Takaitaccen Tarihin Hamisu Breaker Dorayi
Tarihin Hamisu Breaker: Mawakin hausa ne wanda sunan sa ya yadu a Nigerian musammam ma yankin Arewa. Asalin sunan sa shine Hamisu Sa’id Yusuf amma mutane sun fi saninsa da Hamisu Breaker kuma sunan na Breaker ya samo asaline a lokacin da yana yin wani salon rawa da ake kira breaking tun a baya kafin asan shi a matsayin mawaki.
Shekarun Hamisu Breaker
An haifi Breaker a 1992 a Dorayi dake karamar hukumar Gwale a Kano. Kuma yayi makarantar firamare da sakandare a Dorayi amma har zuwa yau mawakin bai samu damar cigaba da karatu ba.
Hamisu Breaker ya fara Waka ne tun lokacin yana makarantar secondary kuma ya yi wakoki da dama kafin ya fara fitar da album Kuma wakar sa da ta yadu sama da ko wacce ita ce Jaruma. A wannan shekara ta 2020, Jaruma ita ce wakar hausa da aka fi kallo domin saida takai wani mataki a YouTube da babu wata waka da ta taba kaiwa a kankanin lokaci a tarihin wakokin hausa.
Tarihin Aisha Najamu Izzar So Shekaru, Hotuna da Phone Number