Domin sanin abubuwan dake bata azumi da kuma abubuwan da basu bata azumi, sunnonin azumi, rukunnan azumi da kuma makaruhan azumi sai kushiga nan.
Minene Azumi ?
- Azumi A Lugga: Shine kamewa.
- Azumi A Shari’ance: Shine kamewa daga barin chi ko sha da saduwa da iyali tun daga ketowar alfijir har zuwa faduwar rana da niyyar yin ibada.
Rukunnan Azumi
- Yin niyya.
- Kamewa dagachi ko sha da saduwa da iyali.
- Zamani (lokachin yin azumi).
Sunnonin Azumi
- Gaggauta buda baki.
- Jinkirta sahur.
- Addu’a yayin buda baki.
- Yin sahur da jinkirta shi.
Makaruhan Azumi
- Kaiwa matuka wajen kurkuran baki
- Sumba
- Dauwamar da kallo na sha’awa
- Tunani akan al’amuran saduwa
- Shafa ko runguma
- Dandanan wani abu
- Sanya tozali
- Yin kaho.
Abubuwan Dake Bata Azumi
- Saduwan wani abu zuwa makoshi (narkakke)
- Fitarda maniyyi ko maziyyi da gangar
- Saduwa ta hanyar tilasta
- Chi ko sha da tunanin sauran dare
- Chi ko sha da gangan
- Saduwan wani abu wanda ba narkakkeba zuwa makoshi
- Ridda
Abubuwan Da Suka Halasta Ga Mai Azumi
- Yin asiwaki
- Sanyaya jiki da ruwa
- Tafiya ta halas
- Sanya magani wanda ya dache
- Tauna wani abu ga karamin yaro
- Sanya turare.
Abubuwan Da Akayima Mai Azumi Rangwame Akansu
- Hadiye yawu
- Rinjayen amai da magwas
- Rinjayen wani kwaro zuwa ga makoshi
- Kuran kan hanya
- Wayan gari da janaba
- Yin mafarki da rana
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
Magungunan Gargajiya Guda 15 Masu Amfani