Amfanin Kubewa Ajikin Dan Adam
Mutane da dama suna amfani da kubewa a matsayin miya ba tare da sanin tarin amfanin ta ga jikin dan Adam ba. Bincike ya nuna kubawa na dauke da sinadarai kaman haka:
- Calories
- Carbs
- Protein
- Fiber
- Magnesium
- Folate
- Vitamin A
- Vitamin C
- Vitamin K
- Vitamin B6
Wassu sinadaran sun hada da sinadaran kare cells da kuma lalata ta guba a jiki kaman:
- polyphenols
- flavonoids
- isoquercetin
- lactin
Ga kadan daga cikin amfanin kubewa a jikin dan Adam:
Kara Karfin Gani
Kubewa yana taimaka wajen kara karfin gani. Ko mai karatu ya san dalili, sabida yana dauke da sinadaran Vitamin A da carotene.
Yana taimakawa masu juna biyu
Kubewa yana matukar taimakawa masu juna biyu wajen inganta lafiyarsu da kuma na jaririn da ke ciki, domin kubewa na kunshe da dimbin sinadaran Vitamin B da ke samarwa da kuma inganta sabbin kwayoyin halitta na gina jiki da. lafiyarsa.
Hana kamuwa da ciwon koda
Wani bincike da aka gudanar a jami’ar Jilin ta kasar Sin ya tabbatar da cewa, yawan amfani da kubewa na matukar rage hadarin kamuwa da ciwon koda.
Maganin cutar Asthma
Kubewa yana maganin cutar wahala wajen fitar da numfashi wato Asthma, saboda sinadarin Vitamin C da ke tattare ta ita.
Maganin Ciwon Sugar
Ana amfani da kubewa wajen maganin cutar siga wacce ta zamo ruwan dare a tsakanin al’umma a yanzu. Tana dauke da sinadarin fibre a cikinta, wanda ke taimakawa wajen daidaita yawan siga a cikin jikin dan Adam.
Inganta Lafiyar Uwar Hanji
Kubewa na inganta lafiyar hanji da tumbi ta hanyar fitar da sanadaran da ka iya lahani ga hanji ko tumbin. Kuma sakamakon haka ne, ta ke maganin kumburi da cushewar ciki wanda kuma ke rage karfi ciwon siga ko ma maganinsa.
Kubewa Na Kara Karfin Garkuwan Jiki
Yawan amfani da kubewa na kara bunkasa tare da karfafa garkuwar jikin dan-adam. akwai wasu Sinadarai dake cikin kubewa masu matukar amfani a garemu da suka hada da, Bitamin C da ‘Calcium’ da ‘Magnesium’ dake taimaka wa wajen yaki da kuma fatattakar duk wata cuta da ka iya kai wa jikin mutum farmaki.
Yana maganin karancin jini
Yana matukar maganin karancin jini a jiki domin kubewa na kunshe da sinadarin Iron sosai. Kuma yawan amfani da kubewa na sanya idan ka ji rauni jini ba zai zuba da yawa har ya yi wa mutum lahani ba.
Gyaran Fata.
Ga mai son kara inganta fatan jikin sa ya yi laushi da santsi kamar yaukin kubewar toh ya lazumci amfani da ita.
Rage Hadarin Kamuwa Da Ciwon Zuciya
Kubewa na wannan aiki ne saboda wani sanadari da take kunshe da shi da ake kira ‘soluble fibre’ a turance, wanda ke taimakawa wajen rage ‘cholesterol’ wanda hakan ke rage yiyuwar kamuwa da ciwon zuciya.