Amfanin Dabino a Musulunci.
Dabino yanada matukar amfani a jikin dan Adam, domin Manzon Allah (S.A.W) ya kasance mai son Dabino, har ma yace “Idan kunyi azumi, to Dabino ya zama abunda. zaku fara ci (buda baki) dashi, idan babu dabino, to ku samu kankana”
- Yana saurin narkar da abinci.
- Yana Sanya kuzari yayin Ibadar Aure.
- Yana taimakawa wajen kara jini.
- Yana taimakawa Ma’aurata maza/mata.
- Yana Maganin Basir Mai sa tsugunni a bayi.
- Yana karawa Ido lafiya
- Yana Rage Nauyin kiba da teba.
- Yana Maganin Gudawa
- Yana Saurin Saukarda Hawan jini.
- Yana taimakawa kwakwalwa wajen Samun basira.
- Yana kariya daga Sihiri.
- Yana taimakawa Mata masu ciki dan samun sauqi wajen haihuwa.
- Yana kariya daga Sihiri.
Dabino Domin Maganin Ciwon Nono.
Anacin dabino guda 7 asha man tafarnuwa karamin cokali sau 1 arana kwana uku.
Dabino Domin Karin Ni’ima ga Ma’aurata
Ana daka dabino a zuba cikin madara (freesh milk) sannan a saka Zuma a ciki a sha awa daya kafin a kwanta.
Dabino Domin Mata Masu Juna Biyu
Ana cin dabino kwara bakwai kullum da safe idan anyi kusan haihuwa Wannan yana hanawa macce yawan zubar jini lokacin haihuwa da iznin Allah.
Dabino Domin Maganin Gudawa
Ana daka garin dabino a saka a ruwan zafi a sha In shaa Allahu yana tsayar da gudawa.
Dabino Domin Samun Kuzari
Ana cin dabino guda ukku a sha zuma cokali 1 da safe da yamma.
Dabino Domin Samun Lafiyar Fata
Ana hada garin dabino da zuma da man zaitun a shafa a fuska awa daya sai a wanke fuskar da ruwan zafi wannan yana saurin gyara fuska. Bin cike ya nuna Yawaita cin dabino na hana kamuwa da ciwon CANCER ko wacce iri. Haka Kuma MANZON ALLAH (saww) YACE DABINO AJWA YANA MAGANIN DUKKAN CUTATTUKA, KUMA DUK RANAR DA KACISHI,BABU WATA CUTA DA ZATA SAMEKA AWANNAN RANA, KO KUMA SAMMU KO SIHIRI. Wasu MALUMMAN MUSULUNCI kuma sunce Annabi (saww) Yana nufin kowanne dabino ba wai sai Ajwaba (Wallahu A’alam)
Amfanin Aswaki ga Mata da Maza