Yadda Ake Duba Date Of Birth Na BVN Ba Tare Da Anje Banki Ba
A wannan rubutun namu na yau zanyi bayanine akan yadda ake duba date of birth na BVN cikin sauqi. Wani lokaci akan samu wannan matsala kuma ba’asan yadda za’a magance matsalar ba dole sai anje banki an duba. A wannan post din zaka dubawa kowa ke buqatar ganin bayanan BVN dinsa koda bakwa gari daya, abinda ake buqata shine kawai ya bayar da BVN din.
Da farko zaka garzaya PlayStore kayi searching “Tajbank”, Zaka ganshi mytaj sai ka sauke application din.
Taj Bank wani sabon bankine da ba kowa yasan dashi ba, domin ba’a jima sosai da fara amfani da shi ba sunada branches a fadin nigeria. Bayan ka sauke app din sai ka duba daga kasa zakaga inda aka rubuta “Open Account” sai ka shiga gun zasu tambayeka “DO YOU HAVE BVN” sai ka danna YES.
Zakaga ENTER BVN Sai ka saka BVN din taka ko ta wani wanda kakeso kaga bayanan BVN dinsa, bayan ka rubuta sai ka danna CONTINUE Zai danyi verifyng na dan sakanni zai nunamaka BVN VERIFICATION SUCCESSFUL Saika danna Continue Nan take zakaga cikakken suna da date of birth baki daya.
Yadda Ake Duba NECO Result
Yadda Ake Duba Number Layin MTN, Airtel, GLO da 9Mobile