Amfanin Lemun Zaki Ga Lafiyar Dan’adam
Shan lemon zaki na bawo guda daya kacal akullum na matukar taimakawa jiki wajen gudanar da ayyukansa na yau da kullun da magance cututtuka da dama. Anan zamuyi dan gajeren rubutu akan amfanin sa guda takwas:
- Maganin Cutar Kansa: Lemo yana taimakawa wajen rage wa mutun yiwuwar kamuwa da ciwon Kansa Kowacce iriyace harsahen wani bincike. Lemon zaki na dauke da wadataccen sinadarin(citrus limonoids),kuma wannan sinadarin na taimakawa wajen hana kamuwa da kansar fata da huhu da nono da ciki da kuma hanji.
- Maganin Cutar Koda: Lemo yana taimakawa wajen magance cutar koda da kuma rage hatsarin kamuwa da cutar nan na duwatsun koda(kidney stones).
- Taimakawa Wajen Kyaran Fata: Yana taimakawa sinadaran ciki wajen samun damar narka abinci yadda yakamata ta yadda jiki zai amfana sosai daga abincin.
- Maganin Gyaran Fata: Yana dauke da sinadarin Vitamin C da “Antioxidant”Wanda suke taimakawa wajen bawa fata kariya daga cututtuka daban daban. Yana Hana fata yin yaushi tare dasata sheki da kyalli.
- Maganin Karin Gani: Yana taimakawa idanu wajen Samar da kyakkyawan gani saboda yana da sinadarin (carotenoid compound)masu yawa Wadanda ake juyasu su zama (bitamin A),sai su taimaka wajen hana matsalar gani.
- Maganin Cututtuka Masu Hatsari: Yana rage hatsarin kamuwa da cututtuka masu hastari,saboda yana dauke da sinadarin bitamin C da yawa.
- Maganin Ciwon Suga da Hawan Jini: Bincike yanuna cewa yawan Shan lemon Zaki kan bada kariya daga kamuwa da wannan cututtuka biyu tare da daidaita hawan jini da siga ajiki.
Yadda Ake Gane Mace Yar Madigo (Lesbian)