Entertainment

Hanyoyin Rabuwa da Istimna’i (Zinar Hannu)

Hanyoyin Rabuwa da Istimna'i (Zinar Hannu)

Hanyoyin Rabuwa da Istimna’i (Masturbation)

Hanyoyin Rabuwa da Istimna’i: Hakika matsalar Istimna’i (wato Masturbation) da hausa kuma Zinar Hannu (kokuma duk wata hanya ta fitar da maniyyi bata jima’i ba, kuma ba a mafarki ba ) gagarumar matsala ce wacce take shiga zuciyar masu yinta, tayi KAKA-GIDA Kuma tana da wahalar fita gaba dayanta dole sai dai albarkacin addu’a da kuma yawaita ibada mutum zai samu wadatuwar tsoron Allah azuciyarsa harma ya zamto ba zai iya aikatawa ba.

Na tattauna da mutane sama da dari biyu (200) a wannan satin yawanci suna kukan yaya zasuyi su rabu da wannan matsalar sudaina yi, suna cewa koda sun daina suna kara komawa basa’iya bari, Wasu daga cikinsu suna cewa gaba daya basa iya haddace karatu adalilin matsalar aikata Istimna’i ta kawo musu.

Wasu Kuma suna cewa haka kawai suke zubarda maziyyi koda wa’azi sukaji anayi akan mace, wasu kuma na cewa kankantar gabane yake damunsu, Wasu Kuma Ya haifar musu da matsalar ido, Wasu Kuma tsananin ciwon baya, Dan Allah ai Ya kamata kodan wannan mutum ya tuba yabar aikata wannan abin.

Mafiya yawan samari suna yi ne bisa niyyar wai zasu kauce ma ZINA. Basu san cewa shima wannan din babban Kaba’ira bane!!.

Matasa Maza da Mata da dama sun afka cikin wannan bala’in. Wasu cikin rashin sanin illolinsa, wasu kuma saboda tsabar Fajirci.

Kuma kamar yadda zina take da mutukar Illa tana cutar da lafiyar mutum, ta chutar da hankalinsa, da gurbata tunaninsa, ta cire masa Kwayar Imani da tsoron Allah daga zuciyarsa.

tohakanan shima Istimna’i yake lalata rayuwar mutum da mutuncinsa da lafiyarsa. Lallai wajibi ne ga duk mutumin da yake son kansa da arziki, kuma yake fatan gamuwa da Allah lafiya, ya nisanci Zina da dangoginta irin su Luwadi, Madigo, Istimna’i, da sauransu. Kamar yadda ake ta fada anan a kafafen Wa’azantarwa da fadakarwa . Babbar hanyar da zaka bi/zaki bi domin rabuwa da wannan bala’in sun hada da:

 • Yin aure
 • Yawaita azumi
 • Nisantar duk wani hoto ko video mai nuna tsaraici. (Ka gogeshi daga wayarka)
 • Nisantar shafukan Internet masu nuna tsaraici.
 • Dena abota da fitsararrun abokai / Qawaye.
 • Nisantar duk wajen da ake chudanya tsakanin maza da mata.
 • Ka dena zama kai kadai a cikin daki in dai ba ibada kake yi ba.
 • Yawaita karatun Alqur’ani da zikirin Allah da sauran ayyukan alkhairi.
 • Zama cikin Mutanen kirki, karanta labaran mutanen kirki tare da kokarin koyi dasu.
 • Tuna Allah ako yaushe da kuma tunowa kusancinsa gareka aduk inda kake.
 • Tuna kusancin ajalinka, fitar ranka, kwanciyar Qabarinka, hisabinka, da kuma masaukinka na karshe. Wuta ko Aljannah.
 • Fita daga duk wani Group ko shafi na batsa a Facebook ko Whatsapp wanda suke Qunshe da abubuwan batsa, tare da nisantar Friends masu sharing din abubuwa irin wannan.

Amfanin Jima’i ga Namiji da Mace

Leave a Comment