Entertainment

Sakonnin Masoya Na Dare Masu Dadi

Sakonnin Masoya Na Dare Masu Dadi

Sakonnin Masoya Na Dare Masu Dadi

Sakonnin mu Kwana lafiya tsakanin masoya, sakwanni ne da suke da tasiri a tsakaninsu. Duk masoyan da suka saba yiwa junansu irin wadannan sakonnin, zai yi matukar wuya bacci ya daukesu ba tare da sun karanta irin wannan sakon daga masoyansu ba. Ga wasu irin sakonnin nan da masoya zasu iya turawa junansu domin inganta soyayyan su.

  1. Naka yin takaici idan dare yayi, saboda sai nayi wasu a wannin ba tare da jinki ko ganinki ba. Da fatan zaki tashi lafiya.
  2. Ina miki fatan yin mafarki mai dadi da kuma kyau tamkar fuskarki.
  3. Babu yadda za a iya kwantanta ganinki a mafarki da kuma ganinki a zahiri. Da fatan dake zan soma arba idan Allah Ya tashemu lafiya.
  4. A kullum, a daidai irin wannan lokacin nakanyi burin ganin lokacin auren mu ya gabato.
  5. Duk abubuwan dake cikin dakina, gidana, duk a banza nake ganinsu har sai ranar da zan ganki tsakar dare a tare a matsayin miji da mata.
  6. Gani nake kamar agogo baya juya saboda yadda na kosa gari ya waya idanuwa su ganki.
  7. Zuciyana ta saba da karanta sakonki, kamin kwakwaluwa na ya amincewa idanuwa su rumtsa. Ina jiran ji daga gareki kamin na iya bacci.
  8. Idan ina son dare ya mini gajartai na soma tunaninki cikin dare.
  9. Muddin ba kece abu na karshe dana tunano ba, bani ba bacci a wannan daren.
  10. Sai dare yayi a irin wannan lokacin nake kara tabbatar da dalilin da ya nake sonki.

Namiji zai iya aikawa mace, ita ma mace na iya aikawa namiji ba wai na maza bane kadai. Da fatan za ayi soyayya mai tsafta domin samun zaman aure da zuriya masu tsafta.

Sakonnin Masoya Na Dare Masu Dadi
Sabbin Kalaman Soyayya Masu Dadi 2022

Leave a Comment