Hanyoyin Mallakar Miji ko Saurayi
Maza suna da bambanci wajen abinda suke so. Ba lallai bane abinda yake burge Bashir ya burge Mustapha. Saboda abinda da turanci ake cewa ‘Individual differences”. Tabbas, akwai abubuwan da kowanne namiji zai iya so daga wajen budurwarsa, bazawararsa ko matarsa. Ga wasu daga cikinsu:
- Tsafta – Mace mai tsafta duniya ce inji matasa. Ba sai namiji ba, kowa yana son kusantar mutum mai tsafta har a sahun sallah.
- Hakuri – Hakuri maganin zaman duniya inji Bahaushe. Duk matsala idan aka yi hakuri za a ga qarshenta idan Allah yaso.
- Shaugwa6a – Mace mai shaugwa6a dadin zama gareta. Ko min tsufan mijinki, zaki iya yi masa shaugwa6a idan kina son ganin annuri a fuskarsa.
- Kalaman soyayya – Girman kai ne yake sa mata da maza rashin fadawa junansu kalaman soyayya. Idan biki fada masa ba, to zai yi sha’awar Aisha Tsamiya idan yaji ta fadawa Ali Nuhu a fim. Kuma ba kyau ta fiki ba.
- Biyayya da iya girki – Ko mahaukaci baya son rashin biyayya shiyasa yake biyo mutanen da suka tsokaneshi. Girki mai dadi har kyauta zaisa miji yayi miki saboda abinci shine buqatar da Dan Adam ta farko.
- Biyan buqata da iya hira – Na farkon ba sai nayi bayani ba. Iya hira yana sa namiji ya dinga marmarin ganin mace. Kowacce mace zata iya gane irin hirar da namiji yake so. Wani yafi son a kawo masa hirar munafinci lol, ban ce ki sa6i Allah ba don ki burgeshi.
- Damuwa da matsalolinsa – Ki dinga nuna damuwarki da halin da yake ciki na rashin dadi. Matsala ce a kasuwa ko wajen aiki ko ta karatu.
- Tattali – Mace mai tattali alheri ce wacce kowanne miji yake so.
- Duk tsufansa, kice masa “baby” zaki sha mamaki. Watakila ma a ranar zai fara doro yana yanga.