Entertainment

Sakonnin Soyayya Na Barka Da Shan Ruwa

Sakonnin Soyayya Na Barka Da Shan Ruwa

Sakonnin Soyayya Na Barka Da Shan Ruwa

Domin inganta soyayya tsakanin masoya yasa muka kawo maku sakonnin soyayya na barka da shan ruwa.

 1. Zuwa ga zaɓin zuciyata, ina fatan ka
  sha ruwa lafiya? Ina fatan izuwa yanzu
  nutsuwa ta game jikinka, ishiruwa ta
  gushe daga makoshinka? Ina kuma fatan lada ya tabbata a gare ka. Fatan ka sha ruwa lafiya? Ka Huta Lafiya.
 2. A dukkan lokacin da na ga daren
  Lailatilkadari, zan kasance mai rokon
  Ubangiji Ya mallaka min kai a matsayin
  mijina uban ‘ya’yana, ina fatan kai ma
  zaka kasance mai tsawaita tsayuwa cikin kowane dare domin ganin cikar
  burinmu? Ina Son Ka.
 3. A lokuta da wurare daban-daban ina
  ganin ka kana yi min gizo, ina ganin ka a lokacin da idanuwana ke a rufe ko a
  buɗe. Ba na iya yin komai ba tare da
  tinaninka ba. Fatan Ka Sha-ruwa Lafiya.
 4. Jin muryarka na sakwan guda, na jefa ni cikin kogin tinaninka, na tsawan
  lokacin da idanuwana ke kasancewa a
  buɗe. Barka Da Shan-ruwa.
 5. Irin kulawar da kake nuna min a
  kullum na saka ni tinanin irin yadda
  rayuwarmu za ta kasance a nan gaba. Zanbzamo tamkar sarauniya a gidanka, kai kuma zaka zamo sarkin da babu wani mai irin masarautarsa a duniya ta kowace fuska. Ina Son Ka.
 6. Zuciyata ba za ta taɓa canja matsayin
  da kake da shi ba a cikinta. Murmushina gare ka ba zai taɓa yankewa ba. Son ka a cikin zuciyata ya yi kafuwar da ba zai taɓa goguwa ba a cikinta na har abada. Barka Da Hutawa.
 7. Da a ce zan iya zama komai, da na
  zama ruwan hawaye a gare ka, a haife ni a cikin idanuwanka, na rayu a saman
  kumatunka, na mace a saman laɓɓanka. Ina son ka so mara misaltuwa. Barka Da
  Shan-ruwa.
 8. A dukkan lokacin da kake bukatar
  wani ya taya ka hira, karda ka manta
  kana da ni, ka nemo ni domin ɗebe maka kewa a cikin kowane irin yanayi da lokaci. Fatan Ka Wuni Lafiya? Yaya
  Ibada?
 9. A lokacin da na tino irin rayuwar da
  na yi a baya, na kan hango irin asarar da na yi, na kasancewa ta ni kaɗai ba tare da kai ba , yanzu na same ka, ina ji na a matsayin wata wadda ta fi kowace mace sa’a a rayuwa. Ina fatan na kasance a tare da kai na har abada. Barka Da Shan-ruwa.
 10. Ba zan taɓa mantawa da ranar cikar burina ba, ranar da wanda nake so ya nuna min soyayyarsa a fili, ba kowa bane face kai hasken idaniyata. Ina son ka. Barka Da Hutawa. Fatan Ka Sha-ruwa Lafiya?

Soyayya Text Message

Leave a Comment