mata 3. Shi ya sa ya bar mata 3 da ‘ya’ya 30 ciki har da jikoki.

Dr Ya karantar da littafai masu dimbin yawa wadanda har ya saukesu tare da Dalibai. Haka zalaika Dr yanada tarin Dalibai masu dimbin yawa wadanda a halin yanzu suma sunada tarin Dalibai da suke karkashinsu.

Dr Ahmad BUK Muwadda

Daga cikin Manyan ayukkan da Dr yayima addini akwai fassara littafin Muwadda Malik zuwa yaren Hausa a ranar 1 ga watan Muharram 1443. Wanda Gerawa Oil ya dauki nauyin bugawa. Dr yakasance wani alheri wajen bayas da gudunmawa ga addini a Nijeriya da Kasashen waje. Dr yakasance mutun marar tsoro wajen yada Sunnah tun lokacin da kowa yakejin tsoron yadata.

Shekarun Dr Ahmad BUK

Dr. Ahmad yana da shekaru 82 a lokacin da yabar duniya a shekarar 2022. Dr. Ahmad BUK ya rasu ne a ranar 7 ga watan Janairun 2022 dai da 4_6_1443, a asibitin koyarwa na Aminu Kano bayan ya sha fama da jinya.

Allah Ta’ala yajikansa da rahma Ameen ya hayyu ya qayyum

Leave a Comment