Entertainment

Tarihin El Clasico Tsakanin Real Madrid da Barcelona

Tarihin El Clasico Tsakanin Real Madrid da Barcelona

Tarihin El Clasico

Wasan El-clasico, wasa ne da ake yi a tsakanin kungiyar kwallon kafa na FC Barcelona da kuma ta Real Madrid da ke Sifen. A duk lokacin da kungiyoyin biyu suka hadu shi ne ake yi wa wasan da lakabi El-Clasico a yaren Sifen ko kuma “Wasa mafi zafi” a Hausance. An kiyasta cewa fiye da mutum miliyan 500 ne suke kallon wannan wasa a sassan duniya a akwatunan talabijin.

Yaushe Aka Fara Wasan El Clasico

Tarihi El Clasico ya nuna an fara yin wannan wasa ne a ranar 17 ga watan Fabrairun 1929 watau kimanin shekaru 87 da suka gabata. An nuna kungiyoyin biyu sun hadu a gasar rukuni-rukuni na La-Liga na Sifen har sau 171 kawo yanzu.

Tarihin El Clasico Tsakanin Real Madrid da Barcelona

Tsakani Barcelona da Madrid Suwa Sukafi Cin El Clasico

Tarihin El Clasico Kawo yanzu Real Madrid ce take gaba a fagen yawan samun nasara bayan ta samu nasara a wasannin sau 71 yayin da FC Barcelona kuma ta samu nasara sau 68. Sannan sun yi kunnen doki sau 32. Haka kuma Real Madrid ta samu nasarar zura kwallaye 278 a raga yayin da FC Barcelona kuma ta zura kwallaye 272.

A Najeriya, da yawa daga cikin masu kallon yadda gasar ke gudana a akwatunan talbijin ba su fara sanin muhimmancin wannan wasa ba sai a shekarar 2004 don mafi yawa matasa ne wadanda ba su da wayau. Kulob din Real Madrid dai ana yi masa kallon kulob din da babu kamarsa a bangaren samun kudin shiga a duniya, don haka yake cefano zaratan ’yan kwallon da suka shahara ba tare da shakka ba, yayin da kulob din FC Barcelona kuma ake masa kallon kulob din da yake tafiyar da harkokinsa sannu a hankali.

Misali, ba kasafai kulob din Barcelona yake ware makudan kudi wajen cefano zaratan ’yan kwallo ba, sai ta kama. Kulob din ya gwammace ya horar da matasan ’yan kwallonsa har su girma da hakan ta sa suke samun shahara a fagen kwallo a duniya. Shararrun ’yan kwallon kulob din irin su Lionel Messi da Andre Iniesta da Sergio Buskuets da sauransu, duk a kulob din suka samu horo tun suna kanana.

Tarihin El Clasico

A bangaren Madrid kuma, zaratan ’yan kwallo irin su Cristiano Ronaldo da Karim Benzema da Gareth Bale da James Rodgriguez da sauransu, kulob din ya cefano ne ba renonsu ya yi ba.

Tarihin El Clasico

How To Apply NEXIT Loan Training Batch C

Leave a Comment