Takaitaccen Tarihin Momee Gombe
Maimuna Abubakar da akafi sani da (Momee Gombe), na daya daga cikin Jaruman masana’antar shirya finafinan Hausa dake Kano, wanda tauraronta ya haska a shekarar 2020.
Shekarun Momee Gombe
An haifi jaruma Maimuna Abubakar da akafi sani da Momee Gombe a garin Gombe dake Najeriya, a ranar 28 ga watan June a shekarar alib 1997. Tayi makarantar Firamari da Sakandire a garin na Gombe. Jarumar ta taso da sha’awar zama daya daga cikin Jaruman na finafinan Hausa dake Kano tun tana karama, harma take ganin babu wani fita a shirin fim wanda zai bata wahala.
Yadda Momee Gombe Ta Shiga Kannywood
Jarumar ta shiga masana’antar shirya finfinan Hausa dake Kano ta hanun babban Frodusa Usman Ma’azu a shekarar 2017, Kuma an fara haskata a fim dinta na farko mai suna ANGO.
Video Wakokin Momee Gombe
Momee Gombe tayi wakoki da dama wanda sukakai 40 zuwa hamsin kuma tayi da manyan Jaruman Masana’antar shirya fim dake Kano kamar su; Adama A Zango, Hamisu Breaker,Garzali Miko dadai sauransu.
Momee Gombe Phone Number
Momee Gombe ta bayyana dalilin samun Sunanta wato Momme da cewa sunan kakarta ne “Maimuna” don haka iyayenta basa iya kiran sunan suke kiranta da “Momee”.