Amfanin Kuka da Madara
Ganyen kuka wanda a Ingilishi suke kiransa da (baobab) na dauke da sinadarai da dama wadanda ke inganta lafiyar jiki. Ga sinadaran da ganyar bishiyar kuka ke dauke da su:
- vitamin c
- calcium
- phosphorus
- carbohydrates
- fiber
- potassium
- protein
- lipids
- magnesium
- zinc
- sodium
- iron
- lysine
- thiamine
Yana inganta lafiya ta hanyoyi da dama, haka kuma yana magance matsaloli iri-iri da ka iya samun mutum na yau da kullum. Ga kadan daga cikin amfanin da ganyen kukar ke da shi:
- Yana magance tari da taruwar majina a kirji.
- Yana rage yawan zufa kamar yadda su turarukan zamani ke yi.
- Yana rage ciwon Asthma da na koda da na madaciya.
- Yana rage gajiya da kumburi.
- Yana rage radadin cizon kwari.
- Yana magance tsutsar ciki.
- Zazzabin maleriya
- Tarin fuka TB
- Tana ingana garkuwar jiki
- Tana ƙara jini a jiki
- Tana maganin gudawa
- Tana maganin hakori
- Tana maganin ulsa
- Tana rage ƙiba
Amfanin Ayaba ga Mace da Namiji