Amfanin Citta a Jikin Dan’adam
Citta na daga cikin abubuwan da ake amfani dasu wajen girkin abinci da kayan shaye-shaye kamar sobo. Yana da kyau ayi amfani da CITTA wajen abinci domin taimakon lafiyar jiki.
- Citta na taimakawa wajen kare ka daga kamuwa da sanyi.
- Citta na taimakawa wajen dauke zafin cuta (antianalgestic)
- Citta na taimakawa wajen gudanar da yawan siga cikin jiki
- Citta na taimakawa wajen kawar da zafin kirji da zuciya
- Citta na taimakawa wajen rage kiba.
- Citta na taimakawa wajen kare ka da kamuwa daga cutar “ALZHEIMER”
- Citta na taimakawa wajen habbaka gunanar jini a jiki (blood circulation)
- Citta na taimakawa wajen rage azabar ciwon ASMA
- Citta na taimakawa wajen warkar da cutar daji (cancer)