Amfanin Lalle Ga Mata da Maza
Macen da take da ni’ima ma’ana wacce Allah ya san ya wa yawan sha’awa a jiki da kuma damshin jiki da gamsarwa, idan tana yin lalle to sha’awar da ni’imarta ba za su gushe ba har sai sanda tsufa ya kai wani mataki.
Lalle na maganin cututtukan da ke lailayi a baki kamar zubar jini a sanda ake kurkurar baki ko kuraje ga harshe ko a cikin baki na ba gaira ba dalili. Sai a tafasa ganyen lalle a dunga kurkure baki da ruwan a kalla sau uku a wuni.
A bangaren gyaran fuska, lalle ya zarce sauran kayan kolliya domin duk yanda kike amfani da foda a fuskarki, to ba za ta kai lalle tasiri ba domin shi lalle har sha’awa yake karawa mace, haka kuma yana janyo hankalin namiji yaji yana sha’awar matarsa muddin tana yawan yin lalle.