Tarihin Maryam Yahaya, Shekaru, Hotuna da Lambar Waya
Tarihin Maryam Yahaya: An haifi Jaruma Maryam Yahya ne a shekarar alif dubu daya da dari tara da casa’in da bakwai 1997, a unguwar Goron Dutse dake birnin Kano a Arewacin Nijeriya, inda yanzu haka tare da shekaru 21 a duniya.
Tayi karatun ta na primary school ne a wata makarantar primary dake “Yelwa Rimin Gado” a cikin garin Kano, sannan tayi karatun ta na secondary school a Bokab Barracks.
Jaruma Maryam Yahya daya ce daga cikin fitattun jaruman fina finan Hausa na Kannywood masu tasowa a yanzu.
Tauraruwar Jarumar ta fara haskawa ne, tuna daga lokacin da ta maye gurbin wata fitacciyar Jaruma, a wani kayataccen shirin fim mai suna “Mansoor” wanda kamfanin Jarumi Ali Nuhu “FKD Production” ya shirya, tare da fitaccen mawaki Umar M Sharif, a matsayin sababbin Jarumai, wanda hakan ne yayi sanadiyyar jan hankalin dumbin ma’abota kallon fina finan Hausa zuwa ga kallon shirin a shekarar 2017. Sannan Jarumar ta lashe kyautar sabuwar Jaruma mai tasowa a gasar “City People Entertainment Awards” na 2017.
Fina-finan Maryam Yahaya
Kadan daga cikin fina finan da Jarumar tayi sune, Mansoor, Arashi, Tabo, Gidan Abinci, da sauransu.
Maryam Yahaya Instagram, Twitter
- Instagram: @Maryam_Yahya
- Twitter: @Maryamyahya
Hotunan Maryam Yahaya
Maryam Yahaya Biography, Age, Photos, Phone Number & Net Worth
Sabbin Hotunan Maryam Yahaya 2022