Tarihin Garzali Miko
Tarihin Garzali Miko: Garzali Miko na daya daga cikin shahararrun mawakan kamfanin shirya fina finai dake Kano wato Kannywood, yanada kwarewa sosai wajen rera wakokin masu shiga zukatan mutane.
An haifi Garzali a watan Satumba na Shakarar alib 1993 a garin Kano. Yayi Karatunsa na Primary a Gyadi Gyadi Special Primary School, Daga nan ya wuce Makarantar Secondary Ta Horizon a cikin Birnin Kano, inda yafita da sakamako mai kyau. Bayan kammala karatun sa na sakandare Jarumin ya fara karatun gaba da sakandare inda ya fita da takardar shaidar Digiri. Garzali ya fara ne tun daga ƙarmin mataki har zuwa babban, kamar yadda yace a hirarsa zamansa Jarumi mafarkinsa ne yazama gaske, kasancewar tun yana ƙarami yake sha’awar zama jarumi.
Garzali Miko Songs 2022
A YouTube kadai, babu wata wakar Hausa da aka kalla kamar ta Hasashe a shekarar 2017, domin zuwa yanzu akalla mutum dubu dari biyar (500,000) ne suka kale ta. Ko wakokin manyan jarumai ba su samu wannan tagomashi ba. Ya fuskanci kalubale da dama, amma hakan bai sa shi ya karaya, ko jin ba zai kai labari ba, ya yi imani da cewar duk abun da ka jajirce a kai to Allah zai taimake ka. A wata hira da aka yi da shi, Garzali ya ce sha’awa ce ta ja shi ga harka finafinai inda ya fara tun daga tushe har kawo matsayin da ya tsinci kansa na jarumi a Kannywood. Yana mai cewa, “kalubale a harkar rayuwa duk abinda dan’dam keyi wani lokaci a samu farin ciki wani lokaci kuwa a sami akasin haka.
Fina Finan Garzali Miko
- Hadari
- Ameerah
- Zee Zee
- Guguwar So
- Makaryaci
- Wata Dukiya
- Dan Masani
- Idan Ana Dara
- Rai Da Rai
- Bakin Kishi
Tarihin Nafisa Abdullahi, Shekaru, Hotuna da Phone Number