Karin Magana Guda 100
Karin Maganar Hausa proverb guda 100 nasu muhimmanci ga hausawa
- Abin da sake, an bai wa mai kaza kai
- Abin nema ya samu, matar dan doka ta haifi barawo
- Aikin banza talaka ya grime sarki
- Ba’a sarki biyu a gari daya
- Ba maraya sai rago
- Ba zama an saci dan barawo
- Banga alama ba, ance wa kuturu ya gama lafiya
- Ba mutuwa ake tsoro ba, sabo
- Cin danko harda su kaza ?
- Ci naka in ci nawa, ba rowa bane halin zama ne
- Da muguwar rawa, gwamma kin tashi
- Da tsohuwar zuma ake magani
- Da haka muka fara, kuturu yaga mai kyasbi
- Da rarrafe yaro kan tashi
- Dan hakin da ka raina shi ke tsole maka ido
- Dole ne a ce wa mijin Iya Baba
- Dogaro ga Allah jari ne
- Dokin mai baki ya fi gudu
- Durkusa wa wada ai ba gajiyawa ba ne.
- Duk yadda ake yi da jaki, sai ya ci kara
- Fata na gari lamiri ne
- Gaba da gabanta, aljani ya taka wuta
- Gaba ta kai ni gobarar titi a Jos
- Garin banza a farau farau din banza yake karewa
- Ga fili ga mai doki
- Gaskiya matakin nasara.
- Gaskiya tafi kwabo
- Gani ga Allah barawo a hannun mata
- Girman kai rawanin tsiya
- Gobara daga kogi maganin ta Allah
- Hankaka mai da dan wani naki
- Hanta ba ta rabo da jinni
- Hali zanen dutse, ba mai shafewa
- Halin mutum jarinsa
- Hannu daya ba ya daukan jinka
- Hankali ya fi wayo
- Idan aski ya zo gaban goshi ya fi zafi
- Idan mutum ya je gari, ya ga kowa da jela, shima ya nema ya sa
- Idan makaho ya rasa ido, sai ya ce yana wari
- Ikon Allah sai kallo
- Ilimi gishirin zaman duniya
- In ajali ya kira ko ba ciwo sai an je
- In ka ga kare na sunsuna takalmi dauka zai yi
- In bera na da sata daddawa ma na da wari
- In kunne ya ji gangan jiki ya tsira
- Ja ya fadi, ja ya dauka
- Ka da hangen hadari ya sa a yi wanka da kasha
- Karen bana shi ke maganin zomon bana
- Karkatacciyar kuka mai dadin hawa
- Karamin sani kukumi ne
- Karshen alewa kasa ne
- Ko da kudinka, sai da rabonka
- Komai nisa dare gari zai waye
- Kowa ya ci zomo ya ci gudu
- Kowa ya iya allonsa, ya wanke
- Kukan kurciya jawabi ne, mai hankali ke ganewa
- Kyauta ba ya hana arziki
- Labarin zuciya, a tambayi fuska
- Laifi tudu ne, ka taka naka ka hangi na wani
- Linzami ya fi karfin bakin kaza
- Madugu uban tafiya ne
- Mai daki shi ya san inda yake masa yoyo
- Mai laya kiyayi mai zamani
- Mai madi ke talla, mai zuma sai a same shi a saya
- Mai nema na tare da samu
- Mai rabon ganin badi ko ana ruwan masu, sai ya kai
- Mai rabon shan duka baya jin kwabo sai ya sha
- Maras gaskiya ko cikin ruwa ya yi jibi
- Mahakurci mawadaci
- Mugu shi ya san kawancin mugu
- Matambayi ba ya bata
- Na shiga ban dauka ba, baya fidda barawo
- Namiji barkono, sai an dandana ake sanin yajinsa
- Raina kama ka ga gayya
- Ramakon gayya tafi ta gayya zafi
- Rashi hakuri shi ya sa ake me aka shuka?
- Rashin sani ya fi dare duhu
- Rashin sani Karen gwauro ya kori bazawara
- Ruwa ba sa’an kwando ba ne
- Samun shiga, barawo da sallama
- Sata a gidan barawo rance ne
- Sauri ya haifi nawa
- Son kowa, kin wanda ya rasa
- Son maso wani cuta ne
- Sharia’a sabanin hankali
- Ta faru ta kare, an yi wa mai dami daya sata
- Tafiya mabudin ilimi
- Tsitacciyar mage bata mage
- Uwa ta fi uba, ko da uban sarki ne
- Wanda ya ci zomo, ya ci gudu
- Wani kaya sai amale, jaki ba zai iya ba
- Wani hani ga Allah baiwa ne
- Yaro bai san wuta ba sai ya taka
- Yau da gobe sai Allah
- Yi na yi, bari na bari, shine biyayya
- Zafin nema baya kawo samu
- Zakaran da Allah ya nufa da cara, ana muzuru ana shaho sai ya yi
- Zo mu ci tuwo yafi tuwon dadi
- Zo mu zauna zo mu saba ne
- Zakara a rataye ba ya cara
Tarihin Bayajidda AKasar Hausa